'Yan Najeriya za Su iya Kayar da Tinubu a 2027,' Hakeem Baba Ahmed

'Yan Najeriya za Su iya Kayar da Tinubu a 2027,' Hakeem Baba Ahmed

  • Hakeem Baba-Ahmed ya gargadi Shugaba Bola AhmedTinubu cewa ‘yan kasa na da ikon kada shi a zabe mai zuwa na 2027
  • Ya ce ya kamata shugaban kasa ya rage harkokin siyasa ya mai da hankali kan ayyukan gwamnati da cigaban kasa
  • Baya ga haka, Hakeem Baba-Ahmed ya soki shiru da Tinubu ya yi kan rade-radin cewa zai canza mataimakinsa Kashim Shettima

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Dattijon Arewa, Hakeem Baba-Ahmed, ya bayyana cewa ‘yan Najeriya suna da damar kada Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027.

Hakan na zuwa ne yayin da 'yan siyasa suka fara maganganu da shiri kan zaben shekarar 2027 a Najeriya.

Dattijon Arewa ya ce za a iya kayar da Tinubu a 2027
Dattijon Arewa ya ce za a iya kayar da Tinubu a 2027. Hoto: Bayo Onanuga|Hakeem Baba Ahmed
Source: Facebook

Baba-Ahmed ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi a shirin siyasa na Channels Television a ranar Laraba 21 ga Yuli, 2025.

Kara karanta wannan

Ana rade radin gwamnan Yobe zai fita daga APC zuwa ADC, hadiminsa ya yi magana

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya yi kira ga Shugaba Tinubu da ya mayar da hankali kan mulki da kyautata rayuwar jama’a maimakon shirye-shiryen siyasa tun kafin lokacin zabe.

Hakeem ya ce za a iya kayar da Tinubu

A cewar Baba-Ahmed, al’ummar Najeriya za su yi tambaya a kan abin da shugaban kasa ya yi da wa’adin mulki na farko da aka ba shi.

Vanguard ta wallafa cewa ya ce:

“Karshe dai ‘yan Najeriya za su ce, ‘Me ka yi da shekaru hudu na farko da muka ba ka?’. Za mu iya kada ka idan aka yi sahihin zabe cikin adalci.”

Maganar ajiye Shettima a zaben 2027

Hakeem Baba ya kuma bayyana rashin jin dadinsa da yadda shugaba Tinubu bai fito kai tsaye ya karyata rade-radin da ake yi cewa yana shirin cire mataimakinsa, Kashim Shettima, a 2027 ba.

Ya ce, da lallai rade-radin ba gaskiya ba ne, da shugaban kasa ya fito ya ce da bakinsa yana goyon bayan Shettima kuma yana aiki da shi lafiya.

Kara karanta wannan

Hakeem Baba Ahmed ya fadi kuskuren Tinubu kan batun sauke Shettima

Dattijon ya kara da cewa yadda Tinubu da mukarrabansa suka ki fadin komai kan rade-radin yana barin kofar zargi a bude.

Ya kara da cewa:

“Ina so in san dalilin da ya sa ba a fadi komai ba har yanzu kan wannan magana. Shiru da rashin yin karin bayani na iya nuni da wani abu.”
Tinubu da mataimakin shi, Kashim Shettima
Tinubu da mataimakin shi, Kashim Shettima. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Bukatar auna nasarar Tinubu a shekara 4

A karshe, Baba-Ahmed ya ce shugabanci na bukatar cikakken bayani da auna nasarori kafin a sake bai wa shugaba dama a gaba.

Ya ce:

“Babu ruwan jama’a da sauyin jam’iyya ko sauyin ra’ayi a siyasance. Karshe dai ‘yan Najeriya za su zabi shugaba bisa abin da ya aikata.”

An yi hasashen nasarar Tinubu a 2027

A wani rahoton, kun ji cewa an fara hasashen yadda Bola Tinubu zai samu nasara a zaben 2027 bayan ganawa da Rabiu Kwankwaso a Abuja.

Reno Omokri wanda ya fara goyon bayan shugaba Tinubu bayan an rantsar da shi a Mayun 2023 ne ya yi hasashen a wata magana da ya yi.

Sai dai wasu 'yan Najeriya sun bayyana cewa ba lallai Bola Tinubu ya samu nasara ba ko ya yi hadaka da jagoran NNPP a 2027.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng