Jigawa: Bayan Mutuwar Ɗan Majalisa, APC, NNPP Sun Fitar da Ƴan Takara domin Maye Gurbinsa

Jigawa: Bayan Mutuwar Ɗan Majalisa, APC, NNPP Sun Fitar da Ƴan Takara domin Maye Gurbinsa

  • Jam’iyyun APC da NNPP sun fitar da ‘yan takararsu ta hanyar lumana domin zaɓen cike gurbi na dan majalisar tarayya da ya rasu
  • Hukumar zaben mai zaman kanta a Najeriya ta sanar da sake zaben cike gurbi a mazabar Babura/Garki da za a yi a watan Agusta
  • Rabi’u Mukhtar Garki ya lashe zaɓen fidda gwani na APC da kuri’u 110, yayin da NNPP ta tsayar da Salisu Sabo ba tare da hamayya ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Dutse, Jigawa - An fara shirye-shiryen gudanar da zaben cike gurbin dan majalisar tarayya daga jihar Jigawa da ya rasu.

Jam’iyyun APC da NNPP sun fitar da ‘yan takararsu ta hanyar lumana domin zaɓen cike gurbi na mazabar Babura/Garki da za a yi.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Ɗan majalisar wakilai ya bi sahun Atiku, ya fice daga jam'iyyar PDP

Za a yi zaben cike gurbin dan majalisa a Jigawa
APC da zaben cike gurbi a Jigawa. INEC Nigeria.
Source: Twitter

Jigawa: APC, NNPP sun shirya zaben cike gurbi

Rahotanni daga jihar sun nuna cewa jam’iyyun sun gudanar da zaɓen tantancewa a garin Babura, hedkwatar mazabar Babura/Garki, cewar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan zaɓen cike gurbi ya biyo bayan rasuwar Hon. Isah Dogon Yaro, wanda ya wakiltar mazabar, a ranar 9 ga Mayu, 2024.

Hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) ta sanya ranar 16 ga Agusta, 2025, domin gudanar da zaɓen cike gurbin a mazabar Babura/Garki.

Alhaji Rabi’u Mukhtar Garki ya zama ɗan takarar APC bayan samun kuri’u 110, wato dukkanin kuri’un da aka kada a zaɓen fidda gwani.

Shugaban kwamitin zaɓen APC, Hon. Ismaila Ahmad Gadaka, ya ce zaɓen ya gudana lafiya kuma cikin adalci ba tare da wata matsala ba.

Ya ce:

“Alhaji Rabi’u Mukhtar Garki, wanda aka zaɓa ta cikin lumana , ya samu kuri’u 110, kuma ya cika duk sharuɗɗan jam’iyya, don haka ya yi nasara.”

Haka kuma, shugaban APC na jihar, Hon. Aminu Sani Gumel, ya bayyana jin daɗinsa game da yadda aka gudanar da zaɓen cikin lumana da doka.

Kara karanta wannan

Guguwar Atiku ta janye tsohon dan takarar shugaban kasa zuwa ADC

An yi zaɓen fitar da gwani na APC da NNPP
Za a yi zaben maye gurbin marigayi dan majalisa a Jigawa. Hoto: Umar Namadi.
Source: Facebook

Jigawa: NNPP ta fitar da dan takara

A gefe guda, NNPP ta gudanar da nata zaɓen a Babura, inda Salisu Sabo ya zama ɗan takara ba tare da hamayya ba.

Shugaban zaɓen fidda gwani na NNPP, Hon. Muhammad Sunusi Gako, ya ce Salisu Sabo ya samu kuri’u 114, kuma ya zama ɗan takarar jam’iyya.

A jawabinsa, Salisu Sabo ya sha alwashin yin aiki tare da jama’ar mazabar domin inganta ilimin sakandare a yankin, Daily Post ta ruwaito.

Yar jarida za ta tsaya takarar zaɓe

Mun ba ku labarin cewa 'yar jarida Amina Dogon-Yaro ta ajiye aikinta a NTA bayan shekaru 15, don ta tsaya takarar majalisar tarayya a Garki/Babura.

Amina ta bi dokar ƙasa ta ajiye aiki kwanaki 30 kafin zaɓe, kuma ta miƙa takardar murabus tare da shaidar biyan albashi na watanni uku.

Jama'a sun nuna goyon baya da fatan alheri ga burin Amina Dogon-Yaro, yayin da suke ƙarfafa gwiwar sauran mata su shiga fagen siyasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.