An Fara Watsewa Tinubu bayan Cikawar Buhari, Tsohon Shugaban APC Ya Shiga ADC

An Fara Watsewa Tinubu bayan Cikawar Buhari, Tsohon Shugaban APC Ya Shiga ADC

  • John Odigie Oyegun ya karɓi katin zama ɗan ADC a Benin, yana zargin APC da haifar da yunwa da rashin tsaro
  • Ya ce sun gudanar da nazari tare da jam’iyyu bakwai kafin zaɓar ADC a matsayin dandalin haɗin gwiwa
  • Tsohon shugaban APC ya ce jam’iyyar ADC ta fi kowacce girma a yanzu saboda haɗin gwiwar da aka cimma

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Edo – Tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, John Oyegun, ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar adawa ta ADC.

John Oyegun ya sauya sheka ne yana mai zargin gwamnatin APC da gazawa wajen ceto ‘yan Najeriya daga halin ƙaƙanikayi.

Oyegun ya sauya sheka daga APC zuwa ADC
Oyegun ya sauya sheka daga APC zuwa ADC. All Progressive Congress
Source: Facebook

The Cable ta rahoto cewa Oyegun ya karɓi katin zama ɗan jam’iyyar ADC ne a wani gagarumin taro da aka gudanar a garin Benin, babban birnin jihar Edo.

Kara karanta wannan

Guguwar Atiku ta janye tsohon dan takarar shugaban kasa zuwa ADC

Wannan mataki na Oyegun na zama tamkar sabon salo ne na sauye-sauyen da ke faruwa a harkar siyasar Najeriya, musamman gabanin zaɓen 2027.

Shugaban ADC yaba wa John Oyegun

Shugaban jam’iyyar ADC na jihar Edo, Kennedy Odion, ya nuna jin daɗinsa da maraba da tsohon shugaban APC, yana mai cewa Oyegun ya taka rawa wajen haɗa jam’iyyu a baya.

Kennedy Odion ya ce:

“A da can, ya haɗa jam’iyyu a matsayin tafiya ɗaya, kuma ya yi nasara. Idan ka fahimci ƙa’idar lissafi, to za ka gane mai zai faru a gaba,”

Ya ƙara da cewa yanzu Oyegun na aiki tare da ADC domin gina sabon haɗin gwiwa da zai ƙara ƙarfafa jam’iyyar a matakin ƙasa.

Oyegun ya bayyana dalilan zabar ADC

Tsohon shugaban na APC ya bayyana cewa kwamitin da ya jagoranta ne ya zaɓi ADC a matsayin jam’iyyar da za a kafa haɗin gwiwa bayan dogon nazari da shawarwari da jam’iyyu daban-daban.

Kara karanta wannan

2027: Shugaban ADC ya fallasa shirin dakile farin jinin jam'iyyar

“Akalla mun yi magana da jam’iyyu bakwai. Har zuwa karshe, muka dawo nan. ‘Eh, mun yi abin da kuka sa mu yi… amma ba mu ga wata jam’iyya da ta himmatu kamar ADC ba,”

- Inji Oyegun.

Ya ce wannan haɗin gwiwar da ake ƙarfafawa a jam’iyyar ADC ita ce mafita ga ‘yan Najeriya, domin jam’iyyar ta kunshi masu nagarta daga APC da PDP.

John Oyegun ya zargi APC da gazawa

Oyegun ya nuna ɓacin ransa kan yadda ake fama da yunwa da rashin tsaro a ƙasar nan, musamman a jihohin da suka haɗa da Benue.

Bayan korafi kan rashin tsaro, Oyegun ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da rarraba ƙasa maimakon haɗe ta.

Oyegun tare da marigayi shugaba Muhammadu Buhari
Oyegun tare da marigayi shugaba Muhammadu Buhari. Hoto: All Progressive Congress
Source: UGC

Punch ta wallafa cewa Oyegun ya ce:

“A watanni da suka wuce, ADC karamar jam'iyya ce. Amma yau, za mu iya cewa ita ce mafi girma a Najeriya,”

Buhari: Ana fargabar samun sabani a APC

A wani rahoton, kun ji cewa kakakin jam'iyyar ADC, Bolaji Abdullahi ya ce burin marigayi shugaba Muhammadu Buhari ne mutanen shi su shiga hadaka.

Bolaji Abdullahi ya bayyana haka ne yana fatan ganin sauran 'yan tsagin tsohuwar CPC sun shiga ADC kafin 2027.

Hakan na zuwa ne bayan samun wasu mutanen Buhari sun koma tafiyar hadakar 'yan adawa domin hamayya da Bola Tinubu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng