Ana Batun Ganawar Kwankwaso da Tinubu, Sanatoci 4 Sun Sauya Sheƙa zuwa APC

Ana Batun Ganawar Kwankwaso da Tinubu, Sanatoci 4 Sun Sauya Sheƙa zuwa APC

  • Majalisar Dattawan Najeriya ta sanar da sauya sheƙar Sanatoci huɗu daga babbar jam'iyyar adawa watau PDP zuwa APC mai mulkin ƙasar nan
  • Sanatocin, waɗanda suka fito daga jihohin Osun da Akwa Ibom, sun miƙa takardun sauya shekarsu a hukumance ga Majalisa yau Laraba
  • Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya karanta wasiƙun sauya shekarsu a gaban manyan jiga-jigan APC da suka halarci zaman

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Sanatoci hudu da aka zaɓa a ƙarƙashin jam’iyyar adawa ta PDP domin wakiltar mazabu daban-daban a Majalisar Dattawa ta 10 sun sauya sheka zuwa APC.

Sanatocin guda huɗu, waɗanda suka fito daga jihohin Osun da Akwa Ibom, sun sanar da komawa APC a hukumance a zaman Majalisar Dattawan Najeriya.

Zauren Majalisar Dattawa da ke Abuja.
APC ta samu ƙarin mambobi 4 a Majalisar Dattawa ta 10 Hoto: Nigeria Senate
Source: Facebook

Me yasa Sanatocin PDP 4 suka koma APC?

Kara karanta wannan

Gudumar majalisa za ta hau manyan gwamnati, za a hana su zuwa makarantu da asibitin kuɗi

Shugaban Majalisar Dattijai, Sanata Godswill Akpabio, ne ya karanta takardun sauya sheƙar a zauren majalisa yau Laraba, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kowane daga cikin sanatocin hudu ya ambaci rigingimun cikin gida da saɓani iri daban-daban da ba za a iya shawo kansu ba a jam’iyyar PDP a matsayin dalilin ficewarsu.

Bayan karanta wasikun, Sanata Akpabio ya umarci magatakardar Majalisar Dattawa ya shigar da bayanansu tare da canza masu wuri zuwa tsagin jam'iyya mai mulki.

Jerin sunayen Sanatoci 4 da suka sauya sheƙa

Wani mai amfani da kafafen sada zumunta, Imran Muhammed ya wallafa sunayen sanatocin a shafinsa na X, sun haɗa da:

1. Sanata Francis Fadahunsi – Mai wakiltar mazaɓar Osun ta Gabas

2. Sanata Oluwole Olubiyi – Mai wakiltar mazaɓar Osun ta Tsakiya

3. Sanata Aniekan Bassey – Mai wakiltar mazaɓar Akwa Ibom Arewa maso Gabas

4. Sanata Samson Ekong – Mai wakiltar mazaɓar Akwa Ibom ta Kudu.

Sanatocin APC sun kai 70 a Majalisar dattawa

Bayan wannan sauya shekar, yawan mambobin APC a majalisar dattawa ta 10 sun ƙaru zuwa 72, yayin da na PDP suka ragu zuwa 26.

Kara karanta wannan

Taron APC: Tinubu ya shiga tsaka mai wuya game da zakulo magajin Ganduje

Sai kuma jam'iyyar LP mai kujeru biyar, NNPP na da guda ɗaya tal, SDP guda biyu da kuma APGA wacce ke da sanata ɗaya a Majalisa ta 10.

Shugaban Msjalisar Dattawa, Godswill Akpabio.
Yawan sanatocin APC a Majalisa ta 10 ya kai 70 Hoto: @NGRSenate
Source: Facebook

Wasu daga cikin manyan kusoshin APC sun halarci zaman Majalisar a yau Laraba, 23 ga watan Yuli, 2025 domin shaida wannan sauya sheƙa.

Daga cikin waɗanda aka hanga a zauren Majalisar Dattawan akwai Sakataren APC na ƙasa, Sanata Ajibola Basiru, da tsohon Ministan Kwadago, Sanata Chris Ngige.

Sai kuma wasu ‘yan Majalisar Wakilai da suka raka su zauren majalisa don nuna goyon baya ga jam’iyyar APC bayan wannan sauya sheka.

Majalisar Dattawa ta aika saƙo ga Bola Tinubu

A wani labarin, kun ji cewa Majalisar Dattawa ta bukaci gwamnatin tarayya da ta girmama marigayi Aminu Dantata ta hanyar sanya sunansa a wuri na ƙasa.

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, tare da Sanata Rufai Hanga da Sanata Abdurrahman Kawu Sumaila ne suka gabatar da kudirin.

Da yake gabatar da kudirin a madadin sauran sanatocin Kano, Sanata Barau I. Jibrin ya bayyana rayuwar Alhaji Dantata a matsayin abin koyi da kuma abin alfahari.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262