Ficewa daga PDP: Hadimin Atiku Ya Yi Wa Ministan Tinubu Wankin Babban Bargo

Ficewa daga PDP: Hadimin Atiku Ya Yi Wa Ministan Tinubu Wankin Babban Bargo

  • Hadimin Atiku Abubakar ya kasa haƙura ka sukar da Festus Keyamo ya yi wa tsohon mataimakin shugaban ƙasan na Najeriya
  • Paul Ibe ya soki ministan na sufurin jiragen sama a gwamnatin Shugaba Bola Tinubu kan tsoma baki a ƙananan batutuwa
  • Ya buƙace shi da ya mayar da hankali kan sauke nauyin da aka ɗora masa na kula da ma'aikatarsa a maimakon batun siyasa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Paul Ibe, mai magana da yawun tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya caccaki ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo.

Paul Ibe ya bayyana sukar da Festus Keyamo, ya yi wa Atiku a matsayin mara tushe wacce kuma take cike da son zuciya.

Hadimin Atiku ya soki Fetstus Keyamo
Hadimin Atiku ya yi wa Festus Keyamo martani Hoto: @fkeyamo, @atiku
Source: Twitter

Mai magana da yawun bakin na Atiku ya bayyana hakan ne yayin wata tattauna da tashar Channels tv a shirinsu na 'Morning Brief' a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

"An karya doka," Abin da Atiku ya yi ana jimamin rasuwar Buhari ya harzuƙa Ministan Tinubu

Atiku Abubakar ya fice daga PDP

A ranar Laraba, labari ya bazu cewa Atiku Abubakar ya fice daga jam'iyyar PDP.

Ana hasashen Atiku wanda bai faɗi inda zai koma ba, zai shiga jam'iyyar ADC wacce ke neman kifar da Shugaba Bola Tinubu da APC a zaɓen 2027.

Bayan ficewar Atiku daga PDP, Festus Keyamo ya caccaki mataimakin shugaban ƙasan na Najeriya.

Hadimin Atiku ya soki Festus Keyamo

Sai dai, a yayin hirar, Paul Ibe ya soki kalaman da Festus Keyamo ya yi kan Atiku Abubakar.

"Ina Festus Keyamo ya ke lokacin da Atiku Abubakar ke gaba da gaba wajen yaƙar mulkin soja tare da taimakon ƴan kishin ƙasa suka taimaka suka kore su daga mulki? Ina ya ke a wancan lokacin? Yanzu kawai yana son surutu ne."

- Paul Ibe

Paul Ibe ya soki zargin da Keyamo ya yi cewa Atiku na yin amfani da tambarin gwamnatin tarayya ba bisa ƙa’ida ba a takardunsa, yana cewa hakan ba ya nuni da yin sojan gona kan wani matsayi.

Kara karanta wannan

Ficewar Atiku Abubakar daga PDP ta girgiza siyasar Najeriya, gwamnoni sun fara magana

“Ba wanda ke yi wa wani sojan gona. Atiku Abubakar tsohon mataimakin shugaban ƙasa ne wanda kowa ya sani. Ban ga dalilin da zai sa na daraja Keyamo ba. Idan yana da ƙara, ya je kotu.

Kan zargin cewa Atiku ya tsufa, Ibe ya mayar da martani da cewa:

“Atiku Abubakar ya tsufa? Wanene ya ce haka? Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, yana da shekaru 79, kuma tsarin dimokuraɗiyyar da muke koyi da shi daga Amurka ya fito."
"To me muke magana akai? Shin Atiku Abubakar ba shi da lafiya ne? Shin ba shi da ƙarfi? Shin yana da wata larura?"

Game da tambayar ko ADC za ta zama jam’iyyar ƙarshe da Atiku zai tsaya takara a kai, Paul Ibe ya ce:

"Atiku Abubakar ne zai yanke wannan shawara. Amma ina ganin wannan haɗakar tana da kyakkyawar dama ta dawo da martabar Najeriya da sake gina ƙasa."
Hadimin Atiku ya yi wa ministan Tinubu martani
Hadimin Atiku ya kare ubangidansa Hoto: @atiku
Source: Facebook

An ja kunnen ministan Tinubu

Paul Ibe ya ja kunnen Keyamo da kada ya shagaltu da ƙananan batutuwa yayin da ake da manyan matsaloli da suka shafi ma’aikatarsa ta sufurin jiragen sama.

"Abin takaici ne yadda minista Keyamo ke bata lokaci yana magana kan ƙananan batutuwa, kuma hakan na nuna yadda yake tafiyar da ma’aikatar sufurin jiragen sama."

Kara karanta wannan

2027: A ƙarshe, Atiku Abubakar ya yi murabus daga jam'iyyar PDP mai adawa

"Ina ganin yana da ɗumbin ayyuka a gabansa, kamar gyaran ababen more rayuwa a filayen jiragen sama, titunan tashi da saukar jirage, gidajen wanka da ke cikin mummunan hali, amma duk da haka yana da lokacin da zai yi magana kan ficewar wani daga PDP."

- Paul Ibe

Lokutan da Atiku ya sauya sheƙa

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasan Najeriya, Atiku Abubakar ya yi murabus daga jam'iyyar PDP.

Ficewarsa daga PDP ta ƙara yawan lokutan da ya taɓa sauya sheƙa daga wannan jam'iyyar zuwa waccan kamar yadda aka tattaro.

A tarihin siyasar Atiku Abubakar, ya taɓa sauya sheƙa sauya har sau biyar daga jam'iyyun siyasa daban-daban daga fara shiga siyasa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng