Tsohon Gwamna a Arewa Ya Juya Mata Baya, Ya Faɗi Wanda Ya Kamata Ya Yi Takara

Tsohon Gwamna a Arewa Ya Juya Mata Baya, Ya Faɗi Wanda Ya Kamata Ya Yi Takara

  • Tsohon gwamnan Benue, Samuel Ortom, ya ce yana goyon bayan shugabancin kudu a 2027, yana mai cewa yankin ya kamata ya kammala wa'adinsa
  • Ortom ya yaba da manufofin Bola Tinubu, musamman cire tallafin mai da sauye-sauyen haraji, yana cewa hakan ya inganta kudaden shiga da bin doka
  • Ya soki mulkin Muhammadu Buhari, yana cewa ya durkusar da kasa, ya kuma ce yana PDP, bai yarda da kawancen jam'iyyun siyasa ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom ya yi magana kan zaben shekarar 2027 da ke tafe.

Ortom ya bayyana goyon bayansa ga ci gaba da shugabancin Najeriya daga yankin Kudu a shekarar 2027.

Tsohon gwamna ya fadi wanda zai goyi baya a 2027
Tsohon gwamna a Arewa ya goyi bayan dan Kudu a takarar 2027. Hoto: Samuel Ortom.
Source: Facebook

Tsohon gwamna ya goyi bayan takarar dan Kudu

Ortom ya bayyana hakan ne a wata ganawa da manema labarai da aka gudanar a Makurdi, babban birnin jihar, a ranar Alhamis, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Tsohon makusancin Obi ya fadi yadda ADC za ta mikawa Tinubu nasara a 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ortom ya ce dole ne a bai wa yankin damar kammala mulki na shekaru takwas kafin a mayar da mulki Arewa.

Ya ce:

“Har yau, ni Ortom, ina goyon bayan shugabancin kudu. Ko da jam’iyyata (PDP) ta fitar da dan takara, sai daga Kudu.
“Ina ganin Kudu ya kamata a bari su kammala shekaru takwas. Don haka, ni ba zan mara wa dan Arewa baya ba.”
An bukaci barin Kudu su karisa wa'adinsu kafin Arewa
Tsohon gwamna, Ortom ya goyi bayan takarar Kudu. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Ortom ya yabawa Shugaba Tinubu

Ortom wanda jigo ne a jam’iyyar PDP kuma mamba a kwamitin amintattu na jam’iyyar, ya kuma yabawa Shugaba Bola Tinubu, Punch ta ruwaito.

“Gwamnatin Tinubu tana kokari; yana tabbatar da mulkin doka, kuma hakan yana da amfani ga kasar mu.
“Masana'antar man fetur ta dade da zama inda wasu 'yan tsiraru ke wawure dukiyar kasa, amma cire tallafi ya kawo sauyi sosai.

Ya ce babu wata jiha da za ta ce ba ta da kudi don biyan albashi tun bayan cire tallafin mai.

Kara karanta wannan

Haɗaka: An faɗi ƴan siyasa 7 a ADC da ke neman takara domin karawa da Tinubu

Ortom ya kuma yaba da sauye-sauyen haraji da ake yi, yana cewa matakin da ya dace ne wajen bunkasa tattalin arzikin Najeriya.

Tsohon gwamna ya soki gwamnatin Buhari

Sai dai Ortom ya soki gwamnatin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari, yana cewa ta kai Najeriya daga sama zuwa kasa.

Ya ce ba ya cikin sabuwar kawancen da aka kafa, yana mai cewa har yanzu yana cikin jam’iyyar PDP.

Ya kara da cewa:

“Ni har yanzu mamba ne kuma jagora a jam’iyyar PDP; har a kwamitin amintattu nake.
“Ba na yarda da kawance, amma idan akwai bukatar hada kai ta dabara, za ku gan ni a ciki.”

An shawarci ADC ta tsayar da Jonathan

Mun ba ku labarin cewa wasu mazauna Jalingo da ke jihar Taraba sun bukaci ADC ta tsayar da Goodluck Jonathan takara a 2027.

Sun ce Jonathan na da karbuwa a Arewa da Kudu, kuma zai tsaya wa wa’adin mulki daya kacal wanda ya fi jan hankalin Arewa.

Masu magana sun jaddada cewa Jonathan zai kawo sauyin tattalin arziki, kuma su na bukatar ADC ta daina son kai ta mai da hankali kan nasara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.