'Daga Allah ne': Malami Ya Gargaɗi Tinubu kan Sanya Rai a Tazarce bayan Hadakar ADC
- Fasto Elijah Ayodele ya gargadi Tinubu kada ya dogara da karfinsa don komawa mulki a zaben shekarar 2027
- Ya ce sihiri ne kadai zai iya karya wannan kawance, kuma idan Tinubu bai dauki mataki ba yanzu, zai fuskanci barazana
- Ayodele ya bayyana cewa wasu mutane a jam’iyyar Tinubu 'yan amana ne, kuma wasu abubuwa shida za su iya rusa mulkinsa gaba daya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Lagos - Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual Church, Elijah Ayodele ya sake magana kan zaben 2027 da ke karatowa.
Fasto Ayodele ya gargadi Shugaba Bola Ahmed Tinubu kada ya samu tabbaci a ransa zai zarce a zaben 2027.

Source: Facebook
2027: Fasto ya fadi tasirin jam'iyyar ADC
Faston ya fadi haka ne a wajen kaddamar da littafinsa na hasashe na shekara-shekara na 2025/2026 mai suna ‘Warnings To The Nations’, cewar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce kafa kawancen ADC da ‘yan adawa suka yi daga sama ne, kuma hanya ce tilo da za a karya shi ita ce ta hanyar sihiri.
Faston ya ce idan ba a yi dace ba wannan ƙawance ko hadakar yan adawa babu mai iya karya su.
Ya ce:
"Watakila sihiri ne kadai zai iya karya wannan kawance, kawancen daga sama ne, dole Tinubu ya shirya."
A cikin littafin, Ayodele ya bayyana cewa idan Tinubu ya dogara da karfinsa, kawancen ADC na iya ba shi mamaki da rusa jam’iyya mai mulki.
Ya kuma bukaci shugaban kasar da ya dauki mataki cikin gaggawa kafin lokaci ya kure masa don samun nasarar tunkarar zabe.

Source: UGC
Fasto ya gargadi Tinubu kan zaben 2027
A cewar Fasto Ayodele, tun tuni ya shawarci kawancen da farko suka hada kai da ADA da su koma ADC a cikin littafin da aka kammala tun Afrilu 2025.

Kara karanta wannan
'Shi ne kaɗai mafita' An faɗi mutum 1 idan ya shiga ADC zai iya kada Tinubu a 2027
Ya kara da cewa:
"Idan ya dogara da karfinsa, kawancen na iya ba shi mamaki kuma su fafata da jam’iyya mai mulki, wannan zabe zai wuce tunaninsa.
"Tinubu dole ya dauki mataki yanzu. Ya saurara yanzu ya yi abin da ya kamata. Ya aikata abin da ba a zata ba idan yana so ya ci.
'Ka da ka yaudari kanka': Fasto ga Tinubu
Ya kuma bukaci Tinubu da kada ya dogara da yawan mutanen da ke shigowa jam’iyyarsa saboda yawancinsu 'yan cin amana ne.
"Tinubu kada ya dauka komai yana tafiya daidai domin akwai mutane da dama da ke adawa da jam’iyyar da ke mulki. Kada ya yarda.
"Ya manta da yawan mutanen da ke shigowa jam’iyyarsa, ya manta da masu hayaniya da ke ciki."
- Cewar Fasto Ayodele
Fasto ya gano hanyar kayar da Tinubu
Kun ji cewa Fasto Elijah Ayodele ya bayyana dabarun da ya kamata ƴan adawa su yi idan suna son kayar da jam'iyya mai mulki a babban zaɓe na gaba.
Limamin cocin ya faɗi dabarun ne a lokacin da ƴan siyasa suka fara shirye-shiryen zaɓen 2027 a Najeriya.
Ayodele ya ce shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu zai yi duk mai yiwuwa domin ya ci gaba da mulkin ƙasar nan har tsawon shekaru takwas.
Asali: Legit.ng

