Tsohon Jigo a PDP Ya Gano Babbar Matsalar Jam'iyyar Gabanin Zaben 2027, "Atiku Ne"

Tsohon Jigo a PDP Ya Gano Babbar Matsalar Jam'iyyar Gabanin Zaben 2027, "Atiku Ne"

  • An nuna yatsa ga tsohon mataimakin shugaban ƙasan Najeriya, Atiku Abubakar kan matsalolin da suka addabi PDP
  • Tsohon mai ba PDP shawara kan harkokin shari'a ya bayyana cewa Atiku ne babbar matsalar jam'iyyar
  • Ya zarge shi da kasa taka rawar da ya kamata ya taka a jam'iyyar duk kuwa da irin magoya bayan da yake da su

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohon mai ba PDP shawara kan harkokin shari'a, Jacob Mark, ya nuna yatsa ga Atiku Abubakar kan matsalolin da suka addabi jam'iyyar.

Jacob Mark ya bayyana tsohon mataimakin shugaban ƙasan na Najeriya kuma Turakin Adamawa, a matsayin babban matsalar jam’iyyar PDP.

An danganta Atiku da matsalolin PDP
An bayyana Atiku a matsayin babbar matsalar PDP Hoto: @atiku
Source: Facebook

Jacob Mark ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin 'Morning Show' na tashar Arise Tv.

Kara karanta wannan

2027: ADC ta fara gargadin ƴaƴanta kan takarar shugaban ƙasa bayan hadaka

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An nuna yatsa ga Atiku kan rikicin PDP

Ya ce tsohon mataimakin shugaban ƙasa ya gaza taka rawar uba da ake tsammanin zai taka, duba da ƙwarewarsa da kuma dumbin magoya bayansa a cikin jam’iyyar.

A maimakon haka, sai dai yana ta sauya jam’iyya daga wannan zuwa waccan, al’adar da ta zama tamkar dabi’arsa.

"Babbar matsalar PDP ita ce Atiku Abubakar."

- Jacob Mark

Tsohon jigon PDP ya koka kan halin ƴan siyasa

Jacob Mark ya lura cewa ƙasa da shafe shekara biyu a wannan gwamnatin da aka zaɓa a 2023 ta fara aiki, wasu ƴan siyasa sun fara tattaunawa kan zaɓen gaba.

Ya ce kamata ya yi a ce sun matsa lamba ga shugaban ƙasa wajen sauke alhakin da ke kansa da kuma tilasta samar da ingantaccen shugabanci.

Jacob Mark ya jaddada cewa ya kamata a mayar da hankali kan shugabanci da ainihin ayyuka da za su amfani ƴan Najeriya.

Kara karanta wannan

Moro: Babban sanatan PDP a majalisa ya tsage gaskiya kan shiga hadaka

Tsohon jigo a PDP ya yi kalamai kan Atiku
Jacob Mark ya nuna yatsa ga Atiku Hoto: @atiku
Source: Facebook

Ya yi gargaɗin cewa wannan tattaunawa da wuri kan wanda zai tsaya takara a 2027 wata matsala ce mai jan hankali daga abubuwan da suka fi muhimmanci.

"Yanzu duk tattaunawar siyasa ya koma kan zaɓe na gaba. Kuma a wurina, wannan abin takaici ne. Babu wanda ke magana kan shugabanci. Babu wanda ke tunawa da jama’ar da suka kaɗa ƙuri’a."
"Babu wanda ke tattauna halin da ƴan Najeriya ke ciki a titi. Tun yanzu har an koma magana kan zaɓe na gaba."
"A wurina, wannan abin damuwa ne. Jam’iyyar da ke mulki ba ta damu ba. Ta sami cikakkiyar dama tana faɗin duk abin da take so domin jam’iyyar adawa ta rikice. Ta rasa ƙarfin ta. Babu wanda ke tambayar irin abubuwan da ke faruwa a cikin gwamnati."

- Jacob Mark

Segun Showunmi ya caccaki Atiku

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon hadimin Atiku Abubakar, Segun Showunmi, ya yi kalaman suka a kansa.

Kara karanta wannan

Takara: Jigon ADC ya fara tone tone kan yadda Wike ya raba 'cin hanci' a 2022

Segun Showunmi ya caccaki Atiku kan yadda ya ci gaba da nacewa wajen yin takarar shugaban ƙasan Najeriya.

Ya bayyana cewa lokaci ya yi da Atiku zai koma gefe domin baya bin ƴan Najeriya bashin zama shugaban ƙasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng