Ana Neman Haɗa Atiku da Peter Obi Faɗa bayan Gano Wanda ADC ke Shirin ba Takara a 2027

Ana Neman Haɗa Atiku da Peter Obi Faɗa bayan Gano Wanda ADC ke Shirin ba Takara a 2027

  • Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, Dumebi Kachikwu ya yi zargin cewa haɗakar ƴan adawa shiri ne domin cika burin Atiku Abubakar
  • Kachikwu ya bayyana cewa duk wani tsari da ADC ta ɗauko ya nuna Atiku Abubakar take shirin bai wa takarar shugaban ƙasa a 2027
  • A cewarsa, shi kansa Peter Obi ya fara fahimtar manufar haɗakar ADC don haka ya fara neman wasu hanyoyin tsayawa takara a zaɓe mai zuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Dumebi Kachikwu, ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC a zaɓen 2023, ya ce an gama shirya yadda za a ba Atiku Abubakar takarar shugaban ƙasa a 2027.

Ya yi ikirarin cewa haɗakar ƴan adawa da ta rungumi ADC a matsayin jam'iyyar da za ta yi amfani da ita, ta gama tsara wanda za ta ba tikitin karawa da APC mai mulki.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: An gano abin da ya hana Atiku shiga ADC bayan ya baro Jam'iyyar PDP

Peter Obi da Atiku Abubakar.
Dumebi Kachikwu ya yi ikirarin cewa Atiku ake shirin ba takara a inuwar ADC Hoto: Peter Obi, Atiku Abubakar
Source: Facebook

Kachikwu ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a shirin siyasa a yau na kafar watsa labaran Channels tv.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

ADC: Yadda aka haɗa ƙawancen ƴan adawa

Tun bayan da wasu jagororin ‘yan adawa suka rungumi jam’iyyar ADC a farkon wannan wata, Kachikwu ya rika sukar wannan haɗaka.

Daga cikin shugabannin wannan ƙawance akwai Atiku Abubakar, tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na LP, Peter Obi.

Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai da tsohon shugaban APC na ƙasa, John Oyegun da wasu manyan jiga-jigai na cikin wannan haɗaka da aka yi a ADC.

A makon da ya gabata, Atiku Abubakar, wanda ɗaya ne daga cikin waɗanda suka kafa PDP, ya fice daga jam’iyyar. Ana sa ran zai shiga ADC a hukumance nan gaba.

Ana shirin haɗa Atiku da Peter Obi faɗa a ADC

“Gaba ɗayan tsarin da aka ɗauko a ADC an yi shi shi ne domin tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar,” inji Kachikwu.

Kara karanta wannan

2027: Atiku ya fara fuskantar matsala a ADC kwanaki kaɗan bayan ya fice daga PDP

Kachikwu ya kuma yi zargin cewa Peter Obi na shirin barin ƙawancen domin ya bi wata hanya wajen cimma burinsa na takarar shugaban ƙasa, rahoton The Cable.

Tsohon dan takarar shugaban kasa na ADC, Dumebi Kachikwu.
Kachikwu ya ce Peter Obi ya fara fahimtar munafurcin da aka shirya a ADC Hoto: Dumebi Kachikwu
Source: Twitter
"Muna ganin abin da ke faruwa, shi kansa Mr Peter Obi yanzu ya fahimci cewa wannan ƙawance duk an shirya shi ne domin Atiku Abubakar.
"A fahimtar mu, abin da muke gani yanzu shi ne Obi ya fara laluben wata mafitar, sauran masu sha’awar tsayawa takara sun fahimci haɗakar wata motar Atiku Abubakar ce kawai domin cika burinsa na mulki.”

- Dumebi Kachikwu.

Me ya hana Atiku shiga ADC bayan baro PDP?

A wani labarin, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar na shirin zuwa da kansa ya karbi katin zaman dan jam'iyyar haɗaka ADC.

Wannan shiri na Atiku ne ya jawo jinkirin sauya sheƙarsa zuwa ADC a hukumance tun bayan sanar da ficewa daga babbar jam'iyyar adawa watau PDP.

Wata majiya ta ce Atiku ya gama shirya yadda zai je ya karɓi katin ADC ta yadda zai ja hankalin ƴan Najeriya amma tafiye-tafiye da rasuwar Buhari sun kawo masa cikas.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262