Gaskiya Ta Fito: Tsohon Gwamnan PDP Ya Fadi Dalilin Yin Aiki don Kayar da Atiku a 2023
- Tsohon gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya yi magana kan dalilinsa na yi wa PDP munaƙisa a zaɓen 2023
- Samuel Ortom ya bayyana cewa ya ƙi goyon bayan PDP ne a zaɓen 2023 saboda ƙin ba ɗan Kudu takarar shugaban ƙasa
- Ya nuna cewa ya yi farin ciki sosai da ɗan Kudancin Najeriya ya zama shugaban ƙasa a zaɓen 2023
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Benue - Tsohon gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya bayyana dalilin da ya sa ya yi wa PDP zagon ƙasa a zaɓen 2023.
Samuel Ortom ya ce dalilin da ya sa ya yi aiki da ƙarfinsa wajen kifar da PDP a zaɓen 2023 shi ne saboda gazawar jam’iyyar wajen kiyaye adalci, daidaito da gaskiya.

Source: Facebook
Tsohon gwamnan na Benue ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi da tashar Arise tv a ranar Alhamis, 17 ga watan Yulin 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin Ortom na ƙin goyon bayan Atiku
Samuel Ortom ya bayyana cewa ko da yake har yanzu yana cikin jam’iyyar PDP, ya ƙi goyon bayan ɗan takararta na shugaban ƙasa a 2023, Atiku Abubakar, saboda abin da ya kira cin amana da ƙin mutunta ra’ayoyin juna.
“Na bijire wa PDP a zaɓen da ya gabata ne saboda na yi imani jam’iyyar za ta tsaya tsayin daka wajen kare gaskiya, adalci da daidaito, amma abin takaici, ba su kiyaye waɗannan ƙa’idoji ba."
- Samuel Ortom
Ya tuna yadda aka naɗa shi a cikin wani kwamitin mutum 20 da aka ba aikin bada shawarar ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa da zai yi takara tare da Atiku.
PDP da Atiku sun ƙi ɗaukar shawara
A cewarsa, mutum 16 cikin 20 (ciki har da shi kansa) sun zaɓi tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, amma aka yi watsi da shawarar.
“Kamar yadda aka saba, ɗan takarar da shugabannin jam’iyya suka yanke shawarar watsi da shi (Wike)."
- Samuel Ortom
Tsohon gwamnan wanda ke cikin ƙungiyar G5, wata ƙungiya ta gwamnonin PDP guda biyar da suka nuna adawa da takarar Atiku, ya ce ƙudurinsu ya fi karkata kan kai mulki zuwa yankin Kudu a lokacin.

Source: UGC
"Ko da yake manufar G5 ta ƙunshi wasu muradun siyasa, amma babban burinmu shi ne samun ɗan takara daga Kudu. Kuma ina farin ciki da cewa a ƙarshe ɗan Kudun ne ya zama shugaban ƙasa."
- Samuel Ortom
Wannan furuci na Ortom ya zo ne a daidai lokacin da ake sake bayyana buƙatar gyara a PDP da kuma tattaunawa kan makomar shugabancinta, bayan kayen da jam’iyyar ta sha a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.
Hadimin Atiku ya soki ministan Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa hadimin tsohon mataimakin shugaban ƙasan Najeriya, Atiku Abubakar, ya caccaki ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo.
Paul Ibe ya buƙaci ministan da ya mayar da hankali kan aikin da ke gabansa a ma'aikatarsa, maimakon yin magana kan ƙananan batutuwa.
Kalamansa na zuwa ne bayan Keyamo ya soki Atiku Abubakar saboda sauya sheƙar da ya yi daga jam'iyyar PDP.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

