APC Ta Samu Rauni a Kaduna, Makusancin El Rufa'i Ya Fice da Magoya bayansa

APC Ta Samu Rauni a Kaduna, Makusancin El Rufa'i Ya Fice da Magoya bayansa

  • Tsohon jigo a APC ta jihar Kaduna, Mukhtar Lawal Baloni ya sanar da ficewarsa daga jam'iyya mai mulki
  • Ya ce fita daga cikin APC ta zama dole saboda ta sauka daga gwadaben da aka samar da ita a kai na tausayin jama'a
  • Baloni, wanda tsohon shugaban karamar hukumar Kaduna ta Arewa ne ya ce akwai matsala a APC yanzu haka

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna – Tsohon shugaban karamar hukumar Kaduna ta Arewa, Mukhtar Lawal Baloni, ya fice daga jam’iyya mai mulki ta APC.

Ya ce barin APC ya zama dole sakamakon babban bambanci da aka samu tsakanin aƙidunsa na siyasa da yadda jam’iyyar ke tafiya a yanzu.

Tsohon jigo a APC, Mukhtar Lawal Baloni da Uba Sani
Mukhtar Baloni ya bar APC Hoto: @muktarbaloni/Uba Sani
Source: Facebook

Baloni ya wallafa a shafinsa na X cewa ya fice tare da wasu magoya bayansa da suka haɗa da tsohon mataimakinsa, Dahiru Abdullahi Maidace.

Kara karanta wannan

ICRC ta gano babbar matsalar da ta tunkaro Arewa sakamakon ta'addanci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran sun haɗa da tsohon shugaban ma’aikatansa Ghali Mohammed Waziri, da wasu tsofaffin mashawarta na musamman, tsofaffin kansiloli da shugabannin jam’iyya a yankinsa.

Dalilin Mukhtar Baloni na barin APC

Daily Trust ta wallafa cewa a cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu, Baloni ya ce ba zai iya ci gaba a cikin jam'iyyar da aƙidunsu ke karo da juna ba.

Ya kara da cewa a baya, jam'iyyar APC ta samu karɓuwa saboda kyakkyawan zaton da ake yi mata na tallafa wa ƙasa.

APC ta yo martani ga Baloni
APC ta ce ko a jikinta don Baloni ya fice daga jam'iyya Hoto: Uba Sani
Source: Facebook

A cewarsa:

“Jam’iyyar a lokacin da muka san ta, ta kasance dandalin da ke ƙoƙarin cika burin ‘yan Najeriya cikin gaskiya da nagarta.”

Baloni ya yi takaicin lalacewar aƙidun APC

Baloni ya bayyana takaici game da yadda ya ce APC ta sauya daga aƙidunta na farko da kuma yadda karɓuwarta ke raguwa a siyasa.

Ya yi kira da a taru a gina sabuwar jam’iyya wacce za ta kasance mai gaskiya da rikon amana, da kuma adalci ga kowa hidima ga jama’a.

Kara karanta wannan

APC ta sanya ranar gudanar da babban taro, ana neman magajin Ganduje

Sauya sheƙar Mukhtar Lawal Baloni na daga cikin sauye-sauyen da PDP ke fuskanta tun bayan ficewar tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i zuwa SDP.

Martanin jam'iyyar APC ga Baloni

Da yake martani, sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar APC a Kaduna, Salisu Tanko Wusono, ya ce babu abin da ficewar Baloni zai sauya.

Ya ce waɗanda ke ficewa na barin APC be ba don cewa Gwamna Uba Sani ko jam’iyyar APC sun gaza ba, sai dai wataƙila dalilai na kashin kai ne.

A cewarsa:

"Abin da muke maida hankali a kai a APC shi ne ƙarfafa alaƙar jam’iyya da mutanen Jihar Kaduna. Ba laifi ba ne mutum ya ga cewa ra’ayinsa na kashin kai bai dace da na jama’a ba a Kaduna. Idan yana so ya tafi, babu abin da za a iya yi.”

APC ta fara neman magajin Ganduje

A baya, mun wallafa cewa Jam’iyyar APC mai mulki na shirin gudanar da taron Kwamitin Zartaswa na Ƙasa a ranar Alhamis mai zuwa a babban birnin tarayya.

Za a yi zaman ne domin tattauna muhimman batutuwa da suka shafi makomar jam’iyyar, musamman nemi wanda zai gaji Abdullahi Umar Ganduje.

Majiyoyi sun bayyana cewa daya daga cikin dalilan kiran taron NEC shi ne domin yanke hukunci game da makomar Ali Dalori, muƙaddashin shugaban APC na ƙasa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng