NEC: Tinubu Ya Yi Ganawar Sirri da Gwamnonin APC gabanin Babban Taron Jam'iyya
- Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya sa labule da gwamnonin APC 22 a Abuja yayin da ake shirin babban taron NEC
- Shugaban gwamnonin APC na kasa kuma gwamnan Imo, Sanata Hope Uzodinma ya ce an duba muhimman batutuwa
- Uzodinma ya ce an tattauna al'amura da dama da za su tabbatar da APC ta ci gaba da zama tsintsiya madaurinki daya
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – Shirin gudanar da babban taron kwamitin zartaswa na ƙasa (NEC) na jam’iyyar APC a ranar Alhamis ya yi nisa bisa dukkan alamu.
Gabanin taron, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gana da gwamnonin jam’iyyar APC da ke ƙarƙashin kungiyarsu ta PGF a daren Laraba, 23 ga Yuli, 2025.

Source: Twitter
Wata sanarwa daga sashen labarai na fadar shugaban ƙasa da aka wallafa a shafin X ta tabbatar da ganawar, wadda aka ce na daga cikin shirye-shiryen taron NEC mai zuwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bola Tinubu ya gana da gwamnonin APC
Arise News ta ruwaito cewa ganawar ta gudana ne a dakin taro na fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, inda gwamnonin APC 22 suka halarta.
Sai dai gwamnonin jihohin Katsina da Akwa Ibom ba su samu halarta ba, amma sun wakilta mataimakan gwamna su halarci zaman.
Bayan kammala taron, shugaban kungiyar PGF kuma gwamnan jihar Imo, Sanata Hope Uzodinma, ya bayyana kadan daga cikin dalilan zaman.

Source: Facebook
Ya ce sun ziyarci Tinubu domin yin ta’aziyya bisa rasuwar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da kuma tattaunawa kan taron NEC da ke tafe.
Ya ce:
“Mun zo a matsayin kungiyar gwamnonin APC don mika ta’aziyyarmu game da rasuwar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, sannan mun tattauna game da taron NEC na jam’iyyarmu da za a gudanar gobe.”
Abin da gwamnonin APC suka tattauna da Tinubu
Uzodinma ya ce sun tattauna ne kan dabarun ƙarfafa jam’iyyar APC a matakai daban-daban daga ƙasa har zuwa sama.

Kara karanta wannan
Ana kewar Buhari, Tinubu da manyan APC za su yi taron farko na maye gurbin Ganduje
A cewarsa, ganawar ta ba su damar tattauna wa da shugaban ƙasa kan dabarun da suka dace a bi don APC ta tumbatsa.
Ya ce:
“Mun miƙa wasu shawarwari ga shugaban ƙasa kan hanyoyin da za a ƙarfafa jam’iyyarmu a matakin ƙananan hukumomi, jihohi, har zuwa matakin ƙasa. "
Da aka tambaye shi ko za a fitar da sabon shugabancin jam’iyya a taron NEC da ke tafe, Uzodinma ya ce:
“Wannan taron NEC ne na jam’iyya, ba za mu iya cewa ga yadda zai kaya ba. Idan kuka zo gobe, za ku gani da idonku.”
Jam'iyyar APC za ta yi taron NEC
A baya, kun ji cewa Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai jagoranci jam’iyyar APC a babban taron kwamitin zartaswa na ƙasa (NEC) da za a gudanar a Abuja.
Babban abin da ake sa ran zai fi daukar hankali a taron shi ne tattaunawa kan wanda zai maye gurbin Abdullahi Umar Ganduje a matsayin shugaban jam’iyya.
Daga cikin wadanda ake sa ran za su halarci taron akwai mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima da tsohon mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
