An Tayar Jijiyoyin Wuya a Majalisar Tarayya da Mambobi 3 Suka Sauya Sheƙa zuwa APC
- Jam'iyyar APC mai mulki ta samu ƙarin mambobi uku daga PDP a Majalisar Wakilai ta Ƙasa yau Laraba, 23 ga watan Yuli, 2025
- Ƴan Majalisar da suka fito daga jihohin Osun da Edo sun sanar da sauya sheka daga PDP zuwa APC a wasiƙun da suka miƙa wa Majalisa
- Ƴan adawa a Majalisar sun yi yunƙurin tayar da hayaniya da hanyar neman a ƙwace ƙujerun waɗanda suka sauya sheƙa amma ba su cimma nasara ba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Ƴan Majalisar Wakilai ta ƙasa guda uku daga jihohin Osun da Edo sun tabbatar da sauya sheƙa daga PDP zuwa jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya.
Biyu daga cikin ƴan Majalisar sun fito ne daga jihar Osun da ke Kudu maso Yammacin Najeriya, sai kuma ragowar ɗaya da ya fito daga Edo a Kudu maso Kudu.

Source: Facebook
Jaridar The Nation ta tattaro cewa mambobi uku na Majalisar Wakilan Tarayya sun bi sahu, sun miƙa takardar ficewa daga PDP tare da shiga APC a hukumance.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jerin Ƴan Majalisa 3 da suka koma APC
Ƴan Majalisar da suka koma APC a yau Laraba, 23 ga watan Yuli, 2025 sun haɗa da:
1. Hon. Ajilesoro Taofeek Abimbola - Mai wakiltar Ife ta Tsakiya/Gabas/Arewa/Kudu daga jihar Osun
2. Hon. Omirin Olusanya — Mai wakiltar Atakunmosa ta Gabas da Atakunmosa ta Yamma/Ilesa ta Gabas/Ilesa ta Yamma daga Jihar Osun,
3. Hon. Marcus Onobu - Mai wakiltar Esan ta Tsakiya/Yamma/Igueben daga Jihar Edo.
Me yasa ƴan Majalisar suka bar PDP?
Shugaban Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Abbas Tajudeen, ne ya karanta wasiƙun sauya sheƙar yayin zaman majalisa wanda ke ci gaba da gudana yanzu haka a Abuja.
A cikin takardunsu na sauya sheƙa, ’yan majalisun sun bayyana rikice-rikicen cikin gida da rashin jituwa da jam’iyyar PDP a matsayin dalilansu na komawa APC.
Haka zalika sun bayyana cewa burinsu na mara wa Shugaba Bola Tinubu baya wajen gyara tattalin arzikin kasa na daga cikin dalilan sauya shekar da suka yi.
Ƴan adawa sun tayar da rigima a Majalisa
Ƴan tsagin adawa a Majalisar wakilai sun yi fatali da sauya shekar ƴan Majalisar, suna mai cewa hakan ya saɓa kundin tsarin mulki.
Jagoran ’yan adawa a Majalisar, Hon. Kingsley Chinda, ya bukaci Abbas Tajudeen da ya bi doka ya ayyana kujerun ’yan majalisar da suka sauya sheƙa a matsayin wadanda babu kowa a kai.

Source: Facebook
Sai dai Hon. Abbas wanda ke jagorantar zaman, ya amsa masa da cewa za a duba ƙorafinsa, kamar yadda rahoton Leadership ya tabbatar.
Sakataren APC na ƙasa, Sanata Suraj Ajibola wanda ya fito daga Jihar Osun, tare da wasu shugabannin jam’iyyar, sun halarci zaman majalisar domin shaida sauya shekar ’yan majalisar.
Sanatocin PDP 4 sun sauya sheƙa zuwa APC
A wani labarin, kun ji cewa Sanatocin PDP huɗu sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC a zaman Majalisar Dattawa na ranar Laraba, 23 ga watan Yuli, 2025.
Sanatocin, waɗanda suka fito daga jihohin Osun da Akwa Ibom, sun miƙa takardun sauya shekarsu a hukumance ga Majalisa.
Kowane daga cikin sanatocin hudu ya ambaci rigingimun cikin gida da saɓanin da ba za a iya shawo kansu ba a jam’iyyar PDP a matsayin dalilin ɗaukar wannan mataki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


