Sauya Sheƙar Atiku Ta Rikita PDP da APC, Tsofaffin Gwamnoni da Jiga Jigai Sun Bi Sahunsa

Sauya Sheƙar Atiku Ta Rikita PDP da APC, Tsofaffin Gwamnoni da Jiga Jigai Sun Bi Sahunsa

  • Ga dukkan alamu ficewar tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar daga PDP ta taɓa manyan jam'iyyun siyasa a ƙasar nan
  • Manyan jiga-jigai daga PDP da APC a jihar Adamawa, mahaifar jagoran adawar sun fara tururuwar barin jam'iyyunsu zuwa haɗakar ADC
  • An ruwaito cewa tsofaffin ƴan takara a APC, tsofaffin gwamnoni da mataimakansu a PDP sun sauya sheƙa zuwa ADC

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Adamawa - Ficewar da tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi daga PDP ta rikirkita manyan jam'iyyun siyasar ƙasar nan musamman a Adamawa.

Rahotanni sun nuna cewa yanzu haka, jam’iyyar haɗaka ta ADC ce ke samun karɓuwa a jihar Adamawa yayin da manyan jiga-jigai daga APC da PDP ke sauya sheƙa zuwa cikinta.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar.
Guguwar sauya sheƙa ta turnuƙe jihar Adamawa bayan ficewar Atiku daga PDP Hoto: @Atiku
Source: Facebook

APC da PDP sun fara rasa manyan jiga-jigai

Kara karanta wannan

Alamu sun fara tabbata, gwamna ya gama shirin sauya sheka daga PDP zuwa APC

Tribune Nigeria ta ce cikin manyan ’yan siyasar da suka bar APC zuwa ADC har da wanda ya nemi takatarar gwamna a APC a zaɓen 2023, Sanata Elisha Abbo, da tsohon kodinetan matasa na kamfen ɗin Tinubu a Adamawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan nan wasu masu ruwa da tsakin APC a faɗin ƙananan hukumomi 21 na jihar Adamawa, sun tattara kayansu suk koma ADC.

A ɓangaren PDP kuwa, wasu tsofaffin gwamnoni da mataimakan gwamnoni, ’yan majalisun tarayya da na jihohi, da manyan jiga-jigai na PDP a jihar da ƙananan hukumomi sun yanke shawarar bin Atiku zuwa ADC.

Fastocin takarar tsohon gwamna sun fara yawo

Tuni fastocin tsohon gwamna, Umar Jibrilla Bindow suka fara yawo a faɗin jihar Adamawa, yana neman takara a ƙarƙashin ADC, yayin da kusan kashi 90% na tsofaffin kwamishinoninsa suka fara shirin baro jam’iyyunsu.

Atiku Abubakar ya bayyana murabus ɗinsa daga jam’iyyar PDP a wata wasika mai kwanan watan 14 ga Yuli, 2025, da ya aika wa shugaban PDP na gundumar Jada 1 da ke ƙaramar hukumar Jada, Jihar Adamawa.

Ya bayyana cewa babban dalilin ficewarsa shi ne sabani da sabon salo da tafiyar jam’iyyar ta dauka wanda ya ce ya sauka daga tubalan da aka kafa jam’iyyar a kai.

Kara karanta wannan

An fara watsewa Tinubu bayan cikawar Buhari, tsohon shugaban APC ya shiga ADC

Atiku ya tabbatar da ficewa daga PDP

Atiku ya gode wa PDP bisa damar da ta ba shi, ciki har da zama Mataimakin Shugaban Ƙasa na tsawon wa’adin mulki biyu da takarar Shugaban Ƙasa har sau biyu.

“Na ga dacewar na rabu da PDP sakamakon tafiyar da take yi a yanzu, wanda na ke ganin ya sha bamban da akidun da muka yi imani da su tun farko,” inji Atiku.
Atiku ya sake raba gari da PDP.
Yan siyasa a Adamawa sun fata bin Atiku Abubakar zuwa ADC Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

A halin yanzu, ana ci gaba da bayyana ra'ayoyi kan murabus ɗin Atiku, duk da cewa ba abin mamaki ba ne domin an yi tsammanin haka, Vanguard ta rahoto.

Shugaban PDP na jihar Adamawa, Barista Aliyu Shehu, ya ce:

"Ficewarsa babban lamari ne ga jam’iyyar, amma ina masa fatan alheri. Duk da haka, na tabbatar muku da cewa PDP a Adamawa tana nan daram!”

Wani dan PDP da ya bi Atiku zuwa ADC, Musa Abubukar ya bayyana kwarin guiwarsa cewa lokaci ya yi da wazirin Adamawa zai karbi mulkin kasar nan.

Kara karanta wannan

ADC: An fara ƙoƙarin canza wa Atiku tunani, haɗaka na fuskantar gagarumar matsala

Da yake tattaunawa da wakilin Legit Hausa kan lamarin, ya ce ba ya tunanin akwai wanda zai iya dakatar da wannan guguwar kawancen a Najeriya.

"Duk wasu alamun faduwar APC sun tabbata, ba a maganar PDP yanzu duk inda ka shiga lungu da sako maganar hadaka ake yi, don haka mu dai muna tare da Atiku.
"Ina fatan ADC ta tsayar da Waziri takara domin shi kadai ne zai iya murkushe wannam tawagar ta APC," In ji shi.

a Makinde ya yi magana kan fitar Atiku daga PDP

A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya ce tafiyar Atiku Abubakar ba zs ta ragi jam'iyyar PDP da komai ba.

Ya ce kowane ɗan siyasa yana da ƴancin shiga ko fita daga jam'iyyar PDP ba tare an hana shi amma duk wanda zai zama matsala gara ya tafi.

Makinde ya ce babu abin damuwa dangane da jam’iyyar haɗaka watau ADC, yana mai cewa ba wata barazana ba ce ga PDP.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262