An soki Rarara kan Rashin Ta'aziyya ga Buhari, Ya Wallafa Bidiyon da Ya Tayar da Ƙura

An soki Rarara kan Rashin Ta'aziyya ga Buhari, Ya Wallafa Bidiyon da Ya Tayar da Ƙura

  • Mawaƙin siyasa, Dauda Abdullahi Kahutu Rarara ya fuskanci suka daga masoyan Muhammadu Buhari saboda rashin yin ta’aziyya bayan ya rasu
  • Duk da Rarara ya saki bidiyo inda ya ce “Allah ya jiƙan maza”, amma bai kira sunan Buhari kai tsaye ba, abin da ya janyo cece-kuce
  • Masu amfani da kafafen sada zumunta sun bayyana rashin jin daɗi, inda wasu ke kallon saƙon Rarara a matsayin rashin girmamawa ga Buhari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Ana ta ce-ce-ku-ce game da mawakin siyasa, Dauda Abdullahi Kahutu Rarara bayan rasuwar Muhammadu Buhari.

Mawaki Rarara na ci gaba da fuskantar matsin lamba daga masoyan Marigayi Muhammadu Buhari, tsohon shugaban ƙasa da ya rasu kwanan nan.

An taso Rarara a gaba bayan rasuwar Buhari
An caccaki Rarara kan rashin ta'aziyya kan rasuwar Buhari. Hoto: Bashir Ahmad, Dauda Kahutu Rarara.
Source: Facebook

Rasuwar Buhari: Rarara ya wallafa bidiyo

Rarara ya wallafa wani bidiyo a Facebook da ake binne Buhari amma bai kira sunansa kai tsaye ba yayin da yake addu'a.

Kara karanta wannan

Gaskiya ta ƙara fitowa, an ji babban abin da ya hana Buhari korar wasu ministoci a mulkinsa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan ya jawo suka daga wasu mutane da suke cewa Buhari bai cancanci haka daga gare shi ba.

Bayan rasuwar Buhari, mutane da dama sun yi ta jiran yadda Rarara zai bayyana jimaminsa game da rasuwar tsohon jagoransa amma shiru.

Rarara ya yi wa Buhari waƙoƙi tun daga shekarar 2015 har zuwa ƙarshen mulkinsa a 2023, yana nuna soyayya da ƙauna da kuma biyayya gare shi.

Sai dai bayan saukar Buhari daga mulki, dangantakar sa da Rarara ta dusashe, inda ya soki gwamnatin da ya ce ta lalata kasar.

Hakan ya haddasa cece-kuce, har aka gurfanar da Rarara a gaban kotu, amma daga bisani al’amari ya lafa kuma ya ci gaba da waƙa wa Tinubu.

Bayan rasuwar Buhari a London, an kawo gawarsa Daura domin jana’iza, amma Rarara bai ce komai ba har sai bayan kwana uku.

Ya fitar da faifen bidiyo inda ya ce:

Kara karanta wannan

Hakeem Baba: Dattijon Arewa ya tsage gaskiya kan 'kurakuran' Buhari

“Allah ya jiƙan maza, Allah ya sa mutuwa hutuce."
Ana zargin Rarara da butulci bayan rasuwar Buhari
Mutane da dama sun soki Rarara saboda kin ta'aziyya kan rasuwar Buhari. Hoto: Muhammadu Buhari.
Source: UGC

An yiwa Rarara rubdugu bayan rasuwar Buhari

Sai dai mutane da dama sun fusata da wannan saƙo, saboda Rarara bai ambaci sunan Buhari kai tsaye ba.

Wasu sun zargi cewa Rarara bai so ya ambaci Buhari domin Tinubu ne ke mulki yanzu, duk da cewa shugaban kasa ya mutunta marigayin.

Masu amfani da shafukan sada zumunta sun nuna fushinsu, suna cewa bai kamata ya yi watsi da sunan mutumin da ya taimake shi ba.

Wannan lamari ya haifar da cece-kuce a shafin Rarara, inda aka yi musayar kalamai masu zafi tsakanin mabiyansa.

Rarara ya sha alwashin kayar da Atiku

Mun ba ku labarin cewa Dauda Kahutu Rarara ya ce ko shi ma idan ya tsaya takara zai iya kayar da 'yan adawa gaba ɗaya a zaɓen 2027 mai zuwa.

Mawakin ya zargi shugabannin haɗaka a ADC da gazawa, yana mai cewa talakawa ba za su sake amincewa da su ba.

Kahutu Rarara ya kare Bola Tinubu, yana mai cewa ya gaji kasar da Muhammadu Buhari ya lalata tun da ya rufe iyakoki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.