Ana Hasashen Nasarar Tinubu a 2027 bayan Haduwa da Kwankwaso a Aso Villa
- Reno Omokri ya saki hoton Rabiu Kwankwaso yana cewa Shugaba Bola Tinubu zai lashe zabe a 2027 duk da sukar wasu 'yan adawa
- Omokri bai ambaci suna kai tsaye ba, amma ya caccaki wanda ke cewa zai kawar da Tinubu a 2027, wanda wasu ke zargin Nasir El-Rufai ne
- ‘Yan Najeriya da dama sun mayar da martani ga hoton da Omokri ya saka, suna tofa albarkacin bakinsu dangane da zaben 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - 'Dan jam'iyyar PDP, Reno Omokri, ya janyo ce-ce-ku-ce bayan ya wallafa hoton Rabiu Musa Kwankwaso, yana hasashen cewa Bola Ahmed Tinubu zai sake lashe zabe a 2027.
Hoton ya haifar da martani daga jama’a saboda kalaman Omokri da suka yi kama da sukar wasu fitattun ‘yan adawa da ke fatan ganin bayan gwamnatin APC.

Source: Twitter
Reno Omokri ya bayyana hakan ne cikin wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ya yi wa wani dan adawa raddi ba tare da ambaton sunansa ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Omokri ya soki masu adawa da Tinubu
A karkashin hoton Kwankwaso da Tinubu da ya wallafa yana fatan samun nasara ga shugaban kasar a 2027, Reno Omokri ya ce:
"Kuma wani karamin mutum a siyasa, mai karamin jiki yana alfahari da cewa zai kifar da Shugaba Tinubu a 2027!"
Ko da yake bai faɗi suna kai tsaye ba, amma wasu sun ce kalamansa sun nuna yana nuni ne ga tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, wanda a baya ya sha alwashin kawar da Tinubu a 2027.
El-Rufai ya yi ikirarin kifar da Tinubu
A wani taro da aka gudanar a Katsina, El-Rufai ya ce hadakar jam’iyyun adawa za su sauya gwamnatin Tinubu a 2027.
Daily Trust ta wallafa cewa El-Rufa'i ya ce ministan sadarwa, Bosun Tijani, zai ci gaba da rike mukaminsa a gwamnatin da za su kafa, yayin da Tinubu zai bar kujerarsa.
Ya jaddada cewa akwai bukatar sauyi a tsarin mulkin Najeriya, kuma jam’iyyun adawa na hada kai domin cimma wannan buri.

Source: Twitter
Martanin ‘yan Najeriya ga hoton Omokri
Wani mai suna Ndako Ndagi ya yi maganar da ta ke nuna shakkun Kwankwaso zai iya jawo wa Tinubu nasara a 2027.
Ya ce:
"Hahaha, amma a matsayin dan takarar shugaban kasa, mutumin ya ci jiha daya kacal, hakan ya sa ake kiran sa shugaban kasar Kano."
Shi kuma Michael Nwankwo ya bayyana cewa da yunwa za su yi yaki, yana mai nuna cewa bai damu da waye abokin takarar Tinubu ba:
"Yunwa za mu kawar, ranka ya dade.”
Olayemi Festus Oke ya rubuta cewa:
"Idan Kwankwaso ne mataimakin shugaban kasa, Kano ta tabbata. Idan muka ci Lagos da Rivers, za mu ga yadda ‘yan ADC za su iya karbe mulki.”
Wani mai suna Godspower Omesah ya ce:
"Idan Atiku da Obi suka hada kai, to Tinubu zai dawo Lagos a 2027.”
APC ta yi wa PDP martani kan zaben 2027
A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar APC ta yi martani kan wasu maganganu da PDP ta yi kan nasarar Bola Tinubu a 2027.
Wani jigo a jam'iyyar PDP ne ya yi magana yana mai cewa zaben 2027 ba zai yi wa APC da Bola Tinubu kyau ba.
Sai dai kakakin APC, Bala Ibrahim ya bayyana cewa maganar PDP ba gaskiya ba ne, domin Tinubu na kara samun karbuwa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


