'Shi ne Kaɗai Mafita' An Faɗi Mutum 1 Idan Ya Shiga ADC Zai Iya Kada Tinubu a 2027
- Wasu mazauna Jalingo da ke jihar Taraba sun bukaci ADC ta tsayar da Goodluck Jonathan takara a 2027
- Sun ce Jonathan na da karbuwa a Arewa da Kudu, kuma zai tsaya wa wa’adin mulki daya kacal wanda ya fi jan hankalin Arewa
- Masu magana sun jaddada cewa Jonathan zai kawo sauyin tattalin arziki, kuma su na bukatar ADC ta daina son kai ta mai da hankali kan nasara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Jalingo, Taraba - Wasu mazauna jihar Taraba sun hango mafita a zaben shekarar 2027 da ke tafe.
Mutanen sun bukaci shugabannin kawancen jam’iyyar ADC da su kau da son zuciya su tsayar da tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan.

Source: UGC
An bukaci ADC ta tsayar da Jonathan
Da suke magana da Tribune a hirarraki daban-daban a Jalingo ranar Lahadi, mazaunan sun bayyana cewa Jonathan ne mafita.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Suka ce Goodluck Jonathan ne mafi karfi da zai kayar da Bola Ahmed Tinubu a zaben shugaban kasa mai zuwa.
A cewarsu:
“Hanyar da tabbas za ta kawo nasara a 2027 ita ce tsayar da dan takara da Arewa da Kudu za su amince da shi, Jonathan ya dace da hakan."
Sun kara da cewa mafi yawan masu fahimtar siyasa a Arewa za su mayar da hankali ne kan zaben 2031, wanda ya kamata ya koma Arewa bayan wa’adin Kudu biyu.
“Za a kayar da Tinubu cikin sauki idan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ne dan takara, muna rokon shugabannin jam’iyyar su bar son rai su mayar da hankali kan dabarun nasara."
- In ji wani mazaunin Jalingo

Source: Facebook
'Dalilin da yan Arewa za su aminta da Jonathan'
Sun dage cewa Jonathan ne zabin da Arewa za ta fi karba, domin kundin tsarin mulki ya takaita shi ga wa’adi daya kacal.
“Abin da ’yan Najeriya ke so shi ne sauyi na gari, wani abu daban da APC. Idan wani daga Kudu ya ci, zai nemi wa’adi na biyu, mu kuma ba ma so a koma daga wahala zuwa wata wahalar.”
“Goodluck Jonathan ne zabin da yafi dacewa da kawancen, musamman ga ‘yan Arewa da za su kada kuri’a ne da sanin cewa zai yi wa’adi daya kacal."
Mr Clement Yakubu Tyokyaa Tar, Haruna Buba, Sadiq Maigeri da Sabastin Tsukwa, wadanda suka yi magana a madadin kungiyar, sun ce dawowar Jonathan zai dawo da daidaiton tattalin arziki da inganta rayuwar talakawa.
“Muna so mu tunatar da shugabannin kawance cewa Jonathan shi kadai ne dan takarar da Arewa za ta karba ba tare da fargaba ba.
"Bayan yard da shi a matsayin wanda zai saukaka matsin tattalin arziki, wa’adin mulki daya da zai yi babban abin la’akari ne.
Bello El-Rufai ya nemi gafarar Jonathan
Kun ji cewa Dan majalisar wakilai a jihar Kaduna, Bello El-Rufai, ya nemi afuwar tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan.
Bello El-Rufai ya nemi afuwar ne bayan sukar tsohon shugaban kasar a baya inda ya ce rashin wayonsa ne ya sa ya soke shi.
Ya bayyana cewa sai bayan ya ga mahaifinsa na shirin ziyartar Jonathan domin shawarwari ne ya gane irin mulkin kirki da ake da shi a wancan lokaci.
Asali: Legit.ng

