APC Ta Lallasa PDP, LP, Ta Lashe Zaben Kananan Hukumomi 20 da Kansiloli 375 a Legas

APC Ta Lallasa PDP, LP, Ta Lashe Zaben Kananan Hukumomi 20 da Kansiloli 375 a Legas

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas – Jam'iyyar APC ta lashe dukkan kujerun shugabannin ƙananan hukumomi 20 a zaɓen kananan hukumomi na Jihar Legas.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Legas (LASIEC) a ranar Lahadi ta bayyana cewa APC ta kuma lashe kujerun kansiloli 375 cikin 376 a jihar.

Jihar Legas na da masu kada kuri'a miliyan 7

Jam'iyyar PDP ta lashe kujerar kansila guda ɗaya a Ward D, Yaba, kamar yadda rahoton Channels TV ya nuna.

Masu kaɗa kuri'a da suka yi rajista a jihar, a ranar Asabar, sun je rumfunan zaɓe don zaɓen ciyamomin ƙananan hukumomi 20 da kuma mazabu (LCDAs) 37.

Rahoton jaridar The Cable ya nuna cewa jihar Legas tana da sama da masu kaɗa kuri'a miliyan bakwai da suka yi rajista.

Kara karanta wannan

2027: Manyan 'yan siyasar Najeriya da suka bar PDP, APC, suka shiga kawancen ADC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayanan da aka samu daga hukumar LASIEC sun nuna cewa an tabbatar da jam'iyyun siyasa 15 daga cikin 19 da suka yi rajista a ƙasar za su fafata a zaɓen shugabanci da kansiloli.

Sunayen kananan hukumomi da mazabu

Kananan hukumomi 20 sune: Agege, Ajeromi-Ifelodun, Alimosho, Amuwo-Odofin, Apapa, Badagry, Epe, Eti-Osa, Ibeju-Lekki, Ifako-Ijaiye, Ikeja, Ikorodu, Kosofe, Lagos Island, Lagos Mainland, Mushin, Ojo, Oshodi-Isolo, Shomolu, da Surulere.

Mazabu (LCDAs) sune: Orile Agege, Ifelodun, Agbado-Oke Odo, Ayobo-Ipaja, Egbe-Idimu, Mosan-Okunola, Oriade, Apapa Iganmu, Olorunda, Badagry West, Eredo, Ikosi-Ejirin, Ikoyi-Obalende, Iru/Victoria Island, da Lekki.

Sauran LCDAs sune: Ojokoro, Onigbongbo, Ojodu, Igbogbo-Baiyeku, Ijede, Imota, Ikorodu North, Ikorodu West, Agboyi-Ketu, Ikosi-Isheri, Lagos Island East, Yaba, Odi-Olowo, Iba, Oto-Awori, Ejigbo, Isolo, Bariga, Coker-Aguda, da Itire-Ikate.

APC ta ci gaba da riƙe Legas

Yayin da aka fitar da wannan sakamakon, APC ta ci gaba da riƙe ikon siyasar Legas, cibiyar tattalin arzikin Najeriya, kuma babbar mai ba da gudummawa ga kudaden shiga.

Kara karanta wannan

2027: Ƴan siyasa 5 da ake hasashen za su nemi takarar shugaban ƙasa a ADC

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ɗan asalin Legas ne kuma ya kasance gwamnan jihar daga 1999 zuwa 2007.

A jajibirin zaɓen, shugaban LASIEC, Mai Shari'a Bola Okikiolu-Ighile, ya ce ba a hana wata jam'iyyar siyasa shiga zaɓen ba.

Duk da cewa babu rahotannin manyan tashin hankali a lokacin zaɓen, an samu rahotannin tsoratar da masu kaɗa kuri'a da kuma jinkirin isowar kayayyakin zaɓe a wasu yankuna.

Amma Okikiolu-Ighile ta bayyana cewa iƙirarin ƙarancin masu kaɗa kuri'a na iya samo asali ne daga masu zaɓen da suka bar wurin bayan sun kaɗa kuri'unsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com