‘Ya Yi Masa Halacci’: An Fadi Alakar Buhari da Tinubu kan Zargin Sabani

‘Ya Yi Masa Halacci’: An Fadi Alakar Buhari da Tinubu kan Zargin Sabani

  • Malam Garba Shehu ya ce babu sabani tsakanin Muhammadu Buhari da Bola Tinubu bayan yada karairayi
  • Ya ce Buhari yana godiya ga jam’iyyar APC da ta ba shi damar mulki har sau biyu, kuma ba zai ci amanar jam’iyyar ba
  • Garba Shehu ya bayyana cewa Buhari da magoya bayansa ba za su taba ruguza APC ba, domin sun san irin wahalar da aka sha wajen kafa ta

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Mai magana da yawun tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya sake yin magana kan alakar Bola Tinubu da mai gidansa.

Malam Garba Shehu ya ce babu wani sabani tsakanin Buhari da Shugaba Tinubu kamar yadda wasu ke yadawa.

An karyata matsala tsakanin Buhari da Tinubu
Garba Shehu ya ce APC ta yi wa Buhari halacci. Hoto: Muhammadu Buhari, Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Twitter

Gaskiyar magana kan matsalar Buhari da Tinubu

Garba Shehu ya bayyana hakan a wata hira ta musamman da aka yi da shi a Trust TV a jiya Litinin 7 ga watan Yulin 2025.

Kara karanta wannan

ADC ta yi martani ga fadar shugaban kasa, ta ce ta gama gigita APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, duk wani labari da ke cewa akwai rashin jituwa tsakanin shugabannin biyu ba shi da tushe.

Shehu ya ce wannan ra’ayoyin jama’a ne kan alaka tsakanin Buhari da Tinubu wanda suke yadawa.

Ya ƙara da cewa Buhari har yanzu mamba ne na jam’iyyar APC, kuma yana mai godiya da yadda jam’iyyar ta ba shi dama ya shugabanci ƙasar har sau biyu.

Malam Garba Shehu ya ce Buhari ba zai taɓa cin amanar jam’iyyar da ta ɗaga shi har ya samu damar rike shugabancin Najeriya ba.

Ya ce:

“Buhari ya gaza sau uku, amma APC ce ta ba shi nasara, shi kuma bai manta ba.”
Garba Shehu ya kuma magana kan alakar Buhari da Tinubu
Garba Shehu ya musanta rashin jituwa tsakanin Buhari da Tinubu. Hoto: Muhammadu Buhari, Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Twitter

Abin da ya APC, Buhari nasara a baya

Ya ce wadanda suka sha wahala wajen kafa APC a 2014 ba za su kasance cikin masu ƙoƙarin rushe ta a yanzu ba.

A cewarsa, APC ta samu nasara ne bayan haɗin gwiwa mai wahala da sadaukarwa.

Kara karanta wannan

Yobe: Hadimin gwamna ya yi murabus, ya faɗi dalilansa na shiga jam'iyyar ADC

Don haka ba za su yarda a rusa jam’iyyar ba saboda tsananin ƙoƙarin da aka yi a wancan lokaci.

Garba Shehu ya ce magoya bayan Buhari ba sa damuwa da rade-radin da ake yadawa a kafafen watsa labarai, inda ya ce ba su damu da su ba, cewar TheCable.

A ƙarshe, ya ƙarfafa cewa Buhari zai ci gaba da kasancewa mai biyayya ga APC, kuma babu wata matsala tsakaninsa da Tinubu da za ta iya ɓalle jam’iyyar daga zuciyarsa.

An bukaci taya Buhari addu'a domin samun lafiya

Kun ji cewa Malam Garba Shehu ya tabbatar da cewa tsohon Shugaba Muhammadu Buhari na samun sauƙi bayan rashin lafiya da ya tafi duba lafiyarsa.

Garba Shehu ya ce Buhari ya kamu da rashin lafiya yayin duba lafiya na shekara-shekara da ya saba yi a ƙasar Birtaniya tun ba yau ba.

A baya, Buhari ya shafe sama da kwana 100 a London yana jinya, musamman a 2017, hakan ya sa mutane suka dage da yi masa addu'o'i.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.