'Ba Tinubu ba ne': Malami Ya Hango Wanda Zai Lashe Zaben Shugaban Kasa a 2027
- Wani malamin gargajiya da ya yi hasashen nasarar APC a 2023, yanzu ya yi hasashen cewa Shugaba Bola Tinubu zai sha kasa zaɓen 2027
- A wani bidiyo da ya yadu a shafukan sada zumunta, an ga malamin yana kulumboto, tare da cewa Atiku Abubakar ne zai lashe zaben mai zuwa
- Hasashen malamin dubar ya jawo cece-kuce, yayin da 'yan Najeriya suka zura ido suka ko hasashensa zai zama gaskiyar kamar na baya
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja – Wani malami mai bin al’adun gargajiya wanda ya yi hasashen nasarar APC a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, ya yi iƙirarin cewa Shugaba Bola Tinubu zai sha kasa a 2027.
Maimakon haka, malamin ya bayyana cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ne zai zama shugaban Najeriya na gaba.

Source: Twitter
Malami ya hango faduwar Tinubu a zaben 2027
A wani bidiyo da Obinna ya wallafa a shafinsa na TikTok, an ga malamin rike da wani zare ya na furta wasu kalmomi na al'adunsu na gargajiya, inda yake magana game da zaben 2027.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ce malamin, wanda Legit Hausa ba ta samu sunansa ba, ya shahara a yin hasashen da ke zama daidai, inda ya yi hasashen nasarar APC a 2023.
A wannan karon ma, an ga malamin yana magana da wasu da ake kyautata zaton cewa iskokai ne, yana kuma fadin abin da suka fada masa, a wani yanayi na rauhanayya.
Malamin ya ce Najeriya za ta fuskanci wani gagarumin sauyi a siyasar kasar nan, yana mai cewa:
“Na tambayi abun bautana, shin wa zai zama shugaban ƙasar Najeriya na gaba a zaɓen 2027?. Abun bauta ya nuna mun Tinubu ba zai ci zabe na gaba ba.

Kara karanta wannan
'Daga Allah ne': Malami ya gargaɗi Tinubu kan sanya rai a tazarce bayan hadakar ADC
"Abun bauta ya ce Tinubu ba zai ci zaɓe na gaba ba ko da mutane da yawa za su shiga APC. Abun bauta ya ce Atiku ne zai zama shugaban Najeriya na gaba.”
Kalli bidiyon a nan kasa:
Atiku na kara yin tasiri a tsakanin 'yan adawa
Hasashen malamin duban ya haifar da cece-kuce a kafofin sada zumunta, musamman daga masu lura da harkokin siyasa, magoya bayan jam'iyyu, da masu sukar jiga-jigan biyu.

Source: UGC
Yayin da wasu ke kallon iƙirarin malamin gargajiyar a matsayin al'amara, wasu kuma suna ɗaukarsa a matsayin wani muhimmin aikin rauhaniyya na sanin makomar siyasar kasar.
Duk da cewa ba a fara yakin neman zaɓen 2027 a hukumance, irin waɗannan hasashen suna ba da gudummawa wajen fadada tattaunarwar farko game da yanayin siyasar kasar.
Yayin da ake tunkarar 2027, mutane za su sa ido don ganin ko wannan hasashen zai kasance daidai kamar yadda malamin gargajiyar ya yi a baya.
'Abin da zai faru a zaben 2027' - Major Prophet
A wani labarin, mun ruwaito cewa, fitaccen fasto, Major Prophet, ya yi hasashen cewa za a fara sayen limamai da shugabannin addini daga 2025 don su mara wa ’yan siyasa baya.

Kara karanta wannan
"Ku yarda da ni": Obi ya fara lallaɓa ƴan Arewa, yana neman ƙuri'un doke Tinubu a 2027
Ya gargadi cewa majami’u za su zama wuraren yakin neman zaben 2027, inda fastoci da bishof za su goyi bayan ’yan takara saboda kudi da alfanun kashin kai.
Major Prophet ya ce duk dan siyasar da ya dogara da goyon bayan fastoci ba zai yi nasara ba; wannan dabi’a za ta taimaka wa ’yan adawa ne kawai.
Asali: Legit.ng
