'Za Mu Ci Zabe cikin Sauƙi': ADC Ta Fara Harin Gwamnan PDP da Ke Shirin Shiga APC
- Jam'iyyar ADC ta ce ficewar Gwamna Ademola Adeleke daga PDP zuwa APC na iya ba ta damar lashe zaɓen gwamnan Osun cikin sauki
- ADC ta ce 'yan PDP masu yawa sun riga sun shiga jam'iyyarta, wasu kuma na shirin shiga saboda rashin jin daɗin yunkurin Adeleke
- Jam'iyyar hadakar na ƙoƙarin jawo gwamnoni biyar daga PDP, duk da sukar da take fuskanta daga PDP da magoya goyon bayan APC
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Osun – Jam'iyyar hadaka ta ADC ta yi magana kan rahotannin da ke yawo cewa gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke na shirin ficewa daga PDP zuwa APC.
Shugaban ADC na jihar Osun, Charles Omidiji, ya bayyana cewa idan har rahoton ya tabbata, to hakan zai iya ba jam'iyyarsa damar lashe zaɓen gwamna na 2026 cikin sauki.

Source: Facebook
A wata tattaunawa ta musamman da ya yi da jaridar Sunday Punch, ya ce Charles Omidiji yawancin 'yan jam'iyyar PDP na jin haushin matakin Adeleke.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin ADC na son Adeleke ya koma APC
Charles Omidiji ya ce 'yan jam'iyyar PDP da ba su ji daɗin shirin Adeleke na komawa APC ba, sun nuna shirinsu na sauya sheka zuwa ADC.
Shugaban jam'iyyar na ADC ya ce:
“Za mu yi farin ciki sosai idan ya sauya sheka zuwa APC. Zai zama matsala a gare mu idan ya ci gaba da zama a PDP.
“Mutane da yawa daga PDP da APC sun riga sun shiga hadakar mu. Don haka, addu’armu ita ce ya shiga jam'iyyar APC.
"Wannan zai share mana hanya. Yana nufin za mu lashe zaɓen gwamna cikin sauki. Babu faɗa a cikin jam’iyyarmu. Muna tafiyar da al’amuranmu yadda ya kamata.”
ADC na neman jawo gwamnonin PDP 5
Wannan na zuwa ne yayin da ADC, wacce ita ce dandalin kawancen shugabannin ƴan adawa, ke shirin jawo gwamnoni biyar masu ci cikinta kafin babban zaɓen 2027.
Majiyoyi daga cikin jam'iyyar sun shaida cewa ADC za ta amfana daga rikicin da ke cikin jam'iyyar PDP ta hanyar sa wasu gwamnonin jam'iyyar su shiga kawancen.
Mun ruwaito cewa, wannan na zuwa ne dai-dai lokacin da shugabannin PDP biyar a jihohi biyar suka ajiye aikin su daga jam'iyyar don shiga ADC.

Source: Instagram
Jam'iyyar hadaka na fuskantar suka
Tun lokacin da aka bayyana ADC a matsayin dandalin kawancen, suka na ci gaba da mamaye ƙarfinta da kuma mutanen da ke bayanta.
Shugaban PDP na kasa, Umar Damagum, ya yi gargaɗi cewa za su hukunta mambobinsu da ke kawo rudani a jam'iyyar, yana nesanta shugabannin jam'iyyar da hadakar ADC.
Wani tsohon hadimin shugaban ƙasa kumamai goyon bayan Tinubu, Reno Omokri, ya bayyana ADC a matsayin taron tsintsiya ba shara na "ƴan siyasar da aka juyawa baya."
Tsohon ministan shari'a ya shiga ADC
A wani labarin, mun ruwaito cewa, tsohon minista Hon. Musa Elayo Abdullahi ya sauya sheka daga PDP zuwa jam’iyyar ADC a Nasarawa.
A cikin wasiƙar murabus dinsa, Musa Elayo ya bayyana ficewarsa a matsayin sakamakon nazari mai zurfi da la’akari da manufofinsa.
Sauya shekar da Elayo ya yi zuwa ADC na iya ƙarfafa jam’iyyar a Nasarawa tare da janyo sababbin ƙawayen siyasa gabanin zaɓen 2027.
Asali: Legit.ng


