'ADC Za Ta Iya Lashe Zaɓen 2027', Tsohon Ɗan Majalisa Ya Kawo Dabarun Doke Tinubu
- Dr. Farah Dagogo ya ce hadakar ADC na da karfin kayar da APC a 2027 idan aka tabbatar da hadin kai da dimokuraɗiyya cikin jam’iyyar
- Tsohon dan majalisar wakilan ya ce shigar Atiku Abubakar cikin hadaka ya nuna cewa ya shirya ceto Najeriya daga matsalolin tattali
- Ya ce gasa tsakanin Atiku, Obi da Amaechi ba zai kawo rikici a ADC ba idan aka yi sahihin zaben fitar da gwani kuma aka yi sulhu bayan zaben
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja – Tsohon dan majalisar wakilai, Dr. Farah Dagogo, ya bayyana cewa hadakar ‘yan adawa da ke karkashin ADC na da damar kayar da jam’iyya mai mulki ta APC a zaben 2027.
Dr. Dagogo, wanda kuma tsohon dan takarar gwamnan Rivers ne, ya ce ADC na iya kawo sauki ga ‘yan Najeriya a 2027 matukar aka kiyaye dimokuraɗiyya da haɗin kai a jam’iyyar.

Source: Twitter
Rawan da Atiku ke takawa a karfafa ADC
A wata hira ta musamman da ya yi da jaridar Vanguard, Dr. Dagogo ya bayyana rawar da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ke takawa wajen sake farfado da jam’iyyar ADC da kuma hade ‘yan siyasar da ke da ra’ayin ci gaban kasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dr. Dagogo ya ce:
“Kasancewar Atiku cikin wannan hadaka ta sake tsara ADC da hada ‘yan siyasa masu akida daya, shaida ce ta jajircewarsa wajen samar da mulki mai inganci da cigaban kowa.
Ya ƙara da cewa ba a tsayar da jam'iyyar ADC don lashe zaɓe kawai ba, illa dai domin farfado da haɗin kan kasa, daidaita tattalin arziki, da inganta tsarin mulki.
“Kwarewar Atiku da hangen nesa da dabarunsa su ne ginshikan wannan hadaka. Kalubale da yawa na fuskantar Najeriya, amma ba a rasa mafita ba.”
- Dr. Farah Dagogo.
Burin Atiku, Obi da Amaechi zai kawo rikici a ADC?

Kara karanta wannan
2027: Malamin addini ya faɗi tikitin mutum 2 kacal da zai iya kayar da Tinubu cikin sauƙi
Dangane da yiwuwar rikici a jam’iyyar ADC sakamakon burin takarar shugaban kasa daga Atiku Abubakar, Peter Obi, da Chibuike Amaechi, Dr. Dagogo ya ce:
“Sha’awar shugabanci daga irin su Peter Obi da Rt. Hon. Amaechi, da kuma Atiku Abubakar, na nuna karbuwa da karfi da wannan dandalin hadaka ke samu."
Ya ce gasa tsakanin masu neman takara abin alheri ne, matukar zaɓen fidda gwanin ya kasance a bayyane, cikin tsarin dimokuraɗiyya, bisa cancanta da dacewar matakin kasa.
“Ba za a sake kuskuren 2023 ba. Dole a gina tsarin sulhu bayan zabe domin hade kan masu neman takara gaba ɗaya don karfafa jam’iyya,” inji Dr. Dagogo.

Source: Facebook
'ADC na da damar kayar da APC' – inji Dagogo
Dr. Dagogo ya nanata cewa ADC na da cikakken iko da karfin kayar da jam’iyyar APC a 2027 kamar yadda APC ta kayar da PDP a 2015.
Ya ce hadin kan da ke gudana cikin ADC na da gagarumar dama matukar aka gina ta bisa gaskiya, ra’ayoyin kasa, da akidar siyasa mai ma’ana.
“Makullin nasara shi ne haɗin kai, cancanta, da sadaukarwa ga ƙa’idojin dimokuraɗiyya,” inji Dr. Dagogo.
Ya ƙara da cewa:
“Idan akwai darasi da za a koya daga 2015, shi ne cewa haɗin kai da hangen nesa kan kyakkyawan shugabanci na iya sauya tafarkin siyasar ƙasa.”
“Amma sabanin na 2015, inda sauyin mulki ya faru ne bisa siyasa ta lokaci, wannan hadaka tilas ta ginu ne kan manufa, akida ta jama’a, da gaskiya.”
Ya ƙare da cewa hadakar da ADC ke jagoranta na da cikakken damar zama wata gagarumar mafita da za ta sake fasalta yanayin siyasar Najeriya gaba ɗaya.
'Atiku dan takarar ADC ba Obi ba' - Fasto
Tun da fari, mun ruwaito cewa, Primate Elijah Ayodele ya ce Atiku Abubakar ne zai zama ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC a 2027, ba Peter Obi ba.
Babban malamin addinin Kiristan ya ce ya hango cewa Peter Obi zai bar hadakar ADC, amma hakan ba zai hana Atiku samun tikitin tsayawa takara ba.
Ya kuma gargadi APC cewa za ta iya faduwa zaɓe idan shugabanninta suka bijirewa maganganunsa, inda ya nuna damuwa kan makomar jam'iyyar.
Asali: Legit.ng

