ADC: Atiku, Peter Obi da Amaechi Sun Cimma Matsaya kan Wanda Zai Yi Takara a 2027

ADC: Atiku, Peter Obi da Amaechi Sun Cimma Matsaya kan Wanda Zai Yi Takara a 2027

  • Jagororin haɗaka sun yanke shawarar goyon bayan duk wanda ya samu nasarar zama sahihin ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC a zaben 2027
  • Tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi ne ya bayyana hakan a Fatakwal, babban birnin jihar Ribas ranar Laraba
  • Atiku Abubakar, Peter Obi da Amaechi ne a sahun gaba wajen neman tikitin takarar shugaban ƙasa a inuwar jam'iyyar haɗaka ADC

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Rivers - Tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa jagororin haɗaka za su marawa duk wanda ya lashe tikitin takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC baya a zaɓen 2027.

Ya ce duka masu neman tikitin takarar jam'iyyar haɗaka watau ADC, Atiku Abubakar, Peter Obi da shi kansa sun amince rashin nasara ba zai sa su watse ba.

Kara karanta wannan

Gaskiya ta fito: An ji dalilan da suka jawo naɗa Ministan Tinubu a matsayin shugaban APC

Tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi.
Jagororin haɗaka sun amince za su marawa duk wanda ya samu tikitin ADC baya Hoto: Rt. Hon. Chibuike Rotimi Amaechi
Source: Facebook

Amaechi, wanda ya yi mulki sau biyu a matsayin gwamnan Ribas, ya bayyana hakan ne a birnin Fatakwal, babban birnin jihar, a ranar Laraba, Channels tv ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku, Obi da Amaechi sun cimma matsaya

Da yake hira da manema labarai, Amaechi ya ce jagororin haɗaka suna da yaƙini da ƙwarin gwiwar cewa za a shirya sahihi kuma ingantaccen zaɓen fidda gwani.

“Duk wanda ya samu nasara a zaɓen fitar da gwani, za mu haɗa kai mu mara masa baya, wannan ita ce yarjejeniyar da muka cimma a tsakaninmu."
"Mun dai ƙara jaddada bukatar shirya zaɓe na gaskiya da adalci, wanda kowa zai gamsu da shi.

- Rotimi Amaechi.

Amaechi ya koka kan matsin rayuwa, yunwa

Tsohon jigo a jam’iyyar APC ya nuna damuwarsa kan yunwa da ƙuncin rayuwa da ke addabar ƴan ƙasa a ƙarƙashin wannan gwamnati.

Ya yi kira ga duk wani dan asalin Jihar Ribas da ya shiga jam’iyyar ADC domin kwace mulki daga jam’iyyar APC mai ci a zaɓen 2027, inji Vanguard.

Kara karanta wannan

Nentawe: Alkawuran da shugaban APC ya daukar wa jamiyya bayan tafiyar Ganduje

“Duk wani ɗan Ribas da ke fatan alheri ga jiharsa da ƙasarsa, ya kamata ya yi rajista da jam’iyyar nan, ya taimaka wajen sauke gwamnati mai ci domin kawo ƙarshen yunwa da wahalhalun da kowa ke fuskanta,” in ji Amaechi.

ADC: Manyan ƴan adawar Najeriya sun haɗe kai

Ƴan adawa sun zaɓi jam’iyyar ADC a matsayin dandamalin da za a yi amfani da shi wajen kalubalantar neman wa’adin biyu na Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Manyan 'yan siyasa da suka shiga cikin wannan sabuwar tafiya sun haɗa da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, da kuma tsohon Gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi.

Jagororin haɗaka, Atiku Abubakar da Rotimi Amaechi.
Amaechi ya koka kan halin matsin rayuwar da aka jefa jama'a a mulkin Tinubu Hoto: Atiku Abubakar, Rt. Hon. Chibuike R Amaechi
Source: Facebook

Sauran gogaggun ‘yan siyasar da ke cikin kawancen sun haɗa da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, David Mark da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai.

Amaechi ya tabbatar da cewa duk waɗannan jagororin haɗakar sun amince za su goyi bayan duk wanda ya zama ɗan takarar ADC a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Amaechi ya shirya kayar da Tinubu a 2027

A wani rahoton, kun ji cewa Amaechi ya sha alwashin kawo ƙarshen burin tazarce na Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen da ke tafe a 2027.

Kara karanta wannan

MTN, Airtel, Glo da sauran kamfanonin sadarwa sun yi gargaɗi, za a iya ɗauke sabis a jihohi 16

Tsohon ministan sufurin ya nuna matuƙar rashin jin daɗinsa game da yadda gwamnatin Tinubu ke tafiyar da harkokin ƙasar nan.

Ya ce lokaci ya yi da za su tashi tsaye su ƙwato Najeriya daga hannun gurɓatattun shugabanni, waɗanda suka jefa jama'a cikin wahala.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262