Zaɓen 2027: Matsalar Farko da Haɗakar Atiku da Ƴan Adawa Ta Fara Cin Karo da Ita

Zaɓen 2027: Matsalar Farko da Haɗakar Atiku da Ƴan Adawa Ta Fara Cin Karo da Ita

  • Wata kungiya cikin jam’iyyar ADC ta soki nadin Rauf Aregbesola a matsayin sakataren riko, tana cewa hakan ba bisa doka ba ne
  • Kungiyar “Concerned Stakeholders of the ADC” ta bayyana cewa ba a tuntubi NEC ko shugabannin jihohi kafin yin wannan nadin ba
  • Sun ce jam’iyyar ADC ba ta shiga wata hadaka da wasu ‘yan adawa ba, kuma wannan batu yana kotu, yana bukatar warwarewa kafin ci gaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Wata kungiya a cikin jam’iyyar ADC ta yi watsi da nadin sabon sakataren jam'iyar na riko.

An nada tsohon gwamnan jihar Osun, Rauf Aregbesola, a matsayin sakataren riko wanda hakan ya fuskanci matsaloli.

An soki nadin sababbin shugabannin a shirin hadaka
Tsagin jam'iyyar ADC ta soki zaben Aregbesola a matsayin sakatare. Hoto: Atiku Abubakar.
Source: Facebook

Tsagin ADC ta musanta shiga hadakar jam'iyyu

Kungiyar ta ce wannan matakin bai da hurumin doka kuma ba a yi zabe yadda ya kamata ba, cewar Punch.

Kara karanta wannan

2027: Rikicin shugabanci ya barke a ADC bayan kulla hadakar 'yan adawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta bayyana matsayinta ne a wata sanarwa da aka fitar ranar Talata, wadda kakakin jam’iyyar na kasa, Dr Musa Isa Matara, ya sanya wa hannu.

Sanarwar da aka sanya wa suna “ADC ba mallakin mutum daya ba ce: Martani ga jawabin karbar aiki na Rauf Aregbesola” ta kuma karyata ikirarin cewa jam’iyyar ta shiga hadakar adawa.

“Ko da muna yaba da kwarin gwiwar da Ogbeni Rauf Aregbesola ya nuna a jawabinsa na karbar nadin sakataren riko, dole ne mu nesanta kanmu da tsarin nadin, wanda ba a bi doka ba.
“Ba ma kin hadaka, ba ma kin sauyi, amma muna kin karbe jam’iyya da tilasta shugabanci da jawaban da ke dauke da son zuciya a cikin kwalliyar kalmomi."

- Cewar sanarwar

Tribune ta ruwaito cewa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, dan takarar LP, Obi da wasu ‘yan adawa na marawa jam'iyyar ADC baya a matsayin sabuwar hadaka.

Kara karanta wannan

A ƙarshe, Atiku, El Rufai da Obi sun haɗe kansu, sun zabi jam'iyyar doke Tinubu a 2027

A cikin shirin, tsohon shugaban majalisar dattawa David Mark da Aregbesola sun bayyana a matsayin shugaban riko da sakataren riko na hadakar jam’iyyun adawa karkashin ADC.

A madadin kungiyar, Matara ya ce hanya daya tilo da ake da hurumin sauya shugabanci ita ce taron kasa na ADC ko kwamitin NEC da aka gayyata bisa doka.

An caccaki nadin Aregbesola a matsayin sakatare
Tsagin jam'iyyar ADC ta musanta shiga hadakar jam'iyyun adawa. Hoto: Rauf Ogbeni Aregbesola.
Source: Twitter

An soki nadin Aregbesola a shirin haɗaka

Kungiyar ta ce nadin Aregbesola ya zo ne ba tare da tuntubar kwamitin NEC ba, shugabannin jihohi, shugabannin matasa ko sauran shugabannin jam’iyyar ba.

Sanarwar ta kara da cewa:

“Muna jan kunnen masu shirin shiga ADC ta wannan hanya, A sani cewa wasu na shirin sayar da jam’iyyar don bukatunsu.
“Jam’iyyar ADC ba ta sayarwa ba ce, ita ce mallakin mambobinta, ba wasu masu yarjejeniya da manyan mutane ba."

Matara ya ce babu wani taro na NEC ko na kasa da ya amince da wannan nadin, don haka ana daukarsu a matsayin karya da bata da inganci.

Sanarwar ta ce:

“Ikirarin cewa ADC ta zama ‘dandali na hadakar jam’iyyun adawa’ wata karya ce da ke kokarin bata gaskiyar al’amura.

Kara karanta wannan

ADC: Atiku ya fara kokarin jawo jagorori zuwa tafiyar fatattakar APC a 2027

An hana taron kaddamar da ADC

Kun ji cewa shirin kaddamar da ADC a matsayin jam'iyyar haɗakar 'yan adawa ya gamu da cikas a Abuja bayan soke wurin taro.

An sanar da masu shirya taron cewa otel ɗin ba zai karɓi baƙuncin taron ba saboda wasu dalilai na tsarin otal din.

Dele Momodu ya zargi gwamnati da hannu a lamarin don tsoratar da 'yan adawa, amma ya ce hakan ba zai raunana ƙudirinsu ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.