Atiku da Ƴan Haɗakar ADC Za Su Dawo da Tallafin Fetur a 2027? Gwamna Ya Jefo Tambaya

Atiku da Ƴan Haɗakar ADC Za Su Dawo da Tallafin Fetur a 2027? Gwamna Ya Jefo Tambaya

  • Gwamnan Katsina ya kalubalanci Atiku Abubukar, Peter Obi da sauran ƴan haɗakar ADC kan batun tallafin man fetur
  • Malam Dikko Umaru Raɗɗa ya nuna cewa ba ta yadda jagororin adawa za su iya dawo da tallafin kuma su tafiyar harkokin gwamnati ko da sun ci zaɓe
  • Mai girma gwamnan ya buƙaci ƴan haɗaka su fito su yi wa ƴan Najeriya bayanin abin da za su yi wanda ba shi Tinubu ke yi ba a yanzu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Katsina - Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Radda, ya kalubalanci ƴan haɗakar ADC, waɗanda ke ɓaɓatun za su kwace mulki daga hannun APC a 2027.

Gwamna Radda ya buƙaci Atiku Abubakar da sauran ƴan haɗaka su bayyana wa 'yan Najeriya shirin da suke da shi kan tallafin man fetur da yadda za su tafiyar da mulki idan suka samu dama.

Kara karanta wannan

Lukman ya rabawa Atiku da Obi gardama, ya faɗi wanda ADC za ta tsayar takara a 2027

Gwamnan Kastina, Malam Dikko Radda.
Gwamnan Katsina ya ƙalubalanci ƴan haɗaka kan batun tallafin man fetur Hoto: Ibrahima Kaulaha Mohammed
Source: Facebook

Malam Dikko Raɗɗa ya yi wannan furuci ne a wata hira da aka yi da shi a shirin Sunrise Daily na kafar watsa labaran Channels tv ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Raɗɗa ya kalubalanci ƴan haɗaka

Ya jefi ƴan haɗakar da tambayar ko za su iya dawo da tallafin man fetur idan sun karɓi mulki? Yana mai cewa abu ne mai wahala su iya tafiyar da gwamnati.

Dikko Raɗɗa ya kuma tambayi shugabannin adawar abin da za su yi daban da irin yadda gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ke gudanar da aiki yanzu.

"Wadanda ke son tsayawa takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin ADC, su fito su gaya wa ‘yan Najeriya ko za su dawo da tallafin man fetur?
"Idan kuma ba za su dawo da tallafin ba, to su bayyana yadda za su tafiyar da gwamnati da kuma daga ina za su samo kuɗin gudanarwar,” in ji Radda.

Kara karanta wannan

Ko gezau: Minista ya fadi fargabar Tinubu kan zaben 2027

Dikko Raɗɗa ya faɗi dalilin haɗewar ƴan adawa

Gwamnan ya buƙaci shugabannin adawa da su daina ruɗar ‘yan Najeriya, yana mai cewa sun haɗu ne kawai don ba su a cikin gwamnati.

Dikko Raɗɗa ya ce lokacin yaudarar ƴan Najeriya ya wuce, ya kamata jagororin haɗakar ADC su fito fili su bayyana manufofinsu.

“Mu fuskanci gaskiya, mu faɗa wa kanmu gaskiya, lokacin yaudarar ‘yan Najeriya ya wuce. Waye a cikinsu da bai kasance cikin gwamnati a baya ba?" In ji Raɗɗa.
Dikko ya aika tambaya ga su Atiku.
Malam.Dikko Radda ya buƙaci hadakar yan adawa ta fito ta gayawa ƴan Najeriya gaskiya Hoto: @Atiku
Source: Twitter

Wannan kalamai na Raɗɗa na zuwa ne yayin da haɗakar ADC ke samun karuwa a jihohin Najeiya ciki har da jihar da yake shugabanci watau Katsina.

Gwamma Raɗɗa ya nuna cewa matukar ƴan haɗakar ba za su dawo da tallafin man fetur ba, to ba su ɗa wani abu da za su iya yi wa ƴan Najeriya, rahoton Vanguard.

Auwal Ibrahim, wani ɗan Katsina da ya shiga ADC ya shaidawa Legit Hausa cewa da izinin Allah sai sun kayar da APC daga sama har ƙasa a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Gwamna Radda ya yi fallasa kan hadakar 'yan adawa

Ya ce a Katsina ba su bukatar sai sun yi yawo kwararo-kwararo wajen neman mabiya domin jama'a sun gaji da mulkin Dikko Raɗɗa.

Auwal ya ce:

"Gwamnanmu dama da iya magana, akwai surutu amma hakan ba zai hana mu samu nasara a kansa ba. Manyan ƴan adawar Katsina irinsu Mustapha Inuwa da sauransu, duk za su dawo ADC, za mu kawar da APC in sha Allah.

Dikko Radda zai sama abokin takarar Tinubu?

A wani labarin, kun ji cewa Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya musanta raɗe-raɗin da ake alaƙanta shi da zama abokin takarar Tinubu a 2027.

Malam Dikko ya karya duka rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta, yana mai cewa hankalinsa na kan ƙoƙarin sauke nauyin al'ummar Katsina.

Ya kuma tabbatar da cewa babu hannunsa a wannan kamfe da kuma hotunan da wasu ke yaɗawa na cewa zai zama abokin takarar Shugaba Tinubu a 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262