'Zai Dawo': PDP Ta Yi Watsi da Ficewar Atiku, Ta Faɗi Babban Abin da Zai Dawo da Shi

'Zai Dawo': PDP Ta Yi Watsi da Ficewar Atiku, Ta Faɗi Babban Abin da Zai Dawo da Shi

  • Atiku Abubakar ya fice daga jam’iyyar PDP karo na uku, yana mai cewa jam’iyyar ta kauce daga tushen manufofin da aka kafa ta a kai
  • Shugaban riko na PDP, Umar Damagum ya bayyana cewa ficewar Wazirin Adamawa ba sabon abu ba ne, domin PDP ta saba da ganin haka
  • Ya kara da cewa jam’iyyar ba ta damu ba domin tana da yakini cewa Atiku zai dawo, tunda hakan ya zama wani salon siyasarsa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Mukaddashin shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Umar Damagum, ya yi magana bayan ficewar Atiku Abubakar daga cikinta.

Damagum ya bayyana ficewar tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar daga jam’iyyar a matsayin abu da aka saba da shi.

Damagum ya yi magana bayan Atiku ya bar Atiku
Damagum ya ce PDP ba ta damu da ficewar Atiku ba. Hoto: People's Democratic Party, PDP.
Source: Twitter

Da yake magana da manema labarai a Bauchi, Damagum ya ce ficewar Atiku ba sabon abu ba ne, domin sun saba da hakan, cewar Premium Times.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Ɗan majalisar wakilai ya bi sahun Atiku, ya fice daga jam'iyyar PDP

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku ya watsar da jam'iyyar PDP

Atiku, wanda ya tsaya takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP a 2019 da 2023, ya fice daga jam’iyyar bisa dalilin kaucewa daga tushen akidar da aka kafa jam’iyyar a kai.

A cikin wata wasika mai kwanan wata 14 ga Yuli 2025, da ya aika wa shugaban jam’iyyar PDP a mazabarsa ta Jada 1, Jihar Adamawa, Atiku ya ce ficewarsa nan take.

Ya ce:

“Na ga ya wajabta na bar PDP saboda hanyar da jam’iyyar ke bi yanzu ta saba da tushen akidun da muka tsaya a kai.
“Zuciyata cike da bakin ciki nake sanar da ficewa ta, domin na fahimci cewa akwai sabani da ba za a iya gyarawa ba."

Wannan ne karo na uku da tsohon mataimakin shugaban kasar ke barin jam’iyyar da ya taimaka wajen kafawa a shekarar 1998.

PDP ta yi watsi da ficewar Atiku daga jam'iyyar
Jam'iyyar PDP da na tabbacin Atiku zai dawo cikinta. Hoto: Atiku Abubakar, People's Democratoc Party, PDP.
Source: Facebook

Damagum ya ce Atiku zai sake dawowa PDP

Kara karanta wannan

Hadimin Wike ya taso Atiku a gaba kan ficewa daga PDP

Sai dai Damagum ya ce sun saba ganin haka a jam'iyyar daga Atiku wanda ya bar PDP har sau uku, cewar rahoton TheCable.

“Ba karo na farko bane; muna sa ran zai dawo."

- Inji Damagum

A cewarsa, jam’iyyar PDP ba ta rude ko firgita ba kan ficewar Atiku, domin sun saba da ficewarsa da dawowarsa cikin jam’iyyar sau da dama.

Shugaban riko na jam’iyyar ya ce hakan na nuna tsarin siyasar Atiku ne, ba tare da ya yanke huldar karshe da jam’iyyar ba.

Ya ce hakan ya biyo bayan rahotannin cewa Atiku Abubakar yana kokarin kafa sabon dandali mai suna ADC domin shirye-shiryen zabe mai zuwa.

Hadimin Wike ya caccaki Atiku

Kun ji cewa hadimin ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya caccaki tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar.

Lere Olayinka ya soki Atiku ne kan matsayar da ya ɗauka ta ficewa daga jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya bayan shekaru kusan 10.

Babban mai taimakawa Nyesom Wike wajen harkokin yada labarai ya zargi Atiku da rusa PDP bayan ya fice daga cikinta a shekarar 2023.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.