Ana Kewar Buhari, Tinubu da Manyan APC Za Su Yi Taron Farko na Maye Gurbin Ganduje

Ana Kewar Buhari, Tinubu da Manyan APC Za Su Yi Taron Farko na Maye Gurbin Ganduje

  • Shugaba Bola Tinubu da Kashim Shettima za su jagoranci taron NEC na APC gobe Alhamis a birnin tarayya Abuja
  • Ana sa ran girmama marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari wanda ya rasu yana da shekaru 82
  • Taron zai tattauna batun shugabancin APC, bayan gayyatar wasu daga cikin mambobin kwamitin koli jam'iyyar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai jagoranci sauran fitattun jiga-jigan jam’iyya zuwa taron kwamitin zartarwa na jam'iyyar APC.

Za a gudanar da taron ne a gobe Alhamis 24 ga watan Yulin 2025 a birnin tarayya Abuja.

Za a taron APC da neman magajin Ganduje
Tinubu da jiga jigan apc za su yi taron maye gurbin Ganduje. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Taron APC: Ana sa ran karrama Buhari

Rahoton Vanguard ya ce cikin masu halartar taron har da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, tsohon mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo.

Kara karanta wannan

2027: Gwamnan PDP, shugabanninta sun ba maraɗa kunya, sun goyi bayan Tinubu a fili

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har ila yau, ana sa ran tsofaffin gwamnoni da mambobin kwamitin aiki na kasa da sauransu za su halarci taron.

Akwai alamun cewa za a gudanar da dan gajeren zama na karrama marigayi Shugaba Muhammadu Buhari a gobe, kasancewar wannan shi ne babban taron APC na farko tun bayan rasuwarsa.

Zaman yana cikin wasu muhimman abubuwan da za a tattauna da su a taron NEC da za a gudanar gobe a hedkwatar jam’iyyar ta kasa.

Taron da za a tattauna batun sabon shugaban jam’iyya mai cikakken iko, ana sa ran zai samu yawan halarta domin ba za a yi taron shugabanni na kasa ba kamar yadda aka saba, amma wasu daga cikin mambobin za su halarta.

Al’adar APC ita ce a gudanar da taron shugabanni na kasa kwana daya kafin NEC, amma yanzu za a bar wannan tsarin saboda matsalolin tsare-tsare, in ji majiyoyi daga jam’iyyar.

Kara karanta wannan

APC ta sanya ranar gudanar da babban taro, ana neman magajin Ganduje

Ana sa ran karrama Buhari a taron APC
Tinubu, Shettima za su jagoranci taron APC. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

Wadanda ake sa ran za su halarci taron

Hakan ya sa za a fadada taron NEC na gobe domin ya kunshi wasu daga cikin mambobin kwamitin jam’iyyar da aka gayyata musamman, cewar Punch.

Dangane da kundin tsarin mulki na APC, mambobin NEC sun hada da shugabannin kasa da mataimaka, sakataren kasa, da shugabannin jam’iyya daga kowanne yanki na siyasa.

Haka kuma akwai lauyoyin jam’iyya, shugabannin kudi, shugabannin shiryawa, hulda da jama’a, jin dadin mambobi, da sauran shugabanni da mataimakansu.

Shugabannin mata da matasa, wakilan masu nakasa, shugabannin jihohi, shugabannin majalisa da wakilai daga kowanne yanki za su shiga wannan taro.

Mambobin kwamitin amintattu, tsofaffin shugabanni, ‘yan majalisa masu mulki da wadanda ba su da rinjaye, da wasu da za a kira ko nada su na daga cikin mahalarta.

Taron na NEC gobe na sa ran samun halartar wasu daga cikin mambobin kwamitin kolin jam’iyyar da aka gayyata zuwa wannan taro mai fadi.

Kara karanta wannan

Tattalin daji: Shettima ya yi korafi a taron da Kwankwaso ya halarta a Aso Villa

Gwamna ya ce babu mai kayar da APC

Kun ji cewa gwamnan jihar Ebonyi, Francis Nwifuru ya nuna goyon bayansa ga tazarcen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027.

Gwamna Nwifuru ya bayyana cewa tazarcen Tinubu wani abu ne da Allah ya riga ya ƙaddara zai auku a Najeriya.

Gwamnan ya nuna cewa babu wata haɗakar ƴan adawa da za ta iya hana a sake zaɓen Shugaba Tinubu a zaɓen 2027.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.