Atiku Abubakar Ya Shiga Rikicin Peter Obi da Gwamna, Ya Ce An Taɓa Ƴan Najeriya

Atiku Abubakar Ya Shiga Rikicin Peter Obi da Gwamna, Ya Ce An Taɓa Ƴan Najeriya

  • Alhaji Atiku Abubakar ya sa baki kan zargin yi wa tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi barazana bayan ziyarar da ya kai jihar Edo
  • Ce-ce-ku-ce ya barke kan gargaɗin da Gwamna Monday Okpebholo ya yiwa Obi cewa ya nemi izini kafin zuwa jihar, lamarin da ake ganin barazana ce
  • Atiku ya bayyana cewa barazana ga Peter Obi, tamkar barazana ce ga dukkan ƴan Najeriya ciki har da shi kansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya ce duk wata barazana da aka yi wa ɗan takarar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, barazana ce ga dukkan ’yan Najeriya.

Kalaman na Atiku na zuwa ne bayan furucin Gwamnan Edo, Monday Okpebholo, wanda ya gargadi Obi da kada ya sake zuwa jihar ba tare da samun izinin tsaro ba.

Kara karanta wannan

ADC: Atiku da El Rufai sun fara fuskantar abin da ba su yi tsammani ba daga manyan Arewa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar.
Atiku ya ce barazanar da aka yiwa Peter Obi ta shafi gaba ɗaya ƴan Najeriya Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Da yake martani a shafinsa na X kan wannan gargaɗi na gwamnan Edo, wanda ya haddasa ce-ce-ku-ce, Atiku ya ce sukar Obi tamkar barazana ce ga ƴan Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda rikicin Obi da gwamnan Edo ya fara

Rikicin ya samo asali ne daga ziyarar da Peter Obi ya kai Benin a ranar 7 ga Yuli 2025, inda aka tarbe shi hannu bibbiyu lokacin da ya je makarantar horar da malaman jinya da ke Asibitin St. Philomena.

A yayin ziyarar, Obi ya bayar da gudummawar Naira miliyan 15 domin taimakawa wajen karasa wasu ayyuka da ake yi a makarantar, rahoton Daily Trust.

Sai dai Gwamna Okpebholo ya nuna damuwa da cewa Obi ya zo ne daidai lokacin da ake fuskantar karuwar matsalar tsaro a jihar, musamman hare-haren da ake kai wa malamai da shugabannin addini.

Gwamnan Edo ya kare kalamansa

A wata sanarwa da Babban Sakataren Yaɗa Labaran Gwamnan, Fred Itua, ya fitar, Okpebholo ya ce ba a bi matakan tsaro na wajibi ba kafin zuwan Obi, rahoton Channels tv.

Kara karanta wannan

Batan maciji ya birkita ƴan Kano, Sanusi II ya roƙi kwamishinan ƴan sanda alfarma

Da yake kare gwamnan, Fred Itua ya ce:

“Gwamna bai yi wa Obi wata barazana ba, kawai dai ya jaddada cewa ya zama wajibi manyan mutane, musamman ƴan siyasa, su sanar kuma su nemi izinin daga gwamnati kafin su shigo cikin Edo."

Duk da ƙoƙarin warware batun, furucin Gwamnan ya fuskanci suka sosai, har ma daga ’yan majalisar dattijai na jam’iyyar LP.

Peter Obi tare da Atiku Abubakar.
kalaman gwamnan Edo sun haddasa cece kuce a Najeriya Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Atiku da sanatocin LP sun maida martani

A wata sanarwar haɗin gwiwa da Sanatoci Victor Umeh, Ireti Kingibe, Ezea Okey da Tony Nwoye suka sanya wa hannu, sun soki gwamnan Edo, suna mai cewa hakan ya nuna bai san aikinsa ba.

A nasa martanin, Atiku Abubakar ya ce barazanar da aka yi wa tsohon gwamnan jihar Anambra ta shafi kowane ɗan Najeriya.

"Ku sani cewa barazana ga Peter Obi ko wani daga cikinmu, barazana ce gare mu duka," inji Atiku.

Ana zargin Atiku ne ɗan takarar ADC a 2027

A wani labarin, kun ji cewa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, Dumebi Kachikwu ya ce babu wata manufar ceto Najeriya a sabuwar haɗakar ƴan adawa.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: An gano abin da ya hana Atiku shiga ADC bayan ya baro Jam'iyyar PDP

Kachikwu ya yi zargin cewa Atiku ya shirya wannan haɗaka ne ba don komai ba sai don cika burinsa na neman mulkin Najeriya.

A cewarsa, shi kansa Peter Obi ya fara fahimtar manufar haɗakar ADC don haka ya fara neman wasu hanyoyin tsayawa takara.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262