2027: Muhimman Dalilan da Suka Sa Atiku, Peter Obi da Ƴan Haɗaka Suka Zaɓi Jam'iyyar ADC
- Jagororin adawar Najeriya sun zabi ADC a matsayin jam'iyyar haɗaka ne saboda tsarinta ya yi daidai da manufofinsu na kawo sauyi
- Mai magana da yawun haɗakar, Bolaji Abdullahi ne ya baygana hakan, yana mai cewa tun farko suka sanyawa kansu sharuɗɗa
- Ya kuma musanta zargin da ake yi cewa wasu tsirarun ƴan siyasa ne suka mamaye haɗakar, ya ce wannan kawance na kowa ne
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Mai magana da yawun haɗakar jam’iyyun adawa, Bolaji Abdullahi, ya bayyana dalilin da ya sa jagororinsu suka zaɓi jam'iyyar ADC gabanin zaɓen 2027.
Bolaji Abdullahi ya ce haɗakar jagororin adawar Najeriya karkashin Atiku Abubakar ta ɗauki ADC ne saboda kyawawan manufofi da ƙa'idojinta.

Source: Twitter
Abdullahi ya yi wannan furuci ne yayin da ya bayyana a shirin Politics Today na Channels TV ranar Laraba.

Kara karanta wannan
Asiri ya tonu: Tsohon gwamna da ya bar APC ya fallasa shirin INEC na murde zaben 2027
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilan da suka sa haɗaka ta zaɓi ADC
Ya ce zaɓin ADC ya samo asali ne daga tsarin jam’iyyar na karɓar sauyi da kuma daidaituwarta da manufofin haɗakar.
“Lokacin da muka fara wannan tafiya, mun ba kanmu zaɓi, ƙa'idoji da sharuɗɗa na jam’iyyar da zamu nema. Wadanda suka fito daga APC suka ce ba za su yarda ba, domin an ci amanar dalilan kafa jam'iyyar.
“Ƴan PDP sun ce jam’iyyar da ta kasance ginshiƙi a siyasar Najeriya ta zama kwanko a yanzu, ƴan LP kuma suka nuna sun yi nadama. Hakan ya sa muka amince mu sa ƙa'idojin da dukanmu za mu bi.
"Duk jam’iyyar da za mu shiga dole ta yarda mu sake zubin tsarinta, ya yi daidai da manufarmu. Abin takaici, babu wata jam’iyya a yau da ke da irin wannan tsari ba kamar zamanin Jamhuriyya ta ɗaya da ta biyu ba."
- In ji Bolaji Abdullahi.
Abdullahi ya jaddada cewa duk da jam'iyyar ADC ba ta cika duka ƙa'idojin da suka gindaya ba, amma tana da damar da za a iya amfani da ita wajen kawo sauyi a ƙasa cewar Vanguard.

Source: Twitter
Shin da gaske wasu ne ke juya haɗakar ADC?
“Mun fahimci jam'iyyar ta yi daidai da manufarmu, mai yiwuwa ba ta da ƙarfi, hakan ne ya sa muka yanke shawarar ɗaukarta," in ji shi.
Dangane da sukar da ake yi cewa wasu manyan ƴan siyasa ne suka mamaye haɗakar, Bolaji Abdullahi ya ce:
“Wannan ba haɗakar wani mutum ɗaya ba ce. David Mark na cikin wannan haɗaka, ba wakilin Atiku ba ne, haɗakarmu ta mutane ce masu burin kawo sauyi."
David Mark ya shirya kai ADC ga nasara a 2027
A wani rahoton, kun ji cewa jagoran ADC na ƙasa, Ralph Nwosu ya ce David Mark zai iya jagorantar ƴan adawa zuwa fadar shugaban ƙasa a 2027.
Nwosu, wanda ya kafa kuma ya kasance shugaban jam’iyyar ADC na farko, ya ce lokaci ya yi ƴan Najeriya za su samu saiyi mai amfani.
Ya ce a shirye yake ya ba da gudummuwa wajen ganin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya bar gadon mulki a zaɓen 2027.
Asali: Legit.ng
