'Buhari a APC Ya Rasu': Hon. Ado Doguwa Ya Gargaɗi Masu Rawar Kafa a Siyasa

'Buhari a APC Ya Rasu': Hon. Ado Doguwa Ya Gargaɗi Masu Rawar Kafa a Siyasa

  • Hon. Alhassan Ado Doguwa ya ce su mabiyan Muhammadu Buhari ne kuma suna bin tafarkinsa na siyasa a jam’iyyar APC har yanzu
  • Doguwa ya bayyana cewa Buhari bai taɓa cewa ya bar jam’iyyar APC ba, don haka su ma ba za su fice daga cikinta ba
  • Ya jaddada cewa za su ci gaba da mara wa Shugaba Bola Tinubu baya a APC, domin Buhari ya bar su a wannan tafarki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Dan majalisar tarayya daga jihar Kano, Hon. Alhassan Ado Doguwa ya yi magana kan siyasar marigayi Muhammadu Buhari.

Hon. Doguwa da ke wakiltar Tudunwada/Doguwa ya bayyana cewa irin akidar siyasar Buhari suke bi kuma suna yi wa jam'iyyar APC biyayya.

Ado Doguwa ya yaba kalar siyasar Buhari
Hon. Ado Doguwa ya ce suna APC kamar yadda Buhari ya mutu a cikinta. Hoto: Hon. Alhassan Ado Doguwa.
Source: Twitter

Ado Doguwa ya yabawa da siyasar Buhari a APC

Kara karanta wannan

'Babu kuɗi': Yadda Buhari ya roƙi gwamnoni su tara N700m kafin ya biya su daga baya

Hakan na cikin wani faifan bidiyo da Salisu Mijinyawa ya wallafa a shafin Facebook a yau Lahadi 20 ga watan Yulin 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin bidiyon, Ado Doguwa ya ce duk wanda yake yin siyasa saboda Buhari to yanzu ya koma ga Allah.

Ya ce kuma har marigayi ya bar duniya babu inda ya furta cewa ya bar jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya.

Ya ce:

"Duk wanda ke siyasa don Buhari malaminsa ne, to ya sani Muhammadu Buhari ya koma ga Allah a matsayin dan APC.
"Tun da muke da mai girma shugaban kasa, mu da muke tare da shi mu gana a bayyane ko a sirri, Buhari babu inda ya yi furuci ya ce ya bar jam'iyyar APC."
An yabawa dogewar Buhari a siyasa kafin rasuwarsa
Hon. Ado Doguwa ya ce za su goyi bayan Tinubu kamar yadda Buhari ya yi. Hoto: Muhammadu Buhari.
Source: Twitter

Ado Doguwa ya fadi wanda za su zaba a 2027

Hon. Doguwa ya ce suna alfahari da Buhari ganin cewa ya mutu a tafarkin Allah da kuma ma'aiki Annabi Muhammad SAW.

Doguwa ya ce a matsayinsu na mabiyan Buhari ya rasu ya bar su a tafarkin APC don haka babu abin da zai kawar da su.

Kara karanta wannan

Shin Allah zai yafewa Buhari ko da al'umma ba su yafe masa ba? Sheikh ya yi bayani

Ya jaddada cewa babu wani wanda zai hana su goyon bayan APC da kuma Shugaba Bola Tinubu a zaben da ke tafe.

"Saboda haka muna alfahari Muhammadu Buhari ya mutu a tafarkin Allah da kuma Annabi Muhammadu SAW.
"Mu mabiyansa da ya bari a bayan kasa kuma mu ke siyasa irin ta sa ya bar mu ne a tafarkin jam'iyyar APC.
"Shugaban kasa Bola Tinubu za mu yi da jam'iyyar APC a zabe ko kana so ko ba ka so."

Ado Doguwa ya soki masu shiga APC

Kun ji cewa Hon. Alhassan Ado Doguwa ya bayyana cewa shi da sauran manya a jam'iyyar APC ba sa tsoron kowa ya shiga jam’iyya mai mulkin Najeriya.

Dan majalisar, mai wakiltar Tudunwada/Doguwa na wannan batu ne awanni kadan bayan haduwarsu da Rabi'u Musa Kwankwaso da a lokacin ake zargin zai dawo APC.

Ya kara da cewa duk wanda ke son ya shiga APC, sai ya yi biyayya da Shugaban jam'iyyar a wancan lokaci, Dr. Abdullahi Umar Ganduje wanda a yanzu ya yi murabus daga kujerarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.