Guguwar Atiku Ta Janye Tsohon Dan Takarar Shugaban Kasa zuwa ADC
- Rahotanni na nuni da cewa Dele Momodu ya fice daga PDP yana zargin wasu da kwace jam’iyyar daga hannun masu kishin kasa
- Yayin da ya koma jam'iyyar ADC, Dele Momodu ya ce babu abin da ya rage a PDP sai ragowar ƙasusuwan gawarta
- Sauya sheƙar Momodu na kara ƙarfafa sabuwar haɗin gwiwar 'yan adawa gabanin zaɓen 2027 domin tunkarar Bola Tinubu
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Edo – Fitaccen ɗan jarida kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Dele Momodu, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP.
Bayan fita daga PDP, Dele Momodu ya bayyana shiga sabuwar gamayyar hadakar 'yan adawa ta jam’iyyar ADC.

Source: Facebook
Legit ta gano bayanin da Momodu ya yi ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Momodu ya fitar da wasiƙar ficewa daga jam’iyyar PDP ranar Laraba, 17 ga Yuli, 2025, inda ya aika da ita ga shugaban jam’iyyar PDP na mazabar Ihievbe, ƙaramar hukumar Owan, jihar Edo.
Momodu ya soki yadda PDP ta lalace
A cewarsa, wannan mataki ya biyo bayan yadda wasu da ya kira da ‘masu adawa da dimokuraɗiyya’ suka kwace ragamar jam’iyyar PDP a fili, daga ciki da wajen jam’iyyar.
A cikin wasiƙar, Momodu ya bayyana cewa:
“Dalilina ba mai rikitarwa ba ne. Ba shakka, an kwace jam'iyyar mu daga hannun 'yan dimokuraɗiyya rana tsaka.”
Momodu ya ce saboda haka ya dace mutum mai daraja ya bar wannan jam’iyya da ta lalace, domin bin sahun sabuwar jam’iyyar hadaka ta haɗin gwiwa – wato ADC.
Ya bayyana PDP a matsayin “gawa” da babu abin da ya rage a cikinta sai ragowar ƙasusuwa, yana mai cewa ya fi dacewa masu kishin ƙasa su sauya sheƙa domin ceto Najeriya.

Kara karanta wannan
Ficewar Atiku Abubakar daga PDP ta girgiza siyasar Najeriya, gwamnoni sun fara magana
Momodu ya gode wa shugabannin PDP
Dele Momodu ya bayyana godiyarsa ga shugabannin PDP na mazaba da suka mara masa baya tun lokacin da ya shiga jam’iyyar a shekararun baya, yana mai cewa ya yarda da dimokuraɗiyya
Vanguard ta wallafa cewa ya ce ya gudanar da ayyuka da dama cikin jam’iyyar, ciki har da tsayawa takarar shugaban ƙasa, kuma ya yi fatan za su fahimci matakinsa.
Fitowar sa daga PDP ya kara zafafa rikicin cikin gida da ke ruguza jam’iyyar, musamman ganin yadda fitattun mutane ke cigaba da sauya sheƙa.

Source: Twitter
Sauya sheƙarsa ta motsa siyasar Edo
Ana ganin sauya sheƙar Momodu zuwa jam’iyyar ADC zai yi tasiri a siyasar jihar Edo da Najeriya gaba ɗaya, ganin yadda yake ɗaya daga cikin fitattun ‘yan siyasa da ke da tasiri a faɗin ƙasa.
Yanzu haka sauye-sauyen siyasa da haɗin gwiwar da ke ƙarfafa a jam’iyyar ADC na ƙara ƙarfafa hasashen canjin tsarin siyasa gabanin zaɓen 2027.
Tsohon shugaban APC ya koma ADC
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon shugban APC na kasa, John Oyegun ya raba hanya da shugaba Bola Tinubu.
John Oyegun ya sanar da fita daga jam'iyyar APC tare da koma wa tafiyar hadakar 'yan adawa a karkashin ADC.
Oyegun ya zargi APC da gazawa wajen magance matsalar tsaro musamman a wasu jihohin Arewacin Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

