Yadda Yan PDP ke Rokon Kwankwaso, Abba Su Sauya Sheka a Kano
- Daya daga cikin jiga-jigan PDP, Hon. Zainab Abdu Bako ta miƙa buƙatarta ga gwamnatin Abba Kabir Yusuf da Rabi'u Musa Kwankwaso
- Ta ce lallai shugabannin biyu sun dawo PDP, ganin cewa yanzu ita ce jam'iyyar da ta fi dace wa da su idan aka kwatanta da APC ko ADC
- A kalamanta, akwai yiwuwar Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya samu tikitin zama ɗan takarar shugaban kasa idan ya dawo PDP
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Jigo a PDP reshen jihar Kano, Hon. Zainab Audu Bako, ta bayyana fatan wasu daga cikin ƴan jam’iyyarta game da gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf.
Haka kuma, ta bayyana cewa sun jima suna aiki tare da tsohon dan takarar shugaban ƙasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.

Kara karanta wannan
Sauya sheƙar Atiku ta rikita PDP da APC, tsofaffin gwamnoni da jiga jigai sun bi sahunsa

Source: Twitter
A wata hira da ta yi da gidan rediyon Express, wadda aka wallafa a shafin Facebook, Hon. Zainab ta ce suna rokon gwamnan Kano da ya sauya sheƙa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rokon ƴar PDP ga Abba, Kwankwaso
Hon. Zainab Audu Bako ta ƙara da cewa, a matsayinsa na gwamna mai rike da madafun iko a Kano, PDP ce ta fi dacewa da shi.
Ta ce:
“Injiniya Abba Kabir Yusuf, ka yi wa Allah, ka dawo gida — ka dawo PDP.”
“Shi kuma jagora, ina kira gare shi, shi ma ya dawo PDP. Abin da ya sa na ce haka, dama ce da zai iya amfani da ita.”
Ta bayyana cewa dukkanninu asali daga PDP suka fito, kuma lokaci ya yi da za su dawo gida saboda muhimmancinsu ga jam’iyyar.
Zainab: 'Mun son Kwankwaso ya dawo PDP'
Hon. Zainab ta bayyana cewa Kwankwaso na da damar samun tikitin takarar shugaban kasa a PDP idan ya dawo cikin jam’iyyar.
A cewarta, idan ya koma APC, ba zai yiwu a sake tsayar da Musulmi a matsayin shugaban ƙasa da mataimaki ba.

Source: Facebook
Ta ce idan har akwai yiwuwar tsayar da dan Arewa takarar shugaban ƙasa, to Kwankwaso na daga cikin mutane da suka dace.
Hon. Zainab ta ce:
“Dama tun da muke tare da shi, ai fata muke ya zama shugaban ƙasa.”
A kalamanta, ADC ba za ta iya yi da Kwankwaso ba, domin jam’iyya ce yar koyo da aka kafa domin don zuciya.
Ta ce:
“ADC, ƴan koyo ne. Manyan iyayenmu sun koma ciki ne saboda suna da manufa ta kawar da gwamnatin APC.”
A ganinta, PDP ce kadai jam'iyyar da Kwankwaso zai iya samun dama yadda ya kamata, saboda a cewarta, jam'iyya ce da ke aiki da jama'a kuma aka samar saboda talakawa.
NNPP ta magantu kan sauya shekar Kwankwaso
A baya, kun ji cewa Shugaban NNPP na jihar Kano, Hashimu Dungurawa, ya karyata jita-jitar da ke yawo cewa Rabi’u Musa Kwankwaso zai sauya sheka zuwa ADC.

Kara karanta wannan
Buhari: Diyar tsohon shugaban kasa ta fadi halin da ta shiga bayan rasuwar mahaifinta
Dungurawa ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a ranar Litinin, yayin da ake rade-radin cewa Sanata Kwankwaso ya fice daga NNPP.
Hashimu Dungurawa ya ce babu gaskiya a jita-jitar da ke cewa dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP a zaben 2023 yana shirin ficewa daga jam’iyyar zuwa ADC.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
