ADC: Abubuwa 5 da za Su iya Karya Lagon APC da Kifar da Tinubu a 2027

ADC: Abubuwa 5 da za Su iya Karya Lagon APC da Kifar da Tinubu a 2027

  • Ana hasasehn cewa jam’iyyar ADC mai adawa na lura da rikice-rikicen cikin gida da ke kara fitowa a APC yayin da 2027 ke karatowa
  • Sauya sheka da zargin gazawar tsarin mulki na shugaba Bola Tinubu na daga cikin manyan matsalolin APC da ADC ke nazari
  • Ganin yadda yankin Arewa ke nuna rashin jin dadi da mulkin Tinubu, ana ganin hakan zai zama kofar samun karbuwa ga ADC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Yayin da Najeriya ke kara matsowa gabar babban zaben 2027, jam’iyyar ADC na kokarin tsara dabarar ta ne bisa wasu manyan kurakurai da ke bayyana cikin jam’iyyar APC mai mulki.

Rikice-rikicen cikin gida na APC da sauyin salon siyasar Arewa na iya zama barazana ga burin Bola Tinubu na wa’adi na biyu.

Kara karanta wannan

ADC ta gano shirin gwamnatin Tinubu na ruguza hadakar 'yan adawa a jihohi

Ana ganin tsare tsaren Tinubu za su jawo masa rashin karbuwa a 2027
Ana ganin tsare tsaren Tinubu za su jawo masa rashin karbuwa a 2027. Hoto: Bayo Onanuga|Atiku Abubakar|Peter Obi
Source: Facebook

Vanguard ta yi wani rahoto kan muhimman abubuwa biyar da ka iya kassara APC tare da bayar da dama ga kawancen 'yan adawa a ADC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Rikicin cikin gida a APC

Jam’iyyar APC na fama da sabani tsakanin bangarorin ACN, CPC da nPDP tare da rashin jin dadi game da rabon mukamai da tsauraran matakan tattalin arziki.

ADC na sa ido kan wannan rikici, kuma idan har APC ta kasa warware shi, hakan na iya jawo karayar jam’iyyar kafin 2027.

Ana zargin shirin Tinubu na sauya mataimakinsa, Kashim Shettima, da kuma murabus din Abdullahi Ganduje daga shugabancin jam’iyyar, na iya kara rikita APC.

2. Tasirin Kwankwaso a Kano da Arewa

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na da karfi sosai a jihar Kano da wasu sassan Arewa maso Yamma.

Saukar Ganduje ya sa aka fara tunanin Kwankwaso zai koma APC, amma ana ganin zuwan ADC ya sa ya tsaya yana duba inda siyasar Arewa za ta karkata.

Kara karanta wannan

ADC ta yi martani ga fadar shugaban kasa, ta ce ta gama gigita APC

Matsayin da Kwankwaso zai dauka nan gaba na iya zama tamkar karshen APC ko samun sabon karfi gare ta a yankin da ke da mafi yawan kuri’u.

3. Ra’ayin 'yan Arewa kan Tinubu

A halin yanzu, wasu 'yan Arewa na ganin gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu na nuna wariya.

ADC ta fara tuntubar fitattun ‘yan siyasa daga yankin kuma rahotanni sun nuna cewa ADC ta karbe tsarin PDP a Yobe, Gombe da Adamawa.

Zainab Galadima, ‘yar jam’iyyar APC kuma ‘yar Buba Galadima, ta bayyana cewa ra’ayin jama’ar Arewa baya tare da Tinubu.

4. Tasirin tsare tsaren Bola Tinubu

Gwamnatin Tinubu na mayar da hankali kan gina tsare tsare, amma mutane na ganin hakan ya yi nesa da halin da talakawa ke ciki.

Ana zargin cewa wannan tsarin ya kara dagula rayuwar jama’a tare da haifar da ra’ayin cewa gwamnati na nesa da damuwar mutane.

ADC da sauran 'yan adawa na amfani da wannan damar wajen sukar gwamnatin da cewa ba ta kula da wahalhalun jama’a.

'Yan adawa yayin zaben ADC a matsayin dandalin hadaka
'Yan adawa yayin zaben ADC a matsayin dandalin hadaka. Hoto: Atiku Abubakar
Source: UGC

5. Sabon kawancen da fatan kawo sauyi

Kara karanta wannan

Yaƴan jagororin ADC da ke cikin jam'iyyun APC da PDP a yau

Ko da yake hadin kan da ke karkashin ADC bai gama karfi ba, yana nuna cewa adawa na shirin kafa sabuwar gagarumar jam’iyya.

Idan har ‘yan adawa suka yi amfani da wannan dama ta bayyana manufofi masu tasiri, ADC na iya zama sauyin da ‘yan Najeriya ke jira.

Bwala ya ce APC za ta ci zabe a saukake

A wani rahoton, kun ji cewa fadar shugaban kasa ta ce zaben shekarar 2027 zai zamo mafi sauki ga APC.

Hadimin shugaban kasa Bola Tinubu, Daniel Bwala ne ya bayyana haka a wata hira da aka yi da shi a Abuja.

Daniel Bwala ya bayyana cewa nan da wata 6 masu zuwa za a daina maganar hadakar 'yan adawa kwata kwata a fadin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng