Gwamnan APC Ya Cika Baki kan Tazarcen Tinubu, Ya Aika Sako ga 'Yan Hadaka

Gwamnan APC Ya Cika Baki kan Tazarcen Tinubu, Ya Aika Sako ga 'Yan Hadaka

  • Gwamnan jihar Ebonyi, Francis Nwifuru ya nuna goyon bayansa ga tazarcen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027
  • Francis Nwifuru ya bayyana cewa tazarcen Tinubu wani abu ne da Allah ya riga ya ƙaddara zai auku
  • Gwamnan ya nuna cewa babu wata haɗakar ƴan adawa da za ta iya hana a sake zaɓen Shugaba Tinubu a zaɓen 2027

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Ebonyi - Gwamnan jihar Ebonyi, Francis Nwifuru ya yi magana kan tazarcen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027.

Gwamna Nwifuru ya bayyana cewa sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a shekarar 2027 abu ne da ba za a iya dakatar da shi ba, kuma Allah ne Ya ƙaddara hakan.

Gwamna Nwifuru ya goyi bayan tazarcen Tinubu
Gwamna Nwifuru ya ce Tinubu zai yi tazarce a 2027 Hoto: @FrancisNwifuru, @DOlusegun
Source: Twitter

Gwamna Nwifuru ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi a taron yankin Kudu Maso Gabas na jam’iyyar APC da aka gudanar a Abakaliki, babban birnin jihar Ebonyi, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

Sarkin Daura ya fadi dalilin goyon bayan tazarcen Shugaba Tinubu a 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Nwifuru ya magantu kan tazarcen Tinubu

Gwamna Nwifuru ya ce fitowar Tinubu a matsayin shugaban ƙasa a 2023 nufin Allah ne, ba na mutum ba, yana mai jaddada cewa babu wata haɗaka ko ƴan adawa da za su iya hana nasararsa a 2027.

Ya yi kira ga ƴan adawa da masu sha’awar takara su janye burinsu su mara wa gwamnatin Shugaba Tinubu baya.

“Allah ne Ya zaɓi Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya zama shugaban Najeriya, saɓanin ra’ayi da fatan akasin hakan da ƴan adawa suka yi a 2023."
"Babu wani irin ƙawance da zai iya hana cikar nufin Allah a 2027."

- Gwamna Francis Nwifuru

Ya yabawa manufofin tattalin arziƙin da Shugaba Tinubu ke aiwatarwa, inda ya bayyana shi a matsayin shugaba mai jarumtaka da ke da zuciyar ɗaukar matakai masu tsauri don farfaɗo da ƙasa.

Gwamna Nwifuru ya yi kira ga ƴan Najeriya, musamman ma na yankin Kudu Maso Gabas, da su ci gaba da nuna haƙuri da nuna goyon baya ga shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

Gwamnan Taraba na shirin barin PDP zuwa ADC, hadiminsa ya tsage gaskiya

"Muna buƙatar wanda zai iya ɗaukar tsauraran matakai, kuma Shugaba Tinubu yana da halin yin hakan. Allah Ya yi watsi da wasu da suka tsaya takara bisa dalilan addini domin Shi ya san zukatan kowa, shi ya sa Ya kawo Tinubu."

- Gwamna Francis Nwifuru

Gwamna Nwifuru ya ba ƴan APC shawara
Gwamna Nwifuru ya bukaci a daina nuna fin karfi wajen fitar da 'yan takara Hoto: @FrancisNwifuru
Source: Facebook

Gwamna Nwifuru ya ba ƴan APC shawara

Yayin da yake taɓo batun harkokin cikin jam’iyya, Nwifuru ya gargaɗi ƴaƴan jam’iyyar APC da su guji naɗa ƴan takara da ƙarfi da yaji, yana mai jaddada muhimmancin haɗin kai da dimokuraɗiyyar cikin gida.

"Ba daidai ba ne a riƙa ƙarfa-ƙarfa kan ƴan takara yayin zaɓe. Dole ne mu rungumi bambance-bambancen ra’ayi mu haɗa kai domin tabbatar da nasarar Shugaba Tinubu."

- Gwamna Francis Nwifuru

APC ta caccaki PDP kan sukar Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar APC ta yi wa PDP maartani mai zafi kan sukar Shugaba Bola Tinubu.

APC ta bayyana PDP a matsayin tamkar mara lafiyan da ke taɓin hankali, kuma ba ta san yadda ake tafiyar da ƙasa.

Martanin na APC dai na zuwa ne bayan da PDP ta bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ba zai yi kasuwa ba a zaɓen 2027.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng