ADC Ta Shiga Borno da Karfinta, Tana Wawashe Yan PDP da APC gabanin 2027
- Tun bayan bayyanar da ADC ta yi a matsayin jam'iyyar hadaka ta kalubalantar APC, aka fara samun sauya sheka a sassa da dama
- Fitattun 'yan siyasa da dama sun sauya sheƙa daga PDP da APC zuwa ADC tare da dubunnan magoya bayansu a jihar Borno
- Daga cikin wadanda suka sauya cewa akwai tsofaffin yan takarar gwamna da sauran yan siyasa daga jam'iyyun PDP, LP da APC
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Borno – Yayin da shirye-shiryen babban zaɓen 2027 ke ƙara ɗaukar hankali, jam’iyyar ADC na samun ƙarfi a jihar Borno, bayan kaddamar da sabon shugaban rikon kwarya na ƙasa, David Mark.
Rahotanni sun tabbatar da cewa ana samun sauya sheƙa mai yawa daga wasu jiga-jigan jam’iyyun adawa da kuma daga cikin jam’iyyar APC a Borno, zuwa ADC.

Source: Twitter
Jaridar Vanguard ta ruwaito Mattawali Kashim Ibrahim Imam, tsohon dan takarar gwamna a PDP kuma jigo a APC, yana gudanar da liyafa ta musamman a yunkurin sauya sheka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Borno: ADC na shirin rikita PDP, APC
Jaridar Independent ta ruwaito fitattun ‘yan adawa guda biyu a Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar na PDP da Mista Peter Obi na LP na daga cikin masu jagorantar ADC.
A cewar rahotanni daga Borno, Alhaji Idris Mamman Durkwa, tsohon mai neman takarar gwamna ya sauya sheka zuwa ADC.
Haka kuma Hon. Sheriff Banki, wanda ke jagorantar matasa da masu ruwa da tsaki, ya ja dubunnan magoya bayansa daga PDP zuwa ADC.
Durkwa, ya jagoranci wani gangami a Maiduguri a makon da ya gabata, inda mutane daga jam’iyyun adawa daban-daban da ma daga APC suka koma ADC.
Jagororin da suka koma ADC a Borno
Cikin fitattun ‘yan siyasar da suka sauya sheƙa zuwa ADC akwai Hon. Mohammed Umara Kumalia, tsohon shugaban marasa rinjaye a majalisar wakilai.
Sai Alhaji Saleh Kida, mataimakin ɗan takarar gwamna na PDP a 2023 da kuma Alhaji Ali Wurge, tsohon ma’ajin ƙasa na PDP.

Source: Twitter
Sauran sun hada da Hon. Babakura Abba Yusuf, ɗan takarar majalisar wakilai a MMC a 2023 da Hon. Abdulrazaq Ahmed Zanna, tsohon dan takarar PDP na kujerar Bama, Ngala da Kala-Balge.
Hon. Maina Justice, jigo daga karamar hukumar Jere, Hon. Fali Wubulari, tsohon ɗan majalisar dokoki daga Askira-Uba da wasu tsofaffin yan takara a PDP da LP sun koma ADC.
Dalung ya fadi dalilin shiga ADC
A baya, kun samu labarin cewa tsohon ministan matasa da wasanni kuma jigo a jam’iyyar ADC, Solomon Dalung, ya caccaki salon mulkin gwamantin APC.
Tsohon Ministan ya bayyana cewa wannan na daga cikin dalilan da yan adawa suka hada kansu a jam'iyya guda domin tsamo yan Najeriya daga talauci.
Ya kara da musanta cewa son kai ne ya sa su shiga ADC, ya ce babu ɗaya daga cikinsu da ke da niyyar neman shugabanci don biyan bukatun kansa kawai.
Asali: Legit.ng

