Shirin 2027: 'Yan Majalisa Sun Saye Motoci domin Kamfen din Tinubu

Shirin 2027: 'Yan Majalisa Sun Saye Motoci domin Kamfen din Tinubu

  • 'Yan majalisar jihar Kebbi sun bayar da motoci 25 ga kungiyar TKT domin goyon bayan Bola Tinubu da gwamnan jihar a 2027
  • Sai dai kungiyoyin fararen hula da 'yan adawa sun ce hakan bai dace ba ganin halin kuncin rayuwa da ake ciki a jihar
  • Kowane ɗan majalisa ya bayar da mota daya ne, amma wasu na ganin ya kamata a kashe kudin ne wajen cigaban jama’ar Kebbi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kebbi - Majalisar dokokin jihar Kebbi ta jawo ce-ce-ku-ce bayan da ta mika gudunmawar motoci 25 ga kungiyar yakin neman zaben Tinubu/Kaura ta (TKT) domin tunkarar zaben 2027.

Shugaban majalisar, Alhaji Muhammad Usman-Zuru ne ya mika motoci kirar Opel Zafira ga shugaban kungiyar a madadin mambobin majalisa 25.

Kara karanta wannan

NELFund: Gwamnatin Tinubu za ta bude dandalin taimakawa dalibai samun aiki

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa ya mika motocin yana mai cewa sun cika alkawarin da suka dauka tun lokacin kaddamar da kungiyar a watan Mayun 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai matakin ya haifar da suka daga kungiyoyin fararen hula da 'yan adawa a jihar Kebbi, suna kallon hakan a matsayin rashin dacewa da kuma nuna rashin damuwa da halin da jama’a ke ciki.

Me ya sa suka ba Tinubu motocin?

Usman-Zuru ya bayyana cewa kowanne ɗan majalisa ya bayar da mota daya domin nuna goyon baya ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Nasir Idris.

A cewarsa, gwamnan jihar Kebbi ya taka rawar gani wajen cika alkawurran zabe, kuma shugaban kasa Tinubu ya nuna kulawa ga jihar, don haka dole ne su mara musu baya a 2027.

Ya ce:

“Mulki na nufin ciyar da jama’a gaba da samar musu da ci gaba.
Gwamna Idris ya yi abin da ba a yi tsammani ba wajen cigaba. Tinubu kuwa ya bai wa jihar Kebbi kulawa ta musamman.”

Kara karanta wannan

London Clinic: Abubuwan mamaki game da asibitin da Muhammadu Buhari ya rasu

Kungiyoyi da 'yan adawa sun fusata

Shugaban haɗaɗɗiyar ƙungiyar fararen hula a Kebbi, Kwamared Ibrahim Ngaski, ya bayyana kyautar a matsayin abin takaici da rashin lura da halin da jihar ke ciki.

Ya ce jihar Kebbi na fama da matsaloli da dama kamar talauci, rashin tsaro, yara marasa zuwa makaranta da kuma bala’o’i da dama.

Gwamnan jihar Kebbi a fadar gwamnati
Gwamnan jihar Kebbi a fadar gwamnati. Hoto: Nasir Idris
Source: Twitter

Ibrahim Ngaski ya ce ya fi dacewa a yi amfani da kudin da aka kashe a kan motocin wajen gyara rayuwar al’umma.

Ngaski ya kara da cewa:

“Ko da daga albashinsu aka saye motocin, kudin harajin jama’a ne. Ya kamata a yi amfani da su wajen gyara rayuwar mutane.”

Martanin 'yan adawa a jihar Kebbi

Wani jigo a cikin ƙungiyar jam’iyyun siyasa a jihar Kebbi, Abdullahi Mustapha, ya bayyana kyautar a matsayin nuna rashin tausayi ga jama’a da suka zaɓe su.

Ya ce:

“Da irin matsin rayuwar da ake ciki a Kebbi, bai kamata a yi amfani da kudin a harkar siyasa ba. Ya kamata majalisar ta fi fifita walwalar jama’a maimakon siyasar son rai.”

Kara karanta wannan

Turawa sun zakulo Abba Kabir cikin gwamnoni, an karrama shi a London

ADC: An maka 'yan adawa a kotu

A wani rahoton, kun ji cewa wasu 'yan jam'iyyar ADC sun yi zargin cewa shugabannin hadakar 'yan adawa sun kwace musu jam'iyya.

Tsohon dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar na 2023 na cikin wadanda suka yi korafi kan zargin mamaye ADC.

A karkashin haka Legit Hausa ta rahoto cewa shugabannin jam'iyyar a jihohi 5 sun maka shugabannin adawa kara a kotu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng