ADC: An Bayyana Wanda Zai Jagoranci Haɗakar Su Atiku zuwa Fadar Shugaban Kasa a 2027
- Uban jam'iyyar ADC kuma shugabanta na farko, Ralph Nwosu ya ce ƴan dawa sun shirya ƙwace mulki daga hannun APC a 2027
- Nwosu ya bayyana David Mark, shugaban ADC na riko a matsayin mutumin da zai jagoranci ƴan adawa zuwa fadar shugaban ƙasa
- A cewarsa, zai koma gefe tamkar mamba amma zai yi aiki tuƙuru domin ceto Najeriya daga mawuyacin halin da ta shiga
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Taohon shugaban Majalisar Dattawa, Sanata David Mark ya shirya jagorantar haɗakar ƴan dawa zuwa fadar shugaban ƙasa a babban zaɓen 2027.
Ralph Nwosu, wanda ya kafa kuma ya kasance shugaban jam’iyyar ADC na farko ne ya bayyana hakan a taron da kungiyar haɗakar ta gudanar jiya Laraba.

Source: Twitter
Ya ce David Mark, ne zai jagoranci manyan ƴan adawar ƙasar nan da nufin ƙwace mulki daga Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027, kamar yadda Daily Trust ta kawo.

Kara karanta wannan
Takarar shugaban ƙasa za ta tarwatsa Atiku, Obi da sauran ƴan haɗaka a ADC? An samu bayani
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
David Mark zai jagoranci ADC zuwa Aso Villa
Tun da farko ƙungiyar haɗakar ta naɗa David Mark da tsohon gwamnan jihar Osun, Rauf Aregbesola, a matsayin shugaba da sakatarensa na rikon ƙwarya.
Amma da yake jawabi a cibiyar taron Yar’Adua da ke Abuja yayin ƙaddamar da wannan jam'iyyar haɗaka watau ADC, Nwosu ya ce:
“Dukkanmu mun yanke shawarar yin murabus ne domin David Mark ya ja ragamar wannan jirgin ya kai mu fadar shugaban ƙasa.”
Nwosu ya bayyana Aregbesola, tsohon na hannun daman Tinubu a siyasa, wanda a yanzu suka samu saɓani, a matsayin mutum mai kyakkyawan tarihin ayyukan alheri.
ADC: 'Ƴan Najeriya na buƙatar sauyi a 2027'
“’Yan Najeriya na fatan samun sauyi, sun gaji da halin da ake ciki. Ina taya ku murna da kuma tabbatar muku da cewa tare da haɗin gwiwar mambobin NWC da NEC da za ku haɗu da su, ba za ku fuskanci wata matsala ba.”
Ya ƙara da cewa:
“Zan ci gaba da zama mamba kuma uba, aikina ba zai ƙare ba sai mun rera taken ƙasa a fadar shugaban ƙasa, wannan shi ne burinmu na gaskiya.
"Najeriya na cikin mawuyacin hali a ICU, kullum sai an rasa rayuka. Fata na shugabanni masu zuwa su ceto Najeriya daga wannan ƙangin, domin za mu iya.
“Za mu iya taimaka wa Mark da Aregbesola ta hanyar haɗa kanmu. Duk wanda ya soki abin da muka yi yau ba ɗan ADC ba ne.

Source: Twitter
Jiga-jigan da suka halarci taron haɗakar ADC
Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar da Peter Obi, dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a 2023, rahoton Punch.
Sai kuma tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, tsohon gwamnan Imo, Emeka Ihedioha da wasu fitattun ƴan siyasa.
Rotimi Amaechi ya fice daga jam'iyyar APC
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon Ministan sufuri kuma tsohon gwamnan jihar Ribas, Ritimi Amaechi ya fice daga APC a hukumance.
Amaechi ya yi ikirarin cewa Najeriya ta lalace a ƙarƙashin gwamnati mai ci, yana mai cewa lokaci ya yi da za a gyara ƙasar nan don dawo da ƙimarta.
A cewar tsohon ministan, gwamnatin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ba ta san halin da talakawa ke ciki ba, ta fi maida hankali kan neman tazarce.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

