Hadaka: Wike Ya Bar Nuƙu Nuƙu, Ya Fadi Jam’iyya 1 da Za Ta Iya Rikita APC a 2027
- Nyesom Wike ya ce kawancen ADC ba shi da ƙarfi ko daidaito don fuskantar Bola Tinubu a 2027, inda ya fadi jam'iyyar za ta iya karawa da APC
- Tsohon gwamnan Rivers ya zargi David Mark da yunkurin karɓar shugabancin PDP kafin ya koma shugaban rikon ƙwarya na ADC
- Wike ya soki Atiku Abubakar da Nasir El-Rufai, ya ce suna yawan sauya jam’iyya don biyan buƙatar kansu kawai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Ministan babban birnin Tarayya, Nyesom Wike ya yi magana mai zafi kan hadakar jam'iyyun adawa.
Wike ya ce kawancen jam’iyyar ADC da wasu jiga-jigan adawa suka kafa, ba shi da ƙarfin fuskantar APC.

Source: Facebook
Wike ya yi magana kan haɗakar jam'iyyun adawa
Wike ya bayyana haka ne a taron manema labarai a Abuja, yana mai cewa PDP ce kaɗai jam’iyyar da za ta iya kalubalantar APC a 2027, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan
PDP ta umarci dukkanin ƴaƴanta su shiga sabuwar jam'iyyarsu Atiku? Gaskiya ta fito
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wike ya ce kawancen ba shi da daidaito, kuma waɗanda suka kafa ta ba su da niyyar ceto Najeriya sai kansu.
A ranar Laraba, Atiku Abubakar da Peter Obi tare da wasu shugabannin adawa suka kaddamar da ADC a cibiyar Yar’Adua.
A taron, an naɗa tsohon shugaban majalisa, David Mark, a matsayin shugaban rikon ƙwarya na jam’iyyar, yayin da Rauf Aregbesola ya zama sakatare.
Wike ya tabo shugaban haɗaka, David Mark
Wike ya ce Mark ya nemi shugabancin PDP, amma aka hana shi, sai yanzu ya koma ADC yana neman shugabanci a can.
Ya ce Dele Momodu bai da tasiri a siyasa, kuma bai taɓa samun ko ƙuri’a guda ba a lokacin da ya tsaya takara.

Source: Facebook
Wike ya yiwa Atiku shagube kan sauya sheka
Game da Atiku, Wike ya ce ya yi ta sauya jam’iyya daga PDP zuwa AC, daga nan ya dawo PDP, ya koma APC, sannan ya koma PDP kuma.
Ya ce yanzu kuma ya koma ADC, domin kawai yana neman inda zai samu mulki, ba wai ci gaban ƙasa ba, cewar Vanguard.
Dangane da El-Rufai, Wike ya ce da Tinubu bai watsar da shi ba, da bai shiga kawancen ADC ba, domin yana jin kishi.
Wike ya yi watsi da kawancen ADC, yana mai cewa PDP ce kaɗai ke da damar fuskantar APC idan ta daidaita kanta.
Ya ce sauran ‘yan siyasa da ke cikin kawancen suna bin kansu ne kawai ba tare da wani tsari ko manufa mai ma’ana ba.
Wike ya fadi cikas da yake samu a Abuja
Kun ji cewa Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana cewa babban cikas wajen tattara haraji shi ne rashin biyan haraji daga manyan mutane.
Wike ya jaddada cewa babu wata hanya da gwamnati ke samun kuɗi a Abuja sai kuma ta kudin haraji da sauran mazauna birnin ke biya.
Ministan ya yi barazana ga mazauna Abuja da ke kin biyan kudin haraji, inda ya ce za a iya wallafa sunayensu a jaridun kasar nan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
