"An Karya Doka," Abin da Atiku Ya Yi Ana Jimamin Rasuwar Buhari ya Harzuƙa Ministan Tinubu
- Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo (SAN) ya nuna takaicinsa kan yadda Atiku Abubakar ya saki takardar barin PDP ana tsakiyar jimami
- Keyamo ya bayyana cewa hakan ya ƙara tabbatar da cewa ƙwaɗayin mulkin Atiku Abubakar ya zarce tausayi da jin ƙansa
- Ministan ya kuma caccaki Atiku bisa amfani da tambarin gwamnatin tarayya a wasiƙar sauya shekarsa, ya ce hakan ya saɓa doka
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo, ya bayyana rashin jin daɗinsa kan fitar Atiku Abubakar daga PDP ana cikin jimamin rasuwar Muhammadu Buhari.
Keyamo ya ce bai kamata tsohon mataimakin shugaban ƙasa, ya fitar da wasikar ficewarsa daga PDP a daidai lokacin da ake alhinin rasuwar tsohon shugaban ƙasa, Buhari ba.

Source: Facebook
Hakan na kunshe ne a cikin wani saƙo da ministan ya wallafa a shafinsa na X da aka fi sani da Twitter yau Laraba, 16 ga watan Yuli, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Keyamo ya fusata da abin da Atiku ya yi
Keyamo ya ce ko da yake Atiku na da ƴancin sauya jam’iyya a kowane lokaci, amma fitar da wasikar a wannan mako na makokin Buhari ya nuna yana yunƙurin karkatar da hankulan jama’a zuwa ga kansa.
Ministan ya ce:
“A zahirin gaskiya, cikin mutuntawa, wannan abin da ka yi ya nuna cewa burinka na takarar shugabancin ƙasa ya rinjayi tausayi da jin ƙai.”
Keyamo ya ƙara da bayyana cewa duba da wasiƙar, Atiku ya shirya, ya buga, ya sa hannu, kuma ya miƙa wasikar fita daga PDP a washe garin ranar da aka sanar da rasuwar Buhari.
Ministan Tinubu ya gano kuskuren Atiku
Bugu da ƙari, Keyamo ya kalubalanci Atiku kan amfani da Tambarin Gwamnatin Tarayya, a cikin wasiƙarsa, yana mai cewa hakan ya sabawa doka.
“A bisa doka, ya sabawa sashe na 6 na dokar ‘Flag and Coat of Arms Act, Cap. F30, na dokokin Najeriya, 2004’ wanda ya haramta wa wanda ba ya rike da kujera a gwamnatin tarayya amfani da tambarin kasar," inji shi.
Keyamo ya ce amfani da tambarin yana iya rikita al’umma da yaudararsu su yi tunanin cewa Atiku na magana ne a madadin gwamnatin tarayya, alhali bai riƙe wani muƙami a gwamnati ba tun shekaru 18 da suka wuce.

Source: Twitter
An zargi Atiku da neman haifar da ruɗani
“Ka yi tunanin idan duk wasu tsofaffin jami’an gwamnati za su ci gaba da amfani da tambarin Najeriya a sako kansu na siyasa, ba makawa za a samu babban rikici da rudani.”
- Festus Keyamo, SAN.
Keyamo ya ce duba da matsayinsa a gwamnatin tarayya da kuma kasancewarsa lauya na ƙasa, nauyi ne a kansa ya kare kundin tsarin mulki da dokokin ƙasa.
Makinde ya yi martani kan sauya shekar Atiku
A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya bayyana cewa tafiyar Atiku ba za ta yi wa PDP illa a siyasance ba.
Gwamna Makinde ya ce ficewar Atiku ba za ta rage karfin jam’iyyar PDP ko damar ta ba, yana mai cewa duk wanda zai kawo matsala gara ya tafi.
Ya ce babu abin damuwa dangane da jam’iyyar haɗaka watau ADC, a cewarsa ba wata barazana ba ce ga PDP.
Asali: Legit.ng

