Bayan Haduwa da Tinubu, Kwankwaso Ya Gana da 'Yan Majalisar NNPP
- Jagoran NNPP na ƙasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya karɓi 'yan majalisar NNPP a gidansa da ke Maitama
- Taron ya zo ne kwanaki kaɗan bayan Kwankwaso ya ziyarci fadar shugaban ƙasa domin wani taro na musamman
- Duk da matsin lamba daga wasu jam’iyyun Najeriya, har yanzu Sanata Rabiu Kwankwaso bai fice daga NNPP ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Jagoran jam’iyyar NNPP na ƙasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya karɓi wakilai daga jam’iyyar NNPP a gidansa da ke Maitama, Abuja a ranar Talata, 22 ga Yuli, 2025.
Taron ya haɗa manyan 'yan majalisa da ke wakiltar jam’iyyar a majalisar dokoki da majalisar dattawa ta ƙasa.

Source: Facebook
Legit ta tattaro bayanai kan ganawar ne a cikin wani sako da hadimin Sanata Kwankwaso, Saifullahi Hassan ya wallafa a X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan taro ya gudana ne kwanaki kaɗan da Sanata Kwankwaso ya halarci wani babban taron da aka shirya a fadar shugaban ƙasa a Abuja.
Ana ganin wannan haduwar na iya daɗa zafafa hasashen game da makomar Kwankwaso a siyasar Najeriya.
Rabiu Kwankwaso ya karɓi 'yan majalisar NNPP
Wakilan NNPP sun haɗu da Sanata Kwankwaso ne ƙarƙashin jagorancin Sanata Rufai Sani Hanga, da ya ke wakiltar Kano ta Tsakiya a majalisa.
Duk da cewa ba a samu bayanai kan abin da suka tattauna ba, ana ganin za su iya tattauna batutuwa masu muhimmanci dangane da cigaban jam’iyyar NNPP a Najeriya.
Haɗuwar na iya zama wani yunkuri na sake ƙarfafa hadin kai tsakanin 'ya'yan jam’iyyar da jagororinta, musamman ganin yadda ake ta hasashe kan yiwuwar sauya sheƙar Kwankwaso.
Kwankwaso ya hadu da baki daga Kano
A wata ziyara ta daban, Rabiu Kwankwaso ya karɓi mai magana da yawun gwamnan Kano, Hon. Sanusi Bature Dawakin Tofa.

Kara karanta wannan
"An kusa fara ganin saƙon kudi," Gwamnatin Tinubu za ta fara biyan ƴan N Power kuɗinsu
Legit ta gano cewa a cikin tawagar Sanusi Bature akwai shugaban ƙaramar hukumar Dawakin Tofa, Hon. Anas Dan Maliki.
A baya, tsohon gwamnan ne ya sasanta Dawakin Tofa da 'dan majalisarsa, Tijjani Jobe.
Sanata Kwankwaso bai fice daga NNPP ba
A cikin 'yan kwanakin nan, ana ta yaɗa jita-jita game da yiwuwar shigar Kwankwaso kawancen jam’iyyun adawa ko ma komawa jam’iyyar APC.
Daya daga cikin dattawan NNPP a Najeriya, Buba Galadima ya tabbatar da cewa manyan jam'iyyun siyasa na zawarcin Kwankwaso.
Sai dai har yanzu ba a samu wata sanarwa daga Sanata Kwankwaso da dangane da barin jam'iyyar NNPP ba.

Source: Twitter
A matsayinsa na fitaccen ɗan siyasa da ya taka rawar gani a matakin ƙasa, mutane da dama na jiran jin sahihan matakan da zai ɗauka, musamman ganin ƙalubalen da ke gaban 'yan adawa.
Kwankwaso ya hadu da Bola Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya gana da shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadar shugaban kasa.
Ganawar na zuwa ne yayin da ake rade radin Sanata Kwankwaso zai iya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC.
A yayin hira da manema labarai bayan ganawa da Tinubu, an ruwaito cewa Kwankwaso ya ce zai iya aiki tare da shugaban kasar.
Asali: Legit.ng
