APC Ta Magantu kan Yiwuwar Samun Matsala bayan Saukar Ganduje, Ta Fadi Tasirinsa

APC Ta Magantu kan Yiwuwar Samun Matsala bayan Saukar Ganduje, Ta Fadi Tasirinsa

  • Sakatare na kasa na jam’iyyar APC ya yi magana kan rade-radin cewa fitan Abdullahi Ganduje zai jawo matsala
  • Sanata Ajibola Basiru, ya ce murabus din Ganduje ba zai janyo rikici a cikin jam’iyyar ba kamar yadda ake yadawa
  • Basiru ya ce Ganduje ya taimaka wajen karfafa jam’iyyar, inda wasu jihohi suka shiga APC tun bayan zaben su a watan Agusta 2023

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Sakataren jam'iyyar APC, Sanata Ajibola Basiru ya magantu kan tasirin Abdullahi Ganduje.

Basiru ya ce murabus da tsohon shugaban jam’iyyar, Ganduje, ba zai jawo wata matsala a cikin jam’iyyar ba.

An yabawa tasirin Ganduje a jam'iyyar APC
APC ta yabawa Abdullahi Ganduje kan kokarinsa. Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
Source: Facebook

APC ta magantu bayan murabus din Ganduje

Sakataren jam'iyyar APC ya yi wannan bayani ne a wani taron manema labarai a yau Laraba, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

'Kofarmu a buɗe take': Jam'iyyar ADC ta tura goron gayyata ga Dauda Lawal

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Basiru ya karyata jita-jitar da ke yawo kan saukar Ganduje, yana mai cewa an yaba masa bisa kokarinsa.

Ya ce Ganduje ya sake farfado da jam’iyyar a matsayin shugabanta na kasa saboda kokarinsa.

Ganduje ya ajiye mukaminsa ne bayan rade-radin cewa tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso, na shirin shiga jam’iyyar APC.

Sai dai Basiru, wanda ya yabawa tasirin Ganduje a jam’iyyar, ya ce wasu karin jihohi sun shiga APC a lokacinsa.

APC ta yabawa Ganduje bayan gudunmawar da ya bata
APC ta musanta samun matsala bayan murabus din Ganduje. Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
Source: Facebook

Kokarin Ganduje lokacin da ya rike APC

Basiru ya ce jam’iyyar ta karu a fannin gudanarwa tun bayan zaben su a ranar 3 ga watan Agusta, 2023.

Basiru ya ce:

“Idan ka duba sanarwar da jam’iyya ta fitar, an yaba masa bisa kokarin da ya yi wajen sake farfado da jam’iyyar.
"A karkashin jagorancinsa, wasu karin jihohi sun shiga jam’iyyar kuma a fannin gudanarwa, jam’iyyar ta kara karfi tun bayan zabenmu a matsayin Shugaban Kasa da Sakatare na Kasa a ranar 3 ga watan Agusta, 2023.

Kara karanta wannan

'Babu abin da zai raba ni da Buhari': Tsohon minista ya musanta barin jam'iyyar APC

"Bayan saukar Sanata Abdullahi Adamu da Sanata Iyiola Omisore ne muka hau kan mukamanmu a ranar 3 ga watan Agusta, 2023.
"Saboda haka saukar Dr Abdullahi Umar Ganduje ba yana nufin wata matsala ba, rade-radi ne kawai.”

Baya ga haka, Sakatare na kasa na APC ya karyata jita-jitar cewa Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, wanda dan jam’iyyar PDP ne, na shirin sauya sheka zuwa APC.

“Adeleke ba zai shiga jam’iyyarmu ba. Na sani cewa a yau babu wani shirin sauya sheka da yake yi kawai jita-jita ce."

- Cewar Basiru

Sakatare na kasa na jam’iyyar APC ya kara da cewa, zai mara baya ga duk wata matsaya da Shugaba Tinubu ya dauka.

Tinubu ya ba Ganduje mukami

Kun ji cewa gwamnatin Bola Tinubu ta nada tsohon shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, a matsayin shugaban gudanarwar hukumar FAAN.

Abdullahi Ganduje ya samu mukamin ne kwanaki kadan bayan ya ajiye shugabancin jam’iyya mai mulki a Najeriya ta APC.

Hukumar FAAN na da alhakin kula da dukkan filayen jiragen saman da ke fadin Najeriya gaba daya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.