'APC, PDP, ADC, Duk Ɗaya Ne': Shettima Ya Tura Saƙo ga Ƴan Adawa Ana Batun Haɗaka

'APC, PDP, ADC, Duk Ɗaya Ne': Shettima Ya Tura Saƙo ga Ƴan Adawa Ana Batun Haɗaka

  • Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya yi magana kan jam'iyyun adawa a wani taro a Abuja a yau Alhamis 10 ga watan Yulin 2025
  • Shettima ya ce duk ‘yan siyasa daya suke wajen gina kasa, komai bambancin jam’iyyarsu da ra’ayinsu na siyasa
  • Shettima ya bayyana haka zaman taron kaddamar da littafi da ya haɗa da ‘yan siyasa daga APC, PDP, NNPP da ADC

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya yi magana kan jam'iyyun adawa a Najeriya.

Shettima ya shaidawa ‘yan siyasa cewa dukkansu daya suke wajen gina kasa, ko da kuwa jam’iyyar su daban ne.

Kashim Shettima ya tura sako ga yan adawa
Kashim Ba jam'iyyun Najeriya shawara. Hoto: Kashim Shettima.
Source: Facebook

Shettima ya fadi haka a Abuja wajen kaddamar da littafin “OPL245: The Inside Story of the $1.3b Nigerian Oil Bloc” da Mohammed Bello Adoke ya rubuta, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

An hango Kashim Shettima, Kwankwaso, El-Rufa'i da Saraki tare a Abuja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ADC ke kara karfi a Najeriya

Wannan jawabi ya fito ne a daidai lokacin da ake ta hadin gwiwa da sauya sheka tsakanin ‘yan siyasa gabanin zaben shekarar 2027 mai zuwa.

A baya-bayan nan wasu ‘yan adawa da suka yi hadaka sun amince da jam’iyyar ADC a matsayin dandalinsu don 2027.

Hakan na karawa jam'iyyun adawa karfin cewa za su iya kwace mulki a hannun Bola Tinubu a zaben 2027.

Goodluck Jonathan ya zargi gwamnatin Buhari

Littafin na Adoke, wanda ya taba zama Antoni Janar a gwamnatin Goodluck Jonathan, ya yi bayani sosai kan yadda aka alakanta shi da batun OPL245.

A wajen taron, tsohon shugaban kasa, Jonathan ya ce bayan barinsa mulki a 2015, gwamnatin Muhammadu Buhari ta dinga muzanta jami’ansa da tuhuma.

Jonathan, wanda Anyim Pius Anyim ya wakilta, ya ce Adoke ya sha wahala a gida da wajen kasa, amma yau ga shi yana nan da rai da lafiya.

Kara karanta wannan

2027: ADC ta fara gargadin ƴaƴanta kan takarar shugaban ƙasa bayan hadaka

Kashim Shettima ya zargi Jonathan lokacin da yake gwamna
Kashim Shettima ya fadi yadda Jonathan ya yi kokarin cire shi. Hoto: Kashim Shettima.
Source: Facebook

Shettima ya zargi Jonathan da kokarin cire shi

Shettima ya ce Jonathan ya taba yunkurin cire shi a matsayin gwamnan Borno amma Adoke ya ja kunnen shugaban kasar da cewa hakan ba daidai ba ne.

Shettima ya ce:

“Adoke ya gaya masa, ‘shugaban kasa, ba ka da ikon cire gwamna mai ci, wannan ya karfafa zumuncin mu har abada.”

Ya kuma ce shugabanni na yanzu su fara rubuta abubuwan da suka fuskanta domin tarihi, maimakon boye su ko watsi da su gaba daya.

“A Najeriya, mun jima da yin shiru kan abubuwan da suka faru. Ya kamata mu fara rubuta tarihinmu don tunawa da su a gaba."

Cewar Shettima

Shettima ya yi jaje bayan ambaliyar ruwa

Kun ji cewa mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya kai ziyara garin Mokwa a jihar Neja domin jajen ambaliyar da ta faru a makon jiya.

Kashim Shettima ya ce Shugaba Tinubu ya ba da umarnin fitar da Naira biliyan 2 domin gyara gidajen da ruwa ya lalata a Mokwa.

Gwamnatin Neja ta tabbatar da cewa zuwa yanzu an gano gawarwakin mutane sama da 200 kuma ana ci gaba da laluben mamata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.