Ana Jimamin Rasuwar Buhari, An Hango Babban Kuskuren da Shugaba Tinubu Ya Yi

Ana Jimamin Rasuwar Buhari, An Hango Babban Kuskuren da Shugaba Tinubu Ya Yi

  • Sanata mai wakiltar Abuja a Majalisar Dattawa, Ireti Kingibe ta bayyana cewa Shugaba Tinubu ya tafka kuskure da ya naɗa Wike a matsayin minista
  • Sanata Kingibe ta bayyana Nyesom Wike a matsayin ɗan kama karya, wanda ke tafiyar da harkokin Abuja ba tare da bin doka ba
  • Wannan kalamai na Kingibe na zuwa ne a lokacin da Najeriya ke jimamin rasuwar tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Sanata Ireti Kingibe mai wakiltar Abuja ta ce babban kuskuren siyasa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi shi ne na naɗa Nyesom Wike a matsayin minista.

Kingibe ta bayyana damuwarta kan yadda Wike ke ƙwace filayen da gwamnatin tarayya ta bai wa makarantu da muhimman wurare a Abuja.

Sanata mai wakiltar Abuja a Majalisar Dattawa, Ireti Kingibe.
Sanatar Abuja ta ce Nada Wike a matsayin minista ne babban kuskuren Tinubu Hoto: @IretiKingibe
Source: Twitter

Sanatar Abuja ta soki Nyesom Wike

Kara karanta wannan

Ana ci gaba da bayyana ayyukan alheran Buhari, Malami faɗI abin da ya sani

A wata hira da aka yi da ita a Arise TV a ranar Litinin, Kingibe ta bayyana cewa salon shugabancin Wike ya yi kama da kama-karya, yana nuna raini ga tsarin mulki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Babban abin damuwa shi ne ministan baya bin dokokin kasa, ɗan kama-karya ne, wanda ba ya bin ka’idoji da dokoki, kuma idan aka ba shi shawarar ya bi doka, ba ya ɗauka."
“Nyesom Wike ya dawo da wasu hukumomi ba tare da izini ba. Idan yana so a dawo da su, sai ya nemi amincewar majalisar dokoki ta ƙasa. Amma bai yi haka ba, saboda yana ganin shi ke da iko. Yana jin zai iya yin komai’.”

- Sanata Ireti Kingibe.

Kingibe ta bayyana laifuffukan da Wike ya yi

Ta kuma zargi Wike da ƙwace filayen da suka kai hektoci 7,000 daga cikin 11,000 da aka ware wa Jami’ar Abuja, lamarin da ya saba da Dokar Amfani da Ƙasa.

Sanatar ta ƙara da cewa

“Jami’ar Abuja tana da kusan hektoci 11,000 na fili. Wike ya soke hektoci 7,000 ya bar musu 4,000 kawai. Wannan ya sabawa Dokar Amfani da Ƙasa, domin ba a yarda a kwace ƙasa daga cibiyar ilimi a ba wa masu zaman kansu ba.”

Kara karanta wannan

Babbar jami'ar majalisar dinkin duniya ta yi wa Buhari shaida mai kyau

Kingibe ta ce matakan da Wike ke dauka sun haifar da asarar ayyukan yi da kuma rashin jin daɗi a tsakanin mazauna Abuja, kamar yadda The Cable ya kawo.

“Duk wani minista da ya zo yana iske matalautan mata ne ke share titi. Ko da wasu sun so kawo injinan share titi, ana ce musu a'a, domin hakan zai daƙile hanyar samun abincin mata marasa galihu.
“To amma shi Wike, ya kori duka kuma bai kawo injinan share titi ba. Saboda haka Abuja ta fara zama da datti," inji ta.
Sanata Kingibe da Ministan Abuja, Nyesom Wike.
Sanata Kingibe ta kira Ministan Abuja, Wike da dan kama karya Hoto: @IretiKingibe, @GovWike
Source: Twitter

Wane kuskure Shugaba Tinubu ya yi?

Sanata Kingibe ta ce naɗa Wike a matsayin minista ya janyo wa gwamnatin Shugaba Tinubu illa sosai.

A cewar Sanata Kingibe:

“Wannan ra'ayina ne domin idan zan lissafa abubuwan da Shugaba Tinubu ya yi kuskure a kai, mafi muni a cikinsu shi ne naɗa Wike, wannan ne ya fi cutar da shi a siyasa.”

Wike ya taso mabarata da tsagerun Abuja

A wani rahoton, kun ji cewa Wike ya bayar da umarnin korar mabarata, masu sana’o’i a kan titi, da 'tsageru' daga cikin Abuja da garuruwan da ke kewaye da ita.

Kara karanta wannan

'Mun yi babban rashi,' Ganduje ya mika ta'aziyya ga 'yan Najeriya kan rasuwar Buhari

Ministan ya kaddamar da shirin kwashe mabarata, masu yawon banza, da sauran masu gararamba a kan titunan Abuja.

Tuni aka samar da hadin gwiwar jami’an tsaro da hukumomin Abuja domin ganin cewa an aiwatar da umarnin kamar yadda Wike ya bayar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262