Matasan Arewa Sun Kunyata Haɗakarsu Atiku, Sun Hango Wanda Ya Dace da Najeriya a 2027
- Matasan Arewacin Najeriya sun jingine jam'iyyar haɗaka watau ADC, sun jaddada goyon bayansu ga Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu
- A cewarsu, bisa tsarin karɓa karɓa da ake amfani da shi a siyasar Najeriya, sai 2031 Bola Tinubu zai sauka ya ba ɗan Arewa
- Sun kuma yi watsi da kalaman ɗiyar dattijon ƙasa, Buba Galadima, inda suka ce ba ta da wata hujja da ke tabbar da abin da ta faɗa kan Tinubu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Matasan Arewa sun bayyana cikakken goyon baya ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu domin ya yi tazarce zuwa zangon mulki na biyu a zaɓen 2027.
Matasan sun kuma musanta kalaman diyar Buba Galadima, wacce ta ce shugaba Tinubu ya rasa goyon bayan Arewa, domin waɗanda za su zaɓe shi ba su wuce 30%.

Kara karanta wannan
Abu ya girma: Jiga jigai 3 sun nemi ruguza haɗaƙar Atiku, Obi da yan haɗaka a ADC

Source: Twitter
Vanguard ta tattaro cewa hakan na kunshe ne a wata sanarwa da kungiyar matasan, 'Arewa Youth Assembly' ta fitar mai ɗauke da sa hannun shugabanta, Mohammed Salihu Danlami.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matasan Arewa sun goyi bayan Tinubu
Ƙungiyar ta jaddada biyayyarta ga Shugaba Tinubu, tana mai sukar kalaman da Zainab Buba Galadima, ‘yar dattijon ƙasa, ta yi game da jama'ar Arewa da kuma gwamnatin Tinubu.
Sanarwar ta bayyana kalaman Zainab kan yadda ƴan Arewa ke kaɗa ƙuri’a da kuma bakin jinin Tinubu a matsayin marasa tushe kuma ba su wakilci ra’ayin yankin ba.
“Muna kira ba kawai ga ‘yan Arewa ba, dukkan ‘yan Najeriya da su yi watsi da kalamanta. Ba su da wani tushe, kuma ba sa nuna ainihin ra’ayin mutanen Arewa,” in ji sanarwar.
Ƙungiyar matasa ta soki Zainab Galadima
Ƙungiyar ta bayyana Zainab a matsayin ɗaya daga cikin mutane marasa kishin ƙasa da ke ƙoƙarin karkatar da hankalin jama’a da jefa su cikin tunanin cewa Arewa na adawa da gwamnatin Tinubu.

Kara karanta wannan
2027: Jam'iyyar haɗaka ADC ta tono tarihin da ka iya hana Tinubu zama shugaban ƙasa
A kan batun tsarin karɓa-karɓa, ƙungiyar ta ce kamata yi yi mulki ya ci gaba da kasancewa a Kudancin Najeriya har zuwa 2031, bisa tsarin da aka saba na rabon mulki.
Ta kuma tuna cewa ‘yan Arewa, ciki har da tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, sun amfana da wannan tsari, inda ya yi zango biyu daga 2015 zuwa 2023, cewar Punch.

Source: Facebook
Matasan Arewa sun yi fatali da haɗakar ADC
“Goyon bayanmu ga Tinubu a 2027 na nan daram. Babu wata jam’iyya ko haɗaka da za ta iya kawar da shi. Ƴan siyasar Arewa su tsaya su goyi bayansa, su jira lokacinsu a 2031,” in ji sanarwar.
Matasan sun ja kunnen masu shirin tsayawa takara daga Arewa a 2027 saboda wani rashin jin daɗi ko ƙyashi, suna mai kira da a mutunta tsarin karɓa-karba da aka amince da shi.
Matasan APC sun shirya tara ƙuri'u
A wani labarin, kun ji cewa matasan APC sun bullo da shirin tara wa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu miliyoyin ƙuri'u a zaɓen 2027.
Shugaban matasan APC, Dayo Israel ya ce sun shirya bude sabuwar cibiyar matasa da za ta tattaro matasan Najeriya don cimma muradin Tinubu.
Dr. Israel ya ce nasarorin da gwamnatin shugaban kasa Tinubu ke samu a tsakanin matasa ne suka ba shi kwarin guiwar tattago wannan aiki.
Asali: Legit.ng