An Yi Gagarumin Taron ADC a Gombe, 'Yan APC da PDP Sun Shiga Hadaka
- Jam’iyyun adawa a jihar Gombe sun amince da jam’iyyar ADC a matsayin dandalin tinkarar zabe a shekarar 2027
- Taron hadakar ya gudana ne a wani babban taro da ya samu halartar fitattun ‘yan siyasa daga jam'iyyun PDP da APC
- Tsohon minista, Sanata Abdullahi Idris Umar ya ce hadakar za ta ceci Gombe da kasa baki daya daga halin kunci
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Gombe - A wani muhimmin mataki da ka iya sauya taswirar siyasa a jihar Gombe, jam’iyyun adawa da dama sun amince da jam’iyyar ADC a matsayin sabuwar mafita.
'Yan adawa sun yi taro a Gombe domin karfafa adawa da fatan karbe mulki daga hannun APC a zaben 2027.

Source: Facebook
Daily Trust ta wallafa cewa ta gano hakan ne a babban taron da aka gudanar a Gombe ranar Talata, inda wakilan jam’iyyar ADC da fitattun jiga-jigan ‘yan adawa suka halarta.

Kara karanta wannan
'APC, PDP, ADC, duk ɗaya ne': Shettima ya tura saƙo ga ƴan adawa ana batun haɗaka
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wajen taron, tsohon ministan sufuri kuma jagoran hadakar jam’iyyun adawa a jihar, Sanata Abdullahi Idris Umar ya ce bai wai domin karbe mulki aka yi hadakar ba.
Sanata Idris ya ce an yi hadakar ne domin ceton al’ummar jihar Gombe da ma kasa gaba daya daga halin kuncin tattalin arziki da tsadar rayuwa da gwamnatin APC ke haddasawa.
"ADC ta bude kofa ga kowa' – Sanata Idris
Sanata Idris Umar ya bayyana cewa jam’iyyar ADC za ta fara rajistar mambobi a dukkan mazabu 114 da ke jihar domin fadada yaduwar jam’iyyar da karfafa ta daga tushe.
Ya jaddada cewa kofa a bude take ga kowa ba tare da la’akari da inda mutum ya fito ba ko irin jam’iyyar da ya fito a baya.
Ya kuma bukaci al’ummar jihar da su yi amfani da damarsu a zabe mai zuwa domin su zabi masu gaskiya da adalci, yana mai cewa mutane ne alkalai tsakanin gwamnati da 'yan adawa.
Bayanin jagoran ADC a jihar Gombe
Tun da farko, jagoran jam’iyyar ADC na jihar Gombe, Auwal Abba Barde, ya tarbi sababbin mambobi hannu biyu-biyu.
Auwal Abba Barde ya tabbatar musu da cewa za su samu dama su taka muhimmiyar rawa a nasarar jam’iyyar a zaben da ke tafe.
Ya ce lokaci ya yi da za a samu sauyi domin fuskantar kalubalen tattalin arziki da rashin tsaro da ke addabar jihar da kasa baki daya.
Legit ta tattauna da Hassan Haruna
Wani matashi da ya halarci taron ADC a Gombe mai suna hassan Haruna ya ce za su yi iya kokarinsu wajen kawo canji a jihar.
Hassan ya ce:
"Da yardar Allah ba za mu zama kamar APC ba. Za mu yi kokarin kawo canji mai kyau. Muna fatan mutane za su mana kallo mai kyau."
‘Yan siyasa sun halarci taron ADC a Gombe
Jaridar Punch ta rahoto cewa taron ya samu halartar fitattun ‘yan siyasa daga jam’iyyun PDP da APC a jihar.
Daga cikinsu akwai AVM Shehu Adamu Fura (Mai ritaya) da Dr Babayo Ardo, wadanda suka nemi tikitin takarar gwamna a PDP a 2023.
Haka kuma, daga APC, tsohon mataimakin gwamnan jihar, John Lazarus Yoriyo, da wakilan tsohon ministan sadarwa, Sheikh Isa Ali Pantami, sun halarci taron.

Source: Facebook
Rahotanni sun tabbatar da cewa wasu tsofaffin kwamishinoni da manyan ‘yan siyasa daga bangarori daban-daban sun hade da ADC a jihar.
Jigon PDP ya koma ADC a Gombe
A wani rahoton, kun ji cewa AVM Shehu Adamu Fura (Mai ritaya) ya fita daga jam'iyyar PDP zuwa ADC a jihar Gombe.
Binciken Legit Hausa ya gano cewa Adamu Fura ne shugaban kwamitin sulhu na PDP kafin ya sauya sheka.
Hakan na zuwa ne yayin da guguwar sabuwar tafiyar hadakar 'yan adawa ke cigaba da karbuwa da jan 'yan siyasa a Najeriya.
Asali: Legit.ng

