2027: An Shigar da ADC Kotu bayan Atiku Ya bar PDP, Ana Son Ruguza Hadaka

2027: An Shigar da ADC Kotu bayan Atiku Ya bar PDP, Ana Son Ruguza Hadaka

  • Shugabannin ADC na jihohi biyar sun maka David Mark da wasu a kotu bisa zargin kwace jam’iyyar ta hanyar kutse
  • Dumebi Kachikwu ya ce ana bai wa shugabannin jam’iyyar na jihohi har Naira miliyan 20 domin su sauka daga mukamansu
  • A makon da ya wuce ADC ta ce APC na da hannu a shari’ar da wasu ke yi da sunan mambobin ADC ba tare da izini ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja - Shugabannin jam’iyyar ADC na jihohi biyar sun maka Sanata David Mark da wasu a kotu bisa zargin kwace jam’iyyar ta hanyar da ba ta dace ba.

Shugabannin da suka shigar da karar sun nemi kotu ta dakatar da wannan sabuwar tafiyar da ta zarga da shirin karbe mulkin jam’iyyar.

Kara karanta wannan

London Clinic: Abubuwan mamaki game da asibitin da Muhammadu Buhari ya rasu

Shugabannin da suka jagoranc hadaka a ADC a Abuja
Shugabannin da suka jagoranc hadaka a ADC a Abuja. Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Jaridar the Nation ta wallafa cewa tsohon dan takarar shugaban kasa a ADC ya yi zargin cewa ana raba kudi wa shugabannin jam'iyyar domin ajiye mukami.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan rikici na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da kokarin kafa kawancen ‘yan adawa gabanin zaben 2027, wanda ADC ta zama dandalin wannan yunkuri.

'Ana raba wa shugabannin ADC kudi'

Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC, Dumebi Kachikwu ne ya bayyana matakin kotu da aka dauka yayin wani taron manema labarai a Abuja.

Kachikwu ya ce an yi kokarin bai wa wasu shugabannin jam’iyyar na jihohi har Naira miliyan 20 domin su sauka daga mukamansu don ba wa sababbin ‘yan tafiyar damar karba.

“Ko sun amince, kundin tsarinmu bai amince da hakan ba,”

- Inji Kachikwu.

Ya ƙara da cewa ADC jam’iyya ce da aka kafa domin bai wa sababbijn jini da matasa damar jagoranci, ba wata mafakar dattijai ‘yan siyasa da suka gaza ba.

Kara karanta wannan

2027: A ƙarshe, Atiku Abubakar ya yi murabus daga jam'iyyar PDP mai adawa

Ana zargin APC da hannu a rikicin ADC

A wata sanarwa da sashen yada labarai na jam’iyyar ya fitar a makon da ya wuce, ADC ta zargi APC da daukar nauyin shari’ar da sunan wasu da ba mambobin jam’iyyar ba.

Punch ta wallafa cewa sanarwar ta ce ana ƙoƙarin hana shugabancin rikon kwarya na ADC ci gaba da aiki ta hanyar daukar wasu zuwa kotu da sunan mambobi.

Wasu mutum uku masu ikirarin zama mambobin ADC sun maka Sanata David Mark da wasu a kotu suna neman a soke shugabancin rikon kwarya na jam’iyyar.

Shugaban ADC yayin taron hadaka a Abuja
Shugaban ADC, David Mark yayin taron hadaka a Abuja. Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Masu karar su ne Adeyemi Emmanuel, Ayodeji Victor Tolu, da Haruna Ismaila, wadanda suka ce mika shugabancin jam’iyyar ga ‘yan kawancen siyasa na iya sabawa doka.

Jam’iyyar ta ce tana da lauya 97 da za su kare ta a kotu, kuma za ta ci gaba da kare dokarta da tsarin mulkinta.

Tsohon shugaban APC ya shiga ADC

A wani rahoton, kun ji cewa, tsohon shugaban jam'iyyar APC na kasa, John Oyegun ya sauya sheka zuwa ADC.

Kara karanta wannan

An zargi Kwankwaso da jawo rashin shigar NNPP zaben Legas

Bincike ya nuna cewa John Oyegun ne ya fara zama shugaban APC da aka zaba a lokacin da aka kafa jam'iyyar.

Oyegun ya ce shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gaza samar da cikakken tsaro kamar yadda ya yi alkawura a lokacin yakin neman zabe.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng