Ahmadu Yaro: Attajirin da Ya Shafe Shekaru Yana ba Buhari Kudin Cefane da Sauransu

Ahmadu Yaro: Attajirin da Ya Shafe Shekaru Yana ba Buhari Kudin Cefane da Sauransu

  • Buba Galadima ya fadi tarihin Alhaji Ahmadu Yaro da ya ce ya rika ba Muhammadu Buhari kudi har ya samu mulki a 2015
  • Tsohon dan siyasar ya ce su da suka dauki nauyin tallata Muhammadu Buhari a siyasa ba su samu komai daga gwamnatin sa ba
  • Duk da haka, Buba Galadima ya ce ya riga ya yafewa marigayi shugaba Muhammadu Buhari duk abinda ya faru a tsakaninsu a baya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Tsohon abokin siyasar Muhammadu Buhari, Buba Galadima, ya yi bayanai da suka ja hankali dangane da wanda ya taka rawa matuka wajen nasarar tsohon shugaban kasar.

Buba Galadima ya bayyana cewa akwai mutane da dama da suka taimaka wa Buhari tun daga tushe, amma daga bisani aka watsar da su bayan samun mulki.

Kara karanta wannan

Hakeem Baba: Dattijon Arewa ya tsage gaskiya kan 'kurakuran' Buhari

Alhaji Ahmadu Yaro da ya tallafawa siyasar Buhari da kudi tsawon shekaru
Alhaji Ahmadu Yaro da ya tallafawa siyasar Buhari da kudi tsawon shekaru. Hoto: Bashir Ahmad|Aminiya
Source: Facebook

Legit ta tattaro bayanan da Buba Galadima ya yi ne a cikin wani bidiyo da Nasir Adamu El-Hikaya ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce su da suka hada gwiwa da Buhari tsawon shekaru don ganin ya kai ga mulki an mayar da su baya a gwamnatinsa.

A cewarsa, akwai mutum guda da ya fi kowa taka rawa wajen tallafawa Buhari da dukiya – shi ne Alhaji Ahmadu Yaro, wanda ya kasance aboki kuma mai daukar dawainiyar Buhari.

Ahmadu Yaro da ya dauki nauyin Buhari

Buba Galadima ya bayyana cewa Alhaji Ahmadu Yaro wanda aka fi sani da Coca-Cola ne ya rika ba Buhari albashi da kudin cefane har ya samu mulki a 2015.

Buba Galadima ya ce mafi karancin kudin da ya ga Alhaji Ahmadu Yaro ya ba Buhari a lokaci siyasa shi ne Naira miliyan 200.

Haka kuma, shi ne ya sayo masa mota kamar yadda ya taba saya wa Sardauna da Tafawa Balewa a baya.

Kara karanta wannan

'Yadda Buhari ya yaƙi Bankin Duniya da IMF domin kare talakan Najeriya'

Daily Trust ta wallafa cewa Ahmadu Yaro ne ya fara samun lasisin fara harkar canjin kudi a Najeriya bayan samun 'yanci a 1960.

Mutanen da suka taimaki siyasar Buhari

Baya ga Alhaji Ahmadu Yaro, Buba Galadima ya lissafa wasu da suka taka rawa wajen gina tafiyar siyasar Buhari.

Wadanda ya ambata sun hada da Alhaji Wada Nass, Alhaji Sule Yahaya Hamma wanda ya shugabanci Buhari Support Organization, da Mukhtar Muhammad (Wazirin Dutse).

Sauran sun hada da Ibrahim Babankowa, Joy Nune, Oscar Udoji, Sanata Rufai Hanga wanda ya yi rajistar CPC da kudi N100,000.

Tsohon abokin Buhari, Buba Galadima
Tsohon abokin Buhari, Buba Galadima. Hoto: Kwankwasiyya Reporters
Source: Facebook

Daga cikinsu akwai Mamman Abubakar Danmusa, Dr Bashir Kurfi, Sanata Kanti Bello, Dr Armaya’u, Tijjani Zangon Daura da Sanata Muhammad Bello daga Adamawa.

Buba Galadima ya ce wadannan mutane sun sadaukar da kudi da lokaci wajen gina Buhari a siyasa amma daga baya aka raba gari da wasunsu bayan samun mulki.

Buba Galadima ya yafewa Buhari

Duk da wannan jayayya da takaici da ya fuskanta daga gwamnatin Buhari, Buba Galadima ya ce yanzu ya yafewa tsohon shugaban Najeriyan.

Kara karanta wannan

'Ya taɓa korarmu kan N15': Diyar Buhari game da tarbiyya da mahaifinsu ya ba su

Ya kara da cewa kafin rasuwar shi a 2019, Alhaji Ahmadu Yaro ya nemi sulhu tsakaninsu da Buhari amma hakan bai yiwu ba.

Alhaji Ahmadu Yaro ya rasu a 2019

A wani rahoton, mun ruwaito muku cewa a shekarar 2019 Allah ya dauki rayuwar attajirin Arewa, Alhaji Ahmadu Yaro.

Shugaban kasa na wancan lokacin, Muhammadu Buhari ya aike da sakon ta'aziyya ga iyalan Alhaji Yaro da gwamnatin jihar Jigawa.

Rahotanni sun bayyana cewa Ahmadu Yaro ya gudanar da harkokin kasuwanci a Najeriya da kasashen waje kuma ya rasu yana da shekara 96.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng