Adamawa: Matar Tsohon Gwamna Ta Watsar Masa da PDP, ta Koma ADC a Yobe

Adamawa: Matar Tsohon Gwamna Ta Watsar Masa da PDP, ta Koma ADC a Yobe

  • Matar tsohon gwamnan Adamawa ta fice daga jam’iyyar PDP zuwa ADC a wani taron mata yayin da haɗaka ke kara ƙarfi
  • Zainab Boni Haruna ta soki gwamnatin Bola Tinubu bisa gazawa wajen tsaro, cin hanci, tana mai cewa mutane suna shan wahala
  • Ta ce tana tare da Adamu Maina Waziri, wanda ke ba ta shawara, tana kuma kira ga mata da matasa su shirya wa zaben 2027

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Damaturu, Yobe - Jam'iyyar ADC ta sake samun ƙarfi a jihar Yobe bayan ficewar matar tsohon gwamna.

Matar tsohon gwamnan Adamawa, Boni Haruna ta tabbatar da ficewarta daga jam'iyyar PDP.

Matar tsohon gwamna ta koma ADC
Matar gwamnan Adamawa ta bar PDP zuwa ADC. Hoto: Maimuna Chiroma.
Source: Facebook

Zainab Boni Haruna ta sanar da ficewarta daga PDP zuwa jam’iyyar adawa ta ADC a Damaturu, Yobe, cewar rahoton Aminiya.

Kara karanta wannan

ADC ta shiga Borno da karfinta, tana wawashe yan PDP da APC gabanin 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yobe: ADC ta rikita jam'iyyun PDP da APC

Hakan ya biyo bayan kara samun ƙarfi da jam'iyyar ADC ke yi a jihar Yobe wacce APC ne mulkinta karkashin Mai Mala Buni.

Wasu majiyoyi sun ruwaito cewa mafi yawan mambobin jam'iyyar PDP da jiga-jiganta a Yobe sun yi watsi da ita zuwa jam'iyyar ADC.

Har ila yau, akwai wasu yan APC da suka sauya sheka zuwa ADC yayin da suke sukar tsarin mulkin jam'iyyar.

Ko a karshe mako, wani hadimin gwamnan jihar Yobe ya yi murabus daga mukaminsa inda ya sauya sheka zuwa jam'iyyar ADC da aka ƙaddamar saboda hadaka.

Matashin Babagana Yakubu Mohammed wanda hadimi ne na musamman ga Mai Mala Buni ya yi murabus daga APC.

Ya bayyana cewa ya gaji da yadda aka bar magoya bayan APC na ƙasa ba tare da karramawa ko daraja ba duk da sadaukarwa.

Jam'iyyar ADC na cigaba da samun karuwar a Yobe
Matar tsohon gwamnan Adamawa, Zainab Boni Haruna ta koma ADC. Hoto: Legit.
Source: Original

PDP ta yi babban rashi a jihar Yobe

Kara karanta wannan

Haɗakarsu Atiku ta ƙara ƙarfi, jam'iyyar ADC ta yi babban kamu a jihar Ƙatsina

Zainab 'yar asalin Nangere ce a Jihar Yobe inda ta bayyana sauyin jam’iyya ne a wani taron mata na ADC da aka shirya a Damaturu.

Ta bayyana matsin rayuwa da rashin shugabanci da gazawar gwamnatin Tinubu tana cewa mutane suna shan wahala, yunwa ta yi yawa.

Zainab ta ce:

“Na yanke shawarar shiga jam’iyyar ADC tare da... Alhaji Adamu Maina Waziri."

Ta kara da cewa PDP na fama da rikici da ya sa mambobi da dama ke sauya sheka zuwa ADC, inda ta ce sulhu ya gagara.

“Kafin na yanke shawarar ficewa daga PDP, sai da na je gidan Adamu Waziri… domin neman shawarar siyasa a wurinsa."

- Cewar Zainab

A karshe, ta bukaci mata da matasa a sauran jam’iyyu su shirya wa babban zaben shekarar 2027 don kawo canji a kasa.

Tsohon minista a Yobe ya koma ADC

Mun ba ku labarin cewa Adamu Waziri, daya daga cikin wadanda suka kafa PDP kuma mamba a kwamitin amintattu (BoT), ya fice daga jam’iyyar, ya koma ADC.

Adamu Waziri ya ce ya fice daga PDP ne saboda yadda ya damu da wahalar da 'yan Najeriya ke fuskanta da kuma rashin karfin PDP.

Ya bayyana cewa jam'iyyar ADC tana da ikon kwace mulki daga APC a 2027 don dawo da martabar tattalin arziƙin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.