An Gano Wanda Jam'iyyar Haɗaka ADC Za Ta Tsaida Takarar Shugaban Ƙasa a 2027

An Gano Wanda Jam'iyyar Haɗaka ADC Za Ta Tsaida Takarar Shugaban Ƙasa a 2027

  • Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, Dumebi Kachikwu ya soki haɗakar ƴan adawa karkashin jagorancin Atiku Abubakar
  • Kachikwu ya bayyana cewa tsagin ADC da a yanzu David Mark ke jagoranta na shirin bai wa Atiku abubakar takarar shugaban ƙasa a 2027
  • Ya ce sun gana da jagororin haɗakar tun a farkon 2025 kuma ba su da wani buri da ya wuce kayar da shugaban kasa, Bola Tinubu a zaɓe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC a zaɓen 2023, Dumebi Kachikwu, ya yi martani kan haɗakar ƴan adawa da suka rungumi ADC.

Ya ce tsagin ADC da tsohon shugaban Majalisar Dattawa, David Mark, ke jagoranta sun gama yanke wanda za su ba tikitin takarar shugaban ƙasa a 2027.

Tsohon dan takarar ADC, Dumebi Kachikwu.
Dumebi Kachikwu ya ce Atiku ake shirin ba takarar shugaban ƙasa a ADC Hoto: Dumebi Kachikwu
Source: Twitter

Ana zargin haɗaka na shirin ba Atiku takara

Kara karanta wannan

Takarar shugaban ƙasa za ta tarwatsa Atiku, Obi da sauran ƴan haɗaka a ADC? An samu bayani

Kachikwu ya ce Mark da sauran ƴan haɗaka na shirin ba tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, tikitin takara a 2027, kamar yadda Punch ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake magana da manema labarai a Abuja ranar Alhamis, Kachikwu ya ce ƴan adawan sun faɗa masa, a taron da suka yi, cewa babban burinsu shi ne ƙwace mulki.

Ya kalubalanci jagororin ƙungiyar haɗakar da su kore zargin da yake masu ta hanyar fitowa bainar jama’a su faɗi cewa za a bai wa Kudu tikitin takarar shugaban ƙasa a 2027.

A cewar Dumebi:

“Ƙungiyar haɗakar siyasa ce da aka tsara kuma aka gina ta domin fitar da Atiku Abubakar a matsayin ɗan takara, wannan ita ce gaskiya.”

Yadda ƴan adawa suka shirya kada Tinubu

Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta samu nasarori da ƙalubale a fannoni daban-daban, amma ‘yan adawa daga jam’iyyu na ci gaba da sukar gwamnatin da APC ke jagoranta da cewa ta gaza.

A wani yunƙuri na haɗa kan ‘yan adawa a zaɓen 2027, fitattun ‘yan adawa sun sanar da sabuwar ƙungiyar haɗaka a Abuja ranar 20 ga Maris.

Kara karanta wannan

ADC: Bayan hasashen El-Rufa'i, sabon rikici ya danno jam'iyyar hadakar adawa

A jiya Laraba, jiga-jigan haɗakar suka haɗu a Abuja, inda suka bayyana ADC a matsayin jam'iyyar da za su yi amfani da ita a zaɓen 2027.

Duk da har yanzu ƴan adawar ba su yi rijista da ADC a hukumance ba, amma sun sha alwashin yin biyayya ga jam'iyyar karkashin jagorancin David Mark.

Ana zargin Atiku za a ba takara a ADC.
Tsohon ɗan takarar shugaban kasa na ADC ya ce haɗakar su Atiku na da wata manufa a ƙasa Hoto: @Atiku
Source: Twitter

Kachikwu ya faɗi shirin haɗakar ƴan adawa

Da yake martani, tsohon ɗan takarar ADC, Dumebi Kachikwu, ya zargi Atiku, Obi da abokan tafiyarsu da kwace jam’iyyar tare da nuna gazawarsu wajen jagoranci.

"A ƙarshen 2024 suka nemi na shiga cikin wannan haɗaka, amma sai a wannan shekarar, na amince da zama tare da su bayan wani abokina ya roƙe ni da na saurare su.
"Mun zauna da tsofaffin ministoci da wasu manyan mutane daga gwamnatin da ta gabata. Suka gabatar da hujjojinsu game da buƙatar haɗin gwiwar siyasa.
"Duk abin da suka faɗa yana da alaƙa da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da yadda gwamnatinsa ta lalata Najeriya.

- Dumebi Kachikwu.

Momodu ya ce haɗaka ta shirya tunkarar 2027

A wani rahoton, kun ji cewa Dele Momodu ya ce babu wani abu da sunan rikicin cikin gida da zai raba kan jagororin adawa da suka ƙulla haɗaka a ADC.

Kara karanta wannan

ADC: An bayyana wanda zai jagoranci haɗakar su Atiku zuwa fadar shugaban ƙasa a 2027

Fitaccen ɗan jaridar ya ce batun tikitin takarar shugaban kasa ko wani abu mai kama da haka ba zai raba haɗakar jam'iyyar ADC ba.

Ya ƙara da cewa ’yan siyasar da ke cikin ADC ba don neman mulki suka shiga ba, sai don ceto ƙasar nan daga ƙangin da aka jefa ta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262