2027: Ana tsaka da Haɗakar Ƴan Adawa, Gwamna Ya Kwantarwa Tinubu Hankali

2027: Ana tsaka da Haɗakar Ƴan Adawa, Gwamna Ya Kwantarwa Tinubu Hankali

  • Gwamna Bassey Otu ya sha alwashin cewa jihar Cross River za ta bai wa Bola Tinubu kashi 96 cikin 100 na kuri’un 2027
  • Otu ya ce gwamnatin Tinubu ta kafa tubalin cigaba, inda ta bunkasa tattalin arziki, da hana rikice-rikice ta rushe sansanonin ‘yan tada kayar baya
  • Ya ce bikin 'Carnival' na bana zai ja hankalin duniya, sannan shirin noma na jihar ya dace da tsare-tsaren kasa gaba daya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Calabar, Cross River - Gwamnan jihar Cross River, Sanata Bassey Otu, ya yi wa Bola Tinubu alkawari a zaben 2027.

Gwamna Bassey Otu ya tabbatar da cewa jihar za ta bai wa Tinubu kashi 96 na kuri'un jihar a zaben 2027 da ke tafe.

Gwamna ya yi wa Tinubu alƙawari a 2027
Gwamna Bassey Otu ya ce dukan kuri'un Cross River na Tinubu ne. Hoto: Bassey Otu.
Source: Facebook

Gwamna Otu ya yi wannan furuci ne a taron goyon bayan Tinubu da jiga-jigan jam’iyyar APC suka shirya a birnin Calabar, cewar Leadership.

Kara karanta wannan

Cire tallafi: Gaskiya ta fito kan zargin Buhari da neman haɗa ƴan Najeriya faɗa da Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

2027: Abin da APC ta ce kan Tinubu/Otu

Hakan ya zo a daidai lokacin da jam'iyyar APC a jihar ta yi taro inda ta tabbatar da goyon bayanta ga Bola Tinubu duba da abubuwan cigaba da ya kawo Najeriya.

Jam'iyyar ta ce ayyukan alherin Tinubu a Najeriya sun cancanci ba shi damar sake nasara a zaben shekarar 2027.

Har ila yau, sun dawo kan maganar zaben jihar inda suka ce Gwamna Otu ba shi da abokin hamayya a 2027.

APC ta tabbatar da goyon baya ga Tinubu da Otu
Gwamna Otu ya ba Tinubu tabbaci kan zaben 2027. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Gwamna ya yi yabawa Tinubu kan ayyukan alheri

Gwamna Otu ya yi magana a madadin Shugaba Tinubu, bayan da mutanen yankin kudu na jihar suka amince da shugabancinsa.

Ya ce gwamnatin Tinubu ta samu ci gaba a fannoni daban-daban, inda aka kafa tubalin tattalin arziki mai karfi da bunkasa GDP.

Ya yabawa jami’an tsaro kan yadda aka samu zaman lafiya, yana mai cewa sun rusa sansanonin mayaka fiye da 16

Kara karanta wannan

'Babu hadaka da Atiku,' Peter Obi ya ce zai yi takara a 2027, zai yi wa'adi 1 kawai

Abubuwan cigaba da Gwamna Otu ya yi

Otu ya kara da cewa nasarar shirin afuwa ga 'yan daba ya taimaka wajen kwantar da tarzoma a jihar sosai, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Dangane da yawon bude ido, Otu ya ce bikin 'Carnival' na bana zai cika shekara 20, wanda zai jawo baki daga kasashen waje.

A fannin noma kuwa, Gwamna Otu ya ce shirin jihar ya yi daidai da na kasa, kuma yana da karfin ciyar da yankin da kasa baki daya domin rage yunwa a tsakanin al'ummarsa.

Gwamna ya gano dalilin dawowar gwamnoni APC

Kun ji cewa Gwamna Bassey Otu na jihar Cross River ya ce kyakkyawan shugabancin Bola Ahmed Tinubu ne ya fara jawo hankalin gwamnoni da manyan ƴan siyasa zuwa APC.

Wannan kalamai na gwamnan Cross River na zuwa ne bayan Gwamnan Delta da manyan jiga-jigan PDP sun sauya sheƙa zuwa APC mai mulkin Najeriya.

Gwamna Otu ya ce a baya Cross River ce kaɗai jihar da APC ke mulki a Kudu maso Kudu amma yanzu Edo da Delta sun haɗe da ita don kawo ci gaba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.